Sai na zo din kenan, yanzu zan
je gida, idan kin gama abin da kike yi ina jiran
wayarki".
Bayan Aslam ya tafi ita kuma Hanifa ta
shiga gida, ta je dakinta tayi wanka sannan ta
gyara gashinta bayan ta kammala duk
abubuwan ta sai ta dauko waya ta buga gidan su
Aslam.
Aslam yana gaban waya yana jiran Hanifa
tabugo.ai kuwa ringin daya sai ya dauka.
Bayan sun gama gaisawa sannan sai ya cе:
22.
Yanzu don Allah sai yanzu kika tuna
dani? Kin san kuwa irin jiran da na yi miki? Tun
bayan na dawo nazo na zauna jiranki.
Har sai dana gaji naje nayi wanka na ci abinci
amma shiru ba labari wai malam ya ci shirwa
Ni da har na kwanta sai kuma na ji karar waya".
ce:
Hanifa ta kyalkyale da dariya sannan ta
"Shi ya sa na ji tanata ringin sai da na
dade sanan aka dauka. Ta kara da cewar:
"To yanzu dai ka yi hakuri, zance ya
wuce ba za'a kara ba".
Hira ta yi dadi har basu san dayan dare ta yiba,
sai da Hanifa ta kalli agogo tace da Aslam.
"Wallahi Aslam dare ya yi fa. ga shi baccі
nake ji".
Aslam ya kalli nasa agogon sannan yace
"Allah ni kuwa ba na jin bacci, kuma
gaskiya kema ba za ki kwanta ba. Haka kurum
ki yi bacci ki barni ni kuma ba na ji".
"To kai ma ai sai ka kwanta, baccin zai
zo sai ka yi kai ma". In ji Hanifa.
"Lallai ma ai ni na san tun da ban jin
baccin ba zan yi ba, ke ma sai ki hakura" cewar
Aslam
23.
"Dare fa ya yi gashi dare mahutar bawa
kana kwanciya baccin zai zo" in ji Hanifa ta na
magana kasa-kasa.
"Gaskiya a'a ba za ki kwanta ba "Yana
darıya ahankali ya fada.
Hanifa tace "To shikenan"
"Don Allah Hanifa hotonki nake so kamar
guda goma masu kyau". Aslam kenan.
Hanifà ta ce dashi cikin mamaki.
"Haba dai guda goma, sai kace a film, ya
ya za ka yi da hotona ni daya guda goma, ai sun
yi maka yawa".
"Wallahi ni da zaki bani film guda ma ina
so". Cewar Aslam.
"Gaskiya sai dai na baka guda daya ko
biyu amma ai sun yi maka yawa". Hanifa ke fada.
"Haba sun yi min kadan, ai ni guda talatin
da shidan nan nake so". In ji Aslam
"Guda talatin da........ fim guda fa kenan!
Hanifa ta fada tare da nuna mamaki a muryarta.
"Eh mana, to meye dan kin bani ko ban isa
a ban ba?" In ji Aslam.
"A'a ni na ce, ai ka isa har kayi yawa, sai
kagansu".
24.
Aslam ya dan dauke wuta kadan (Ya yi shiru
ga barin zancé) sannan ya ce da Hanifa
"Gaskiya ni ma na fara jin bacci, bari na barki mu kwanta haka".
"Ka yi me? Ka kwanta lallai ma Aslam
wasa ma kenan. haba haba nima fa yanzu ka
hana ni na kwanta". Ta fada cikin nishadi ta
kama shi a hannu
"Ya nesa ya ce to shikenan ki je kema ki kwanta" inji Aslam
ta ce da shi:
"To ai ni yanzu bana jin baccin kuma gaskiya ba za ka kwanta ba kai ma".
Aslam ya hakura da baccin suka cigaba da hira.
Bayan wajen minti talatin sai Aslam ya ji
suna cikin magana Hanifa ta yi dif, ya dan
saurara shiru. Can sai ya ce a hankiali "Hanifa
ya ji ba amsa sai ya dan bubbuga kan da dayan
hannunsa ya kara kiranta "Hanifa. Hanifa da ya
tabbatar Hanifa ta yi bacci sai ya hakura shima
ya kwanta.
Washegari da yamma sai ga Aslam. Ya
zo gidan su Hanifa.
Bayan sun gaisa sai ya ce da ita:
"An tashi lafiya sleeping beauty?"
25.
ta sha kunu sannan ta се:
Wai don Allah jiya ya aka yi kayi bacci ka barni?
Ya kalleta ya saka wata hadaddiyar dariya
sannan ya ce:
"Ni Hanifa? Yaushe ma muka hadu da kе
bare na yi bacci na barki?".
Ta dan yi masa kallon soyayya mai kwantar da hankali sannan ta ce:
"Don Allah zancen gaskiya".
Sannan sai Aslam yace tare da sassauta murya:
"To Wallahi keki ka yi bacci kika barni
akan line ina ta faman magana da fanfalakwai.
"Ta dan rufe idonta tana dariya ta ce:
"Wallahi ni bansan lokacin da ya dauke ni
ba. Ni dai kawai natashi wajen shida da safe don
ban samu sallar Asuba ba ma. Sai na ganni a
kwance ni a can kan wayar a can".
Suka kyalkyale da dariya sannan ta kara da.
cewa:
"Allah ya so nima na kulle kofata kafin na
bugo wayar, da na san sai mama ta yi min fada
ban yi sallar Asuba a jam'l ba, daman ai na gaya
maka bacci nake ji, ka hana ni na kwanta".
Haka dai suka sha hirarsu sai da aka kira
sallar magriba suka yi sallama. Ya je masallacin
26.
unguwar ya bi sallah, ita ma Hanifa tana shiga
gida ta daura alwala ta yi sallah.
Bayan an yi sallah ne sai suka ci abinci
gaba dayansu har da Alh. Aminu. Da aka kare
cin abinci sai Hanifa ta shiga dakinsu ta yi
wanka.sannan tanufi dakin maminsu.
Bayan ta zauna a kan kafet din falon
mamansu sai mamansu ta fara da yi mata
nasiha da bata shawarwari a harkar rayuwa
Sannan sai ta kara da cewa:
"Hanifa ina fatan kin fara tunanin mafita a
harkar ki, domin kuwa na san Abbanku yana
dab da gabatar da zancen aurenki, domin na ga
ya fara damuwa da wadannan samarin da suke
zuwa wajenki".
Ta dan kalli indaHanifa take zaune à nutse
sannan ta cigaba da cewa:
"Hanifa ina kara jan.kunnenki da ki rabu
da wadannan taron tsintsiya ba sharar, samarin
yanzu karya ta cika musu ciki. Kuma yau inason
ki gaya min duk cikin masoyan naki waye kika
zaba ya zama mijinki? Don kin san dai ba sa
miki ido za mu yi ki kawo mana lalatacce ba".
27.
Hanifa tashiga kogin tunani yayin da
mamansu tà bata lokaci domin ta yi tunanin ta a
hankali.
Tabbaş ina son Zubair, kuma ina matukar
kaunar Aslam.
Ni kuwa yanzu idan ban auri Aslam ba ya ya zan
yi, gaskiya ina matukar kaunarsa ina kuma
kaunar kasancewa tare da shi. Amma yanzu idan
na ce zan auri Aslam, to ai shi yanzu ba aüre
za'a yi mishi ba, yanżu ma masters dinsa ya ke yi
level 100, kuma gashí, shima Aslam din yana
kaunar ta sosai.
Basu kara da komai ba sai ga babansu
Hanifa ya shigo tare da Haj. Salamatu. bayan sun
samu waje sun zauna sai Hanifa ta tashi za ta fita
waje, sai Abbansu ya ceda ita
"Ke Hanifa! Zo nan ki zauna ina da
magana muhimmiya da ke"
Bayan ta dawo sai ta koma inda ta tashi ta
zauna.
Sannan sai Abbansu Hanifa ya fara da salatin
Annabi goma sannan suka yi addu'a aka shafa.
Alh. Aminu ya dubi Hanifa ya ce:
"Kin gama makaranta, gashi har
sakamako ya fito, yanzu kuma sai abu na gaba
28
kin riga kin san babu zancen makaranta sai dai
idan mijin da za ku aura yayarda.
Ya dan gyara muryarsa sannan ya ce tare da
kallon matayen nasa a lokaci daya:
"Ina son ki gabatar min da wanda ki ka
zaba a matsayin abokin rayuwar ki ba da bata
lokaci ba idan kuma duk maneman naki ba su
kwanta miki a rai ba, to kada ki kwari kanki ki
fito ki gaya mini. Ina son ki gaya mini abin da
yake ranki".
Hanifa hankali duka tashe ta ce a cikin
rawar murya:
"Baba ina da shi"
Baban nasu ya ce "To Alhamdulillah".
Bayan dan dakikun da suka wanzar da shiru sai
Alh. Aminu ya ce:
"To kafin na kai ga nisa, ina son
na san kin san wani yaro wai Zubair?"
Hanifa ta kara. sunkuyar da kanta kasa sannan
ta ce:
"Eh Baba! Na san shi yana zuwa wajena,
dan uwan su Salimat ne"
sai mahaifin nasu ya sake cewa:
"To shi ne ya aiko da magabatanshi
wajen kawunki Sani, suna nemar wa dansu
aurenki, ina so na ji kin amince da shi ko kuwa
29
akwai wani daban. sai a sanar da su tun kafin
lokaci ya kure".
Hanifa kwalla ta cika mata ido taf ai ba'a
kara sakan ba sai da hawaye ya cika mata fuska
Bata ce komai ba sai ma dada sunkuyar da kanta
kasa da ta yi.
Hanifa ba ta san yanda za ta yi ba, a ranta ta san
tana son Zubair tana ganin kuma za ta iya zama
da shi don ya cancanci a so shi. To amma Aslam
ta san ba aure za ayi wa Aslam ba yanzu, kuma
ita ta san ba barinta za a yi a zaune a gida ba,
dole ta zabi Zubair.
Haj. Salamatu ce da ta ga shirun ya yi yawa ta ce
da ita:
"Ya ya dai 'yar Hajja, ba ki yi magana ba".
Hanifa ta daga kanta sannan ta ce:
"Ina son shi, Baba"
Haj. Amina ta ce da ita:
"To Hanifa tunda kin.amsa kina son shi sai
ki rabu da wadannan samarin da suke sallama da
ke"
Dukkansu suka watse aka bar Hanifa a
zaune. Sai da ta gama nazarin ta sannan ta tashi
ta nufi wajen Haj. Salamatu.
30.
Haj. Salamatu ta ce da ita daman yanzu
nake son na aiki'Zahra ta turo mini ke a falon
Hajiya.
Bayan sun dan taba hira sai Hanifa ta
kara yin shiru tare da ajiyar zuciya. Haj.
Salamatu ta rarrashe ta tare da yi mata
dabarun manyan mata har sai da ta gaya mata
abin da yafi tada mata da hankali.
Haj. Salamatu ta yi nazaria kan matsalar
Hanifa sannan ta ce da ita:
"To, 'yar diyata ga wani taimako zan baki
ki yi kokari ki aiwatar da shi"
Ta tashi ta shiga cikin dakinta ta fito mata da
takarda da biro sannan ta koma ta zauna a.
kusa da ita kan kujera ta fara da cewar:
"Hanifa ko da yaushe ki kasance mai
mika lamarinki ga ubangiji" zaki ga biyan bukata
a cikin lamarinki".
Tadan saurara kadan ta ce:
"Yanzu ga wata addu'a ina so ki yi ta
cikin yardar Allah za ki ga biyan bukata.
A game da biyan bukata an samo Hadisi daga
SA'AD BIN ABI WAKKAS(R.A) cewa Annabi
mai tsira da aminci ya ce (Addu'ar nan da
Annabi Yunusa ya kira Ubangiji da ita lokacin
31.
da yake cikin kifı, duk mutum musulmi wanda ya roki Allah da ita a kowace bukata, to Allah zai
amsa masa). Turmizi, Nasai Hakeem ne suka
ruwaito.
"LAA'ILAHA ILLA ANTA
SUBHANAKAINNI KUNTU MINAL ZAALIMIN"
Ita dai wannan addu'a manyan malama
na musulunci sun yi bayanin hanyoyi iri dabandaban wajen amfani da ita, to amma daga ciki ga
wasu muhimmai guda uku.
1. Hanya ta daya mutum ya yawaita fadar
wannan addu'a dare da rana. Safe da yamma
a ko wanne lokaci da nufin Allah ya biya masa
wata bukata da ta dame shi.
2. Hanya ta biyu, mutum ya dinga karanta
addu'ar sau dubu daya da dari daya da goma
sha daya (1,111) sau uku kullum wato safe,
yamma da daddare, sannan ya nemi biyan
bukatar da ta dame shi a duk lokacin da ya
karanta adadin.
3. Hanya tą uku, ita ce mutum ya yi sallah raka'a
biyu da fatiha da ko wacce sura ta sawwaka
gareshi sannan a sujadar karshe wacce daga
ita sai tahiyya sai ya karanta ita addu'ar sau
arba'in da daya (41) kuma ya roki bukatar
tasa, sannan sai ya dago ya yi tahiya ya yi
sallama, kana ya yi istigfari da salatin Annabi
(SAW) sannan kuma ya maimaita fadin
bukatar tasa. In sha-Allah za ta biya kamar
dai yadda hadisin ya nuna. Kuma wadan nan
32.
hanyoyi da malamai suka bayyana wacсе
đük mutum ya bi duk daya ne. Allah ya'sa
mu dace amin.
Haka kuma, dai game da ita dai wannan
addu'ar an samu Hadisi daga
ABDURRAHMAN BIN AUFIN (RA) cewa:
ANNABI mai tsira da aminci ya ce:
"Hakika addu'ar nan ta dan uwana
Annabi Yunusa (AS) akwai mamaki acikinta,
farkonta Hailala ce, tsakiyar ta tasbihi ne
sannan kuma karshen ta furuci ne da
zunubi.
Kuma wani mai fama da tsanani, ko bacin
rai.ko bakin ciki, ko bashi, bai roki Allah da
ita sau uku a rana ba,sai Allah ya amsa
masa. DAILAMI NE YARAWAITO.
Hanifa ta gama rubuta duk wannan
bayani da takardar da Haj. Salamatu ta
kawo mata, sai ta kuma karanto abin da ta
rubuta don tabbatar da bata samu bata ba.
Bayan an gyara batan da kuma kara yi
mata bayani sai Haj. Salamatu ta kara da
cewar ga wata kuma, "Idan kin samu
isasshen lokaci ki dinga yin ta itama."
Idan mutum yana da wata bukata
muhimmiya a game da sha'anin aiki ne, ko
33.
aure, ko neman arzikı. ko kuma kashe wata
magana. ko sarauta. ko tafıya ko kuma ko
wacce irin babbar bukata, to sai ya yı wannan
sallah tare da wanan addu a kamar daı yadda
manzo (SAW) ya nuna mana.
An samo Hadisi daga ABDULLAHI BIN
MAS'UD (RA) cewa: daga ANNABI mai tsira
da aminci ya ce: wanda ya yi wannan sallah
raka'a 12 sallama 6 a dare ko rana, bayan ya
gama sai ya yi yabo ga Allah madaukakin
sarki, da kuma salati ga Annabi mai tsira da
amincı.
Sannan kuma sai ya yi sujjada. yana halin
sujjadar sai ya karanta:
1 Fatiha kafa (bakwai 7)
2. Ayatul kursiyu (bakwai 7)
3 Wanan addu'a (10) goma:
"LAA'ILAHA
LAASHARIKA
WALAHULHAMDU
ILLALLAHUWAHDAHU
LAHU,LAHUL MULKU
YUHYI WAYUMITU WA
HUWA ALA KULLI SHAI'IN QADIR".10
4.. Ita kuma wannan addu'ar sau (daya 1).
"ALLAHUMMA INNIY AS'ALUKA 'BIMА
AAQIDIL IZZI MIN ARSHIKA: WA
MUNTAHAR RAHMATI MIN RITAABIKA, WA
ISMIKAL A'AZAMI WAJADDIKAL A'ALA
WAKALIMAATIKAT TAMMAT"
34.
Sai kuma mutum ya fadi bukatarsa yana
halin sujjadar. kana kuma sai'ya dago ya yi
tahıya ya yi sallama dama da hagu.
Annabi mai tsira da aminci ya ce:
"Kada ku sanar wa da wawaye wannan
addu'a domin kada su dinga amfani da ita
barkatai. kuma za'a amsa musu
IMAM HAKEEM ne ya rawaito
(Wannan addu'a babu shakka babban
makami ne wajen biyan bukatu, don haka ya
rage mai bukatu ya dukufa.
Bayan sun gama suka rufe da addu'ar
biyan bukata, suka tashi.
BABI NA HUDU
Bayan kwana biyu Hanifa ta tambayi
abbanta tana so, za taje gidan Aunty Sakina ta
kwana biyu.
Abbansu ya amince mata. Ta sanarwa da
mamainsu ita ma ta ce: "Sai kin dawo, а се
muna gai da su da kyau
35.
Hanifa ta shirya ta tafrgıdan Sakina "Salim
ne ya kai ta da shi da abokınsa Nazir. Hanifa na
zaune a gidan baya
Bayan sun isa gidan Sakina, sai suka shiga suka
sha hira sannan da yamma ta yi Sakina da
Hanifa suka shirya suka tafi well-care
Suka sayi kayan dadi, su lemo da
sauransu. Sannan Hanifa ta sayi fim na hoto. ta
sa a camerar ta, da yake ta taho da ita.
Bayan sun fito daga well-care sai Sakina
tafara daukan Hanifa a hoto, har idan sun ga
gidamai kyau a hanya sai an tsaya an dauka a
wajen sannan su wuce, har sai da suka karasa
Badawa
Hanifa na kaunar ta ga ta faranta wa
Aslam rai shi ya sa ta yanke shawarar ta dauki
hoton fim guda ta ba shi.
Sun sami kwana biyu ana daukan Hanifa a hoton
sannan aka karar dashi. Hanifa ta je beirut road
ta ba da a wanke mata a AGFA.
Ranar Juma'a su Hanifa da aunty Sakına
suka tashi da wuri don su yi 'yan girke-girken su
Matar yayansu ta haihu wato.
Ta haifi da namiji an sa masa sunan kakansa
wato Amin.
36.
Bayan sun gama hada kayan abincı sai
kuma suka fada wanka. duk suka gama suka
shirya cikin wani brown cotton lace. Anko za a
yi duk yan uwa har da iyayensu da iyayen
matan yayansu.
Bayan an hadu a gidan suna aka yi
shagali mai kayatarwa. Sai da aka yi sallar
magriba sai Hanifa tace da Sakina tana so, za
ta je gidan su Halwa. Sakina ta ba ta mukullin
motarta ta ce mata ta dawo da wuri saboda su
wuce gida.
Da isarta gidan su Halwa sai ta ci sa'a ta
tarar da su tare da Aslam da kannen Halwa a
falonsu suga hira
Halwa ta yi murna kwarai don ganin Hanifa
bazata.
Suka gaggaisa sannan ta shiga gai da mutanen
gidansu Halwa
Da ganin hotona sai Aslam ya ce lallai
lallai shi kam bazai ba da hotuna ba, daman
guda haka ya ce yana so.
Halwa tana ta mitar ita ba'a kawo mata ba
amma sam Aslam ya hana ta ko guda daya.
37.
Da ta samu 'yan dakiku sai ta ce da su za
ta koma, saboda auntyn ta tana jiranta a gidan
suna
Sukayi sallama ta ja motarta ta dau hanya. Yayın
da Aslam ya kasa tsaye ya kasa zaune sai
murnar daukan hotunan nan yake don ya
tabbatar da Hanifa na son shi sosai.
Bayan su Hanifa sun koma gıda sun
kammala komai za su kwanta sai Sakina ta ce da
Hanifa.
"Hanifa zabinki na auren Zubair ya birge
ni, Allah ya ba da zaman lafiya. Domin kin ga
yanzu a gidan biki har an gayyato meeting ranar
wata juma'ar saboda a fara shirin bikinku".
Hanifa ta kalle ta a hankali sannan ta се
da ita:
"Amma kin san me aunty Sakina? Wallahi
har yanzu ina jin son Aslam a raina. Kamar ma
ba aure za'a yi mini ba. ga shi ko Halwa na kasa
gaya wa zancen Zubair don ina ganin za ta gaya
wa Aslam"
Sakina ta ji tausayin kanwar tata sannan ta
ce da ita cikin muryar ban baki:
"Kada ki ji komai Hanifa Allah zai kawo
komai cikin sauki, amma dai ya kamata cikin
week din nan ki gayawa Halwa duk abin da kike
38.
ciki ciwon ya mace na ya mace ne, sai ki ga
ma ta Bà ki hadin kai kun samu hanyar nusar da
Aslam yadda al'amarin ya ke
Zancen auren Hanifa ya koma hannun
manya sai shirye-shirye ake yi. An sa ranar
daurın aure ya kasance wata biyu.
Yanzu Hanifa da Zubair ko da yaushe ana tare
don ko da a ofis ya ke yana bugo mata waya.
su dau awa daya ko biyu kafin su ajiye.
soyayyar su abar sha'awa ga kowa.
Tabbas shawarar Aunty Sakina ta yi amfani,
domin yanzu Aslam da Hanifa kamar wa da
kanwa haka suka zama. Soyayyarsu tana nan
lafiya kalau, sai dai ance fadan da ya fi karfinka
ka mai da shi wasa.
Haka ma 'yan gidan su Halwa, sun mai
da kansu kamar 'yan dangin su Hanifa, da su
ake shirye-shirye komai na bikin Hanifa.
Biki ya rage sati biyu aka kawo kayan lefe da na
sa lalle.
Kaya sun hadu kamar ba da kudi aka sayo su
ba. Komai dozin biyu aka zuba mata, a kalla
akwatin sun kai ashirin sai kuma kanana guda
biyu da kita shima guda biyu. Ashirin da hudu
kenan haka aka kawo su a cike da kaya. ko
wanne sai an danne kafin arufe.
39.
Gwal ma set hudu aka zuba acikin da manya
guda biyu sannah kirar white daimon guda daya
da kuma half set shima guda daya. Awarwaro
mai guda shidda-shidda quda uku. Agoguna
guda goma sha-daya.
.Da rotar ta sabuwa dal a cikin ledarta. A
bayan motar ma wasu kaya ne akwati biyu inji
ang Kayan ready made ne wasu kuma 'yan
dubai ne sannan da wata dalleliyar sarka (fashion
peart) da (wrapper) dallar America guda biyu
kudio dinki.
Katin biki ma daga Swizerland aka bugo
shi mai kyau da tsari.
Babu wani (events) da yawa.
Kamu ranar Laraba, sai tea perty ranar Alhamis,
ranar Juma'a a yi yini sannan a yi mothers night a
Lebanon Club. Ranar Asabar za'a kai amarya
sai ranar lahadi da daddare akwai Dinner party a
Chinese restaurant.
Zubairu Auwal, kyakkyawa ne amma ba
fari ba ne chocolate colour za'a kira shi dona
garin bakake shi fari ne kal.
Alhaji Auwal Naira, sunan mahifinsa kenan, suna
zaune a Mayu road.
40.
Allah ya yi wa mahaifin Zubair arziki,
mutumci. kyau da tausayi ga kuma uwa uba
rikon amana da son mutane. Alh. Auwal
haifaffen kasar sudan ne, yana da matarsa tun
auren fari, ko yaji ba ta taba yi ba, Suna da
va ya guda hudu Amal. Sadiya (Sunan
mominsu). Abdulhamid sannan Zubairu.
Amal ita ce babba a gidan tana aure acan
Sudan din a dangin mahaifinta. Sadiya ita ma ta
yi aure tana zaune a matan fada road tana
auren dan shugaban kasar Niger. Abdulhamid
kuwa yana Swizland da matarsa Basma, yana
aiki a swiz Bank.
Alh. Auwal ya dade da baro kasarsu
Sudan, domin yanzu akalla sun doshi shekara
bakwai a gidansu na Ibrahim Dabo road, kusa
da Aliyu Ibn Abutalib. Zubair kuwa a can aka
barshi har sai da ya gama kara tunshi ya kuma
kama aiki yanzu ma ya zo ganin iyayen shi ne,
to Hanifa ce ta tsai da shi domin tun ranar da ya
ganta a asibitin nan ya san ya samu matar
aure.
Zubair ya kasance da mai biyayya da
ganin girman na gaba da shi ga Addini, kamar
dan Sudais haka za ka ji idan yana karatun
Kur'ani.
41.
Hanifa an zama amare, ko ina sai labarın
auren' ta ake yi. kowa kuma yana musu fåfan
alheri da samun 'ya'ya na gari.
An gama gyara gidan da Zubair zai sa
Hanifa a ciki.gida ne da ya amsa sunansa na
gida, a Zoo road ya sayi gidan a hannun kwaran
nan mai sunaTahir (mamallakin Tahir Guest
palace).
Gida ya tsaru kamar dai wani rantsatstsen fadar
shugaban kasa.
Surar dawisu shine ainihin abin da idonka
zai dinga hango ma, kamar dai yanda yake baza
gashin nan nasa kore. A farkon gidan garage
dinsu ne mai kunshe da motoci na gani na fada
da kuma katon fili.
Akwai wata hanya wadda aka zuba kwalta
ya nufi cikin gidan. Idan ka bi kan kwaltar
ahankali sai ta kaika bayan gidan wanda babu
komai a wajen sai wani tafkeken swimming pool
da kuma garden a gefe.
A cikin garden din babu abin daba'a shuka
ba Apple, lemo na tsami da na zaki, gwanda,
Ayaba, Abarba, Baure, Peach, Kankana da sai
sauransu. Ko wanne dan itace ya sakata ya wala
a bangarensa.
42.
Akwai boys Quarters (BQ) a can gefen
gidan an zagayeshi da 'gini. Dakuna uku ne da
falo babba ko wanne daki akwai Air condition
da kuma fankar sama. Bangaren matar gida da
na maigida abin sai dại a yi shiru, don ba
magana sai talking.
Hanifa ta sami dakuna guda shida, da
dakin yara guda biyu na maza da na mata.
Akwai dakin baki (Guest room) guda daya da
babban falo a ciki da bandaki.
Akwai kicin dinta gudabiyu daya а
samadaya akasa. Kowanne dauke da kaya fal,
ba masakar tsinke.
Bangaren maigida kuwa, wato katon falo
ne, wanda idan da fili ne kawai za'a iya gina
gida mai dakuna uku har a samu kicin da
bandaki.
Kujerun falon ko wanne set dinsa guda goma
shabiyu ne da tebura a tsakiya da gefe. Fitilun,
falon ma abin kallo ne. Akwai dakunan kwana.
guda biyu da kuma sito a gefe.
An kawo amarya bayan da aka gama hidimar
biki da kuma bidi'o'l na malam Bahaushe.
Bayan iyayenta sun dadayi mata nasiha
da fadan zaman gidan miji sai kowa ya watse.
Yan siyan baki su shida aka bari. Da Halwa
43.
daRabi'at Aliyu Mohammed, Asma'u Abba Garko
da Halima Murtala Gaya, Hafsát Ibrahim da
Aisha (Indian girl).
Angwaye suka shigo aka kammala sayen
baki da kuma sai da fura da yakę ba su samu
damar zuwa sai da furar ba, sai angwaye suka
biya su kudinsu. sun samu dubu dari biyu da
hamsin.
Suka yi sallama da Amarya abokanen Zubair da
kuma motar gidan su Hanifa ta kwashe su sai
gida.
Gida ya zama daga Ango sai Amarya.
Ranar da Hanifa ta kwana bakwai sai ga
Halwa da kanwarta Rahma, suka zauna suka yini
suka sha hira.
Hanifa ta yi mugun kokari don har sai da za su
tafi sannan ta ce da su "don Ailah ku ce ina gai
da mama da Aslam".
Ranar da Hanifa za ta koma Zari'a suka zo
sallama da Hamida.
Bayan sun gama hirarsu za su tafi sai Hamida ta
ce da ita:
"Hanifa girma fa ya kama ki, sai hakuri
sannan ki dage da addu'a da kuma bin mijinkı
Ga wannan Addu'ar ki dinga yi ta zama a
wuri ce" "SUBHANAKAL LAHUMMA WA BI
HAMDIKA, ASH-HADU ANLA'ILAHA ILLA ANTA
ASTAGFIRUKA WA ATUBU ILAIКА".
44.
Kuma ko da yaushe ki kasance mai biyayya da
ganin girmån mai gidanki".
Hanifa ta ce da yayarta "To insha Allah zan yi
biyayya gareshi, Allah ya kiyaye hanya.
Hamida ta kara da cewa".
"Ga wani sirri kuma da zan gaya miki,
saboda ki samu jin dadin zaman aure.
Kin ga Hanifa ki lura da kyau zaman aure
sai da kwantar da hankali. Kuma kada ki
kuskura ki kasance mai cewa mijinki "Daga ina
kake?" ba ke ce mai iko da shi ba, shi yake iko
da ke. Ki barshi ya yi abin da yake so, idan kika
takurawa kanki saiya daina dawowa gidan, baki
kuma da katabus. Abin da ya fi ki yi masa tarba
ta musamman tare da nuna damuwarki ta
rashin dawowar tasa da wuri, sannan idan ma
tambayar ce sai ta biyo baya.
"Dan jira ba'a gama abincin ba har
yanzu". Ya dawo daga aiki a gajiye da kuma
yunwa, wannan ba dai-dai ba ne, Allah ya
taimaka.
"Sulaiman ya sayo wa matarsa karima
katuwar sarka da sabuwar mota mai kyau,
wancan satin. Wayyo ina ma nima na samu
kamar ta". Za ki sa shi ya zama kamar ba ya
gabatar da aiyukan da ya kamata a kansa naki".
Hamida ta gyara zamanta sannan ta ce daita:
45.
"Abin da ya kamata ko da yaushe shi ne;
ki kasance mài godiya a gareshi, mai yawan
addu'a gareshi. Ko wannen ku yana da hakkı a
kan dan'uwansa, ku kasance masu ba da hakin
juna. Idan abu ya taso masa ki kasance mai
kwantar masa da hankali maı yawan damuwa da
bukatunsa
Ko da yaushe ku kasance masu goyan bayan
junanku a ko ina. Ku kasance tare da juna ko da
yaushe. kuma ko da wane lokaci ku kasance
masu samun abin da kuke so. ki gaya masa
bukatarki cikin kwanciyar hankali. shi ma ki
tabbatar ba shi da damuwa".
Hamida ta kalli agogo ta ce da Hanifa tare da
mikewa tsaye:
"Kada dare ya yi mana a hanya Amarya,
sai mun yi waya ma karasa abin da ya rage
mana. Asha amarci lafiya".
Hanifa ta koma cikin gidan su ta fara
shirye-shiryen tarbar Angonta domin lokacin
dawowarsa ta kusa.
"BARKA DA SHANRUWA"
46.
Tammat.
Taku Siyama
(mrs. Idris)
1
40h ANNIVERSARY !!!
MUNA TAYA MAIMARTABA SARKI ALH. ADO
BAYERO (CFR LLD. JP)
(SARKIN KANO) MURNAR CIKA SHEKARA 40 A KAN GADON SARAUTA.
RANAR 11. Ga watan OCTOVER 1963-2003
ALLAH YA JA ZAMANIN SARKI
a
t
DAGA:
lyalan maimartaba
Sarkin kano
(maza da Mata)
"A YI SALLAH LAFIYA!!"
47.
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya