Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 6
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels FALLASAR UWAR MIJI Anty sadiya Garba Yakasai HAUSAВООK.COM FALLASAR UWAR MIJI Anty Sadiya Garba Yakasai (Mrs Sani Haruna Fanisau) 1 "yan alkawari cikawa, ga shi na ga Wahiddahi, babu zancen "KYusuf. Na ga da ko ba ya nan, kina kya barin zancensa. Na san yau dole a gayan labarin wannan irin soyayyar da kuka yi da Yusuf, alhali da saurayin kawarki ne. yaya aka yi kuka yi aure? Yaya labarin Hajara da na ji labarin kun yaudara?" Wahhida ta yi ajiyar zuciya gami da murmushi ta kuma kalli Rashida, da alamar ta yi mata tambayar da ta fi tada mata hankali da zarar an ambaci sunan Hajara. Ta runtse idanunta kana ta bude su ta kalli Rashida, ta ce, "Rashida, kin san an ce komai mukaddari ne daga Allah? Kuma matar mutum kabarinsa." "Haka ne." Rashida na kallon amaryar tata 'yar shekara talatin a duniya. A yanzu har wannan lokacin kyakkyawa ce ajin farko, idan ka ga Wahiddah ka rantse da Allah ba ta kai wannan shekarun ba. Har yau Wahiddahh 'yar gaye ce, kyakkyawa kamar yau, ba ka ce tana da 'ya'ya biyu 'yan tagwaye ba 'yan kimanin shekaru shida-shida, don steel tana nan kamar da a Wahiddahnta. "Yaya na ji kin yi shiru ne Wahiddahh?" "Me kike so na ce maki Hajara." "Na ce so nake na ji gaskiyar labarinku da yadda aka yi har Hajara ta hakura bar maki Yusuf ta auri Umar. kuma har gobe kuke kamar da, har ma kuke business tare, ina mamakin haka. Wahiddahh ta yi murmushi ta ce, "Ba ki ga komai ba Rasida. Zumuncinmu da Hajara ba zai taba karewa ba, kuma kowacce mace kika gani da mijinta, sai dai in ba mutum ba ce, ko kuma za ta auri mijinta karfi da yaji. To wannan kuwa. Bara na buga ma Yusuf waya tukunna, na ji sanda zai dawo gida, kar na saki baki na manta da ango. "Oh Wahiddah." Rashida ta ce tana rike habarta. "Ya yi tafiya ne kika gani?" "Ba inda ya je yana ofis kalau." "Amma sai an jiwo shi tukunna?" "Ai ya zama dole muddin zai taso daga Ofis da wuri to, dole fa ki hakura da inda labarin mu ya tsaya middin lokacin yi ma Yusıf hidima ya z0. Okey go ahead, ina jiranki Laila majnun wadda ta wuce kan wani lafiyayyan tebur na gilas ta dauko 'yar karamar wayar tafi-da-gidanka ta kara a kunnanta, fuskarta kunshe da murmushi, ta juyo ta dawo ta zauna tana kallon fuskar Rashida, da ta zura mata ido, ta ce "Hello my dear Yaya aiki?.... Sam ba haka bane, ina da bakuwa ne.... ka santa mana Rashida ce fa. D.K, ni ma ka san kawai maleji nake muddin ka fita, to fa bani da sharan sukuni sai dai in su Salwa na guna. Haba Oga karfe takwas ba ka yi dare ba? You know yadda muke damuwa da su 'yan biyu muddin ba ka nan. Don Allah kar ka zarce takwas din, kai ma ka san abin da na tanadar maka. Na yarda Allah ya kai mu. Yanzu dai nake shirin buga mata na gaya mata kayan da muka saro sun kare, okey see you Dear." Ta kife wayar tana dariya. "Yusuf ba shi da dama, har yau bai san ya girma ba," "Ke din fa kinga yadda kike wani lanlankwayewa, wai ke mai masoyi ko?" "Kai Rashida meye laifina ne? Mu fara ko ko kin fasa, na ji da yin hidimomina?" "A'a ta Yusif, Allah ya huci zuciyarki, ke nake saurare. By the way ina su 'yan biyun ne? Ni duk na sha'afa wallahi ban tambaye su ba, suna ina? Don ban jiyo duriyarsu ba? "Kin san yau Juma'a, suna can gidan su Yasuf, sai jibi za su dawo.""Oh lallahi kam jininsu 'yan biyun ya hadu da Hajiya." Wahiddah ta yi dariya ta ce ba dole ba, baki ga fa yadda ake son Yusuf ba, tun da shi kadai ne gun ta." "Well fara, lokaci na tafiya," Wahiddah ta gyara gashinta dake neman rufe mata ido ta ce "Well, da farko ni mutuniyar Sokoto ce. Mahaifana haifaffun garin Sokoto ne, kuma mu Fulani muke, don sana'ar mahaifina Mado sayar da shanu da kuma kiwonsu, duka rigarmu shi ne mai arziki. Sunan mahaifina Mado, amma asalin sunansa Alhaji Muhammadu, kasancewar matsayin sunan ake sayewa da Mado. Allah ya hada jinin mahaifina da mahaifiyata Safiyya, muna kiranta da Innawuro. Mace ce kyakykyawar łokacinta, duk da mahaifina ma ba baya bane, to amma a gun mahaifiyata na gado kyau da goshi. Abu daya na dauko daga mahaifina shi ne tsaho da kalar fatarsa. Fatarmu baka ce amma ba kirin ba, a'a irin fatar nan mai haske da sulbi, babu yadda ma za ki iya tantancewa farare ne mu ko bakake ne. Rashida mu takwas ne gun babarmu, mata hudu maza hudu, wake da shinkafa muka yi. Babbanmu shi ne. Yaya Najir, sai Safiyanu da Nasir da kuma Naja'atu da Salma da Hadiya da ni Wahiddda, sai autanmu Haidar, saboda sunan mahainmu aka sa masa shi ne muke ce masa Haidar. Allah ya hore ma mahaifanmu sani saboda haka sun ba mu kyakykyawan Ilmi. Tun muna Sokoto aka aurar da Yayyena mata, Yaya Naja'atu na garin Bauci tana auren wani soja, Salima na Bauci tana auren ma'aikacin Lahda, sai Hadiya dake nan garinmu Sokoto, tana auren dan hakimin rugarmu. Yaya Nadir ma ya yi aure yana kaduna kasancewar aikinsa haka Yaya Nasir shi ma yana nan Sokoto da matarsa. Yaya Safiyanu ma haka, amma shi ma yana Sokoto. Ni da Haidar aka taho damu nan garin Katsina, saboda Baba ya gina tankasheshen gida mun koma, sai dai su Yaya sun ringa zuwa. Muna zaune a unguwar sarki nan Baba ya gina gida muna tafiya makaranta ni da Haidar nan muka haďu da Hajara da yake ita ma kyakykyawa çe kuma kamilalliya. Sai ta shiga raina muka yi kawance, idan ba'a zo daukarmu da wuri ba, to motar gidansu muke bi. Ba inda bana shiga a gidansu haka ita ma, har iyayenmu OWSD 2 suka yi kawance. Kaya iri daya ake dinka mana walau daga gidansu ko daga gidanmu, komai namu daya ne ga mu da dan jiki, saboda haka muna shekara goma sha tara - tara muka gama Secondary, sai jiran sakamako don mun yi alkawarin tafiya Jami'a. Muna gama makaranta muka tafi Sokoto don ganin gida nan na shiga kalle kalle kamar bakuwa don rabona da Sokoto tun ina form one, to yau ga shi na gama, Allah-Allah nake mu je ko na ga 'yan'uwana. Baba na karatun jarida amma sai da gilas yake gani, saboda tsufa amma in ka gan shi lafiyayye, saboda kudinsa. Ya kuma samu kulawa, duk da yana fama da ciwon zuciya muna kula da shi yadda ya kamata, ba'a bari ransa ya baci gudun kar a yi sm masa laifi ciwonsa ya tashi. 6 Inna ta kalli Baba ta ce "Dubi ka ga yadda Wahiddah ke faman zumudl, ni har dariya take ban" Baba ya dan kallan ya ce "Wa ya ga sabon shiga, ni ma ban san dalilin murnar ba." "Abba Zango su da Yaya Salima suna farin ciki da kuma zan je gidan Yaya Naja'atu,""Eh, lallai kam kya yi murna da haka." Muna hira muka isa Sokoro kofar gidan mu direba ya yi fakin an gyare shi kamar me. Nan na fito da murna ban saurari komai ba, gidan Yaya Najir na nufa da murnata ban ma jiwo kiran da Mani direba yake yi min ba, mutane sai kallona suke suna mamakin girmana da irin shigar kayan da na yi. Na fada gidan Yaya nan na ga motarsa a waje, na tabbatar yana nan, da sauri na shiga ina "Yaya ga mu mun zo", matarsa ce ta fito da sauri ta tare ni tana "Auta, auta ina ki ka bar min karamin maigida?" Na kalli Yaya Umaima na ce "Ina masu kula da Babana ne? Haidar kawai Yayana nake son gani da 'ya'yana, ina suke?" Na shiga ina "Hello children." dukkan su suka taso suka rungume ni da oyo oyo, har kasan kafet suka kai ni muna murna. Yaya Umaima na kallon mu tana dariya, uwar fitina Murja ta ciren dan kwali ta shiga ja min ribbon din da na kama kaina da shi, duk sai da ta yi min kaca-kaca da adon. Yaya ya fito fuskarsa washe da fara'a ya ce "Wahiddah ke ce haka kika zankale, kin koma Inna sak," na`mike da fara'a na gaida Yaya, ya amsa da fara'arsa, ya ce "Wonderful, ina su Abban?" "Suna gida har Haidar bai san nan zan gudo ba," ta fada cikin alamun yarinta. Najir ya dubi yadda kanwarsa ta hade duk sai ya ji kamar ita kadaice mai kyau a garin Sokoto. "Yaya ina za ka ne?" Na tambaye shi? “Gun su Inna za ni mana, ko zaki bi ni?" "A'a Yaya sai na huta na taho, don yau ma daga nan gidan Yaya Halima za ni na gan ta." "A`a ki bari na dawo na kai ki, ba na son ki fita ke kadai," ya zari makullansa. Faisal ya ce "Abbana zan bi ka," dole Yaya ya tafi da shi. Yaya ya kalli Yaya Umaima ya ce "Na manta, Mustafa Zai zo ki ce ya jira ni za ni gida su Abba na sun zo. Ta ce "to zan gaya masa" ni ko ina ta kokarin bude food flaks din da na gani kan kafet, "Yi a hankali sarauniyar kyau 7 abınem Yayan ki ne a ciki," na yi dariya jin ba'ar da Yaya tai min "Ni ce ma sarauniyar kyau, Yaya Umaima har da tsokana tsakaninmu," ta yi dariya "Allah ba tsokana ba ce, don dai ba ki ga yadda ki ke bane. Wai ina Hajara ne?" "Tana Katsina ita ma garinsu suka tafi shi ya sa ba ki gan ta ba, amma in kin haihu za mu zo." "Allah ya nuna mana lokacin, yanzu kuma sai aure ko?" Na firfito da idona na ce "aure kuma Yaya? Wace ni da aure, ina, ai sai mun ga karshen biro. Ko zancen samartaka ma ba na yi, balle in sami mijin auren." "Wa zai bar ki yi karatun Baby?" "Babana mana," "Shi Abban ne ya ce?" Na hadiye burabuskon bakina, na ce "kwarai kuwa, muna komawa za'a sai min form." "Da kyau" 'Yar sallamar da muka jiyo ce ta katse mana hirar. Yaya ta ce "Shigo mana Mustafa kamar wani bako." Ya shigo kaina na duke, saboda haka ban ga fuskarsa ba. Ya ce “A'a ta Najir bakuwa kuka yi ne?" Ya fada daidai lokacin da yake kokarin zama. "Ba ka santa ba ke nan?" Yaya ta tambaye shi, “Ai ko a jikina ban taso ba bare ya ganni, ko ni na gan shi, "Don Allah wacece wannan?" "Kai Musty to kanwarka ce Wahiddah," "wacce Wahiddahr?" ya fada a gaggauce, "Wahiddahh dai ta gidansu Najir." "Ita ce haka I can/t believe my ears,""Wallahi ita ce, to don haka na dago don na ga mai yi min magana. To a nan na ji yawun bakina ya kafe, don tafiya birnin tunani da na yi waye wannan? Shi ma kallona yake kamar sabon maye, har na ji kunya na sunkayar da kaina kasa. "Musty yaya ne?" Ya dan motsa ya ce"Ba komai Umaima," ta yi murmushi kawai ta ce "Ina fa ba komai," na dago kaina na ce "Ina kwana?" ya ce "lafiya kalau Wahiddah, yaushe ku ka zo garin mu?" Na yi murmushi na ce dazu muka zo, yaya su Abba? Suna nan lafiya, ice ko za ki yi mana dan kwana biyu a garin namu, Eh, sati daya zamu yi mu koma, sati daya Wahiddah ai ya yi kadan. a'a bai yi ba na ce masa, ya ce to ai shi ke nan. 8 Ke madan ina angonki? Ya tafi can gidan gaida su Abba ya ce ka yi jiransa, ya kamata ni ma na je na gaida su kar na yi laifi, Wahiddah zo mu tafi ki raka ni mana? A'a ni ba yanzu zan tafi ba, haba kanwata kya ki raka yayan naki gida kuwa? Dole na bi Yaya Mustafa ba don na so ba. Duk na dabarbarce a motar, ban san dalili ba, sai da na tsinci kaina ina jin kunyar Mustafa, abin da ban taba ji ba a rayuwata. Ya kula da hakan sai ya shiga zolaya ta, wani na tanka, wani kuma na yi masa shiru. Ya dan kalli fuskata cikin sigar so, ya ce "waye gwanin ki?" Na ce "Ban gane ba," nufina waye surikin namu a can Katsina? Na ce ba ni da wani gwani, ni sai biro da takarda," Mustafa ya sheke da dariya, ya ce "Wahiddah baki da dama, kin taba ganin biro da takarda sun zama saurayin budurwa?" na ce kwarai ma kuwa", ya ce a'a don Allah abar biron da takardar, ga wani masoyin kin samu," na kalle shi na ce "Waye? Ya kanne ido ya ce "Ni Mustafa ina ciki, ko na yi maki tsufa?" Na rasa bakin magana sai kawai na sunkuyar da kaina. Hakika Mustafa ya hadu sosai, illah gaskiya ba na son soyayya, muna farawa aure za a yi min, shi ke nan na rasa karatuna. "Me ki ke tunani ko ban yi maki ba? Na ce "A'a kawai dai ba na soyayya, ya dan bata rai kamar yaya ba kya soyayya? Nufinki ba kya so na kе nan na hakura?" Na kalle shi naga duk ya rude na ce "Ba haka nake nufi ba, nufina muddin ka nuna ma su Abba da Yaya cire ni za'ayi a yi min aure, ni kuma karatuna nake so. Ya dan saki rai, ba komai ba zan shaida masu ba, har sai kin fara Jami'ar in ya so sai a yi maganar tamu, kin amince?" Na daga kai na dai-dai lokacin da muka isa kofar gidanmu. Yaya ya fito ganinmu ya tsaya ya ce "Kai da na ce kai jira na? Ka san dole na zo gun su Abba?" Ni ko ban saurare su ba, na wuce saboda kallon da Mstafa ke min kar yaya ya gano. Inna na damu na taddata na dan jingina kan cinyarta na ce "Inna kamar kin san ina son shan furar nan," ta yi dan murmusi ta ce "Abbanki ya sani damu, amma ta ishe ku, har yana fada wai me ya sa yayanki bai taho da ke ba, ya bar ki a can, shi ba ya so ki ringa nisa." Nnayi dariya na ce "Ba ga Haidar nan ba," "A to, ai kin kwace mini mai gidan nawa",", na yi dariya na ce "Ina Abban 9 yake?" "Yana samansa", na mike da guduna na nufi sashin Abba kai na ba dan kwali, dai-dai lokacin su Yaya suka shigo. Mustafa ya kuran ido cikin sha'awa ya ce "Yi a hankali kar ki fadI." na dan waiwayo shi na yi dariya na haye sama. Yaya Najir ya kalli Mustafa ya ce "In ka biye ta Wahiddah, sai ka sha kallo. Tun tana karama Allah ya sanya mata fitina kamar biri, ka ga har yanzu ganin kanta take kamar yarinya." "Haba Najir shekarunta nawa? She steel a Baby, sha tara fa. In da an yi mata aure da wuri da yanzu tana da 'ya'ya amma to kai meye ra'ayinka?" "Kawai ta samu miji ta yi aure da ya fi mana kyau” Daidai lokacin da suka shiga falon Inna tana kallon talabijin suka yi sallama Inna ta gyara lullubinta ta ce "Ku shigo mana kai da wannan yaron ne." kasancewar shi ma ba ta fadar sunansa wai kara, dalilin babban abokin danta ne na fari. Inna yaya kuka zo gida lafiya? Lafiya kalau ina manyan naku ice ko suna lafiya? Lafiya kalau Inna basu san da zuwan ku ba. da sun zo ai ba komai muma bamu jima da zuwa ba, kai ka kai su gun Abban naka ne? a'a nan muka fara zuwa, to kuje yana sama ku gaisa mana, Mustafa cikin jin kunya ya mike ya ce bara muje mu gaisa wai kuwa anyi bikin naka? Najir ya yi sauri ya café ina sam ya ki yadda har yau kuma bai yi ba kin gan shi nan. Mustafa ya shiga hirar Yaya ai gaskiya nee kake harara ta. Inna ta ce to lallai ba ka kyuta ba, don Allah a yi kokari a yi ka ji ko, zaman haka ba shi da wani amfani sam. To Umma insha Allahu za'ayi. Allah ya taimaka ai komai lokaci ne kuma shi aure ba a yi masa garaje. Mustafa ya hankada Najir suka hau sama wallahi Najir ba ka da sirri, me ye na gaya ma Inna gaskiya. To kayi auren ne? Hayaniya suka jiyo, ni da Haidar muna kallo a falon Abba. Mustafa ya zuban ido yana wani murmushi, nan kunya ta dan kama ni na sakı Haidar. Ke uwar kokawa ina Abban? Yaya ne ya tanbaye ni. yana bandaki yanzu zai fito. Suka samu kujeru suka zauna. nı ko da na koma kuryar falon na makure saboda mayataccen kallon da nake samu daga Mustafa. 10 Ke kin fasa zuwa baccin ne? Ban fasa ba Abba P כב PU bari gobe ka kai ni wai shi ba zan kwana ba, Uhum ba zan maki karya ba unguwa za mu da Mustafa sai dai Manu ya kai kı Na turfune, gaskiya kai za ka kai ni, na ce maki bani da lokaci ba ga Manu ba, Abba ya fito kai meye na yi mata ihun haka? Yaya ya ce wai sai lallai na kai ta gidan Yayarta Salima, na ce ba ni da lokaci ga Manu nan ya kai ta shi ne take wani bori. Baba ya ce ba ka ganin yarinya ce ko ba za ka kai ta ba ai sai ka lallaba ta ba ka tsaya kana mata ihu ba. Abba ka fa sangarta Wahiddah da yawa to in daina ni na kai ta, da dai Yaya ya ga Baba ya yi fushi da shiri ya ce Allah ya huci zuciyarka tashi mu tafi. Ni kuma na yi hajin nawa na ce na fasa na shiga daka na yi sororo jikin kujerar Babansu. Ban san ka zama babban banza ba sai yau ashe in har na mutu ba za ka iya kula da ita ba balle Haidar. Nan jikin Yaya Najir ya kama rawa har na tausaya masa ya ce ka yi hakuri Baba, na yi kuskure ya juyo gareni ki yi hakuri Wahiddah. Na share hawayena na ce na hakura yaya don Allah ni ma ka yi hakuri ka san ba na so ka tafi ka bar ni ne. Yaya ya yi murmushi ya ce shi ke nan ya wuce Baba ga Mustafa ya zo gaisheka, wanne Mustafan? Baba Mustafa abokina na gidan Alhaji Umar, Oh oh ka ce abokinka tun kuna makaranta shi ne yazo gaishe ni.? Mutafa ya durkusa har kasa ya gaida Baba nan suka fara hirar wancan da wancan, in takaice maki Rashida Allah munji dadin hutun mu kuma baki sani ba soyayya mai karfi ta shiga tsakanin mu da Mustafa, ranar da za mu tafo kamar anyi masa mutuwa Dukkan 'yan uwana sun zo yi mana sallama nan muka bar Haidar gidan Yaya Najir tun da ya ga su Faisal ya like dole muka taho muka bar Haidar Bamu iso Katsina ba sai yamma likis tun kan na shiga gida na tsinkayo muryar mutuniyar tawa, da gudu muka rungumi juna muna tsalle. Hajara ta ture ni ta ce ke don Allah tafi can kın 11 barni da kewarki, yi hakuri kawalliya wallahi ban so haka by the way ina Yusuf dinki? Ta share hawayenta ta ce mun rabu, kunyi me? Na tanbaye ta, mun rabu na ce maki, me ya faru fada kukayi? Ta jijjiga kai zuwa nayi na same su da wata da nayi masa magana sai ya ce da ma yana son ya gayan shi gaskiya ba ya sona, na tambaye shi me ya faru tsakanin mu? Sai ya ce min kawai shi ba zai iya ci gaba da ni ba don Allah nayi hakuri ya canja ra'ayi. Na ce masa wata ka samu? Ya ce min shi ba wacce ya sake illah ya gaji da sona na shawo kansa amma ina sai ya ce min wai is over na yi tsaki gwarma da Allah ya sa ban san shi ba to ke me ye na kukan ki ki hakura kawai ki yi fatan Allah ya hada ki da rabonki, ayya Wahiddah ina ga ba ki san yadda na ke son Yusuf bane ina ga ba zan iya rabuwa da shi ba. Ba za ki iya me ba? Don Allah kar ki ba da ni, wallahi ba zan iya ba ina ga fushi yake da ni amma na san zai wuce zamu shirya ne. To Allah ya sa, wanda bai ji bari ba ai ya ji hoh na ce da ita ta yi dariyar karfin hali ta ce yaya labarin Sokoto? Nan na saki murmushi na mance da wani zancen Yausuf na shiga lassafa mata duk abin da ya faru a can, ta yi shewa ta ce at last Wahiddah na zancen soyayya lallai za'ai ruwa da kankara. Kin san me ya faru Rashida? Rashida ta girgiza kai cikin alamar Wahiddah ta ci gaba, ta ji yadda aka yi suka hadu da Yusuf. Wahiddah ta kur61 ruwan lemon da aka kawo musu ta ce bayan mun yi sallama da Hajara ta tafi ni kuma na fada gyaregyaren daki na bayan na gama na ce me zan yi ba bacci ba, bacci mai nauyi ya kwashe ni ban farka ba sai da Inna ta shigo da kanta ta ce to Wahiddah a tashi a yi sallar asuba baccin ya isa haka. Na dan murje ido na alamar baccin bai ishe niba na ce Inna ta manta ina fashin salla tun jiya. Inna ta ce oho wallahi ko na manta, amma dai ya kamata ki tashi ki yi wanka ki je Abbanki ya ganki a huta. Na ce to Inna gani nan fitowa Allah tilas Inna ta fita, ina ganin fitarta na koma baccina, ban tashi ba sai karfe lakwas. Na yi salati na mike duk jikina a mace na zagaya 12 bayi na shiga wanka, don mun yi za mu hadu'da Hajara yau d gidansu, saboda haka na shiga da sauri na watsa ruwa na fito. Ina tsane jikina wayar jikin gadona ta dau ruri, na dan ja tsaki na ce wane gwanin ne da sassafe haka. Kamar kar na dauka, sai na canja shawara na dauka a wulakance na ce wanene? Haba gimbiya fada ne da ke haka lallai zan yi aiki Babba, na dan saki murmushi hadi da ajiyar zuciya na ce Musty kane? Ni ne gimbiya yaya kuka zo gida? Well lafiya sai dai ..... nai dariya, ya ce dai dai me? Fadi mana, shi ke nan abar maganar mu shiga wata, ba zai yuwu ba sai an gayan kafin na cigaba, O,K dama ca zan yi sai dai ke warka shi ke nan ko? Ya yi dariya ya ce amma da za'a ce min bakomai bayan gashi an gayan abu mai dadi da muhimmanci. Na dan fada gado na ce kai Musty me ye abin dadi anan ya ce kince kina kewata kin ga ke nan ina da matsayi me ki ke yi ne honey ya fada a sanyaye? Na

Chapter 1 of 6