An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
HAUSABOOK.COM
HNL
BILKISU ADo BAYERO
2
HANIFA
BILKISU ADО
BAYERO
Harafi Publlshers KaAure Ni
BILKISUHAMUHD
BABI NA UKU
Washegari sai ga Umar da abokinsa
Usman. Usman shi ne wanda sukaje gidan sa
Jiya ba yanan. bayan sun gaisa sai suka shiga
hirar su.
Umar ya ce da Hanifa da Usman:
"Hanifa gaskiya na dauko abokin nan
nawa ne don ya zo mu yi magana dani,da ke a
gaban shi". Ya dan kalle su a lokaci daya
sannan ya kara da cewa:
"Kamar yanda kika riga kika sani ne, ina
sonki sosai da sosai,kuma ina muradin ki zama
matata, saboda haka nake ganin ya kamata ki
tsayar min da magana daya, wallahi sam bana
kaunar ganin wani ko wasu, suna zuwa wajenki.
Bana son kina kula wani bayan ni.
Gaskiya Hanifa ki gaya min gaskiyar ki a kaina,
domin ni aure nake so mu yi. idan kin amince
dani zan turo manya na gidanku da neman iri".
"Hanifa ta amsa masa da cewa:
"to kamar yanda ka tambaye ni, to dole
na gaya maka gaskiya ta. Ka san dai ni
budurwa ce ba bazawara ba saboda haka ban
1.
1
yi tsammanin masu neman aure na zan rabu da
su ba. Kai ma layi kawai ya kamata' ka bi kamar
kowa amma ba ruwanka da zancen na daina kula
kowa. Wa ya san gobe ai sai Allah
"Usman ya kalleta ya ce:
"Ni madai na goyi bayan ki Hanifa.ka ci
gaba kawai da gwada sa'ar ka, idan Allah yayi
matar kace duk iya yawan masu zuwa wajentá
dolesu hakura ka dauka. Saboda haka mun barki
lafiya".
"Umar ya dan ja numfashinsa tukunna
sannan ya ce da su gaba daya.
"To, sai mu tafi din. Sai da safe".
Hanifa da ta shiga gida sai ta dauro alwala tazo
ta ta da sallah, ta yi salla raka'a biyu, bayan
sallama sai ta kara da ALLAHU ALLAHU RABBIY
LAA 'USHRIKU BIHI SHAI'AN sau bakwai.
Sannan ta yi fatiha kafa daya da salatin Annabi
goma.
{Wannan addu'ar ana yin ta ne ayayin da
wani abu na bakin ciki ya faru ga musulmi, ko
kuma mutum yana cikin damuwa. To sai ya dinga
karanta ita wanan addu'ar kafa bakwai. To Allah
zai yaye masa duk abin da ya dameshi.
Saboda an samu Hadisi daga ASMA'U
BINT UMAIS (RTA) cewa: Annabi mai tsaira da
aminci ya ce da ni "Bari in sanar da ke wata
2.
addua'a da za ki dinga karanta wa sau bakwai a
duk lokacin d'a wani abu na bakin ciki da bacin
rai ya sameki". Abu Dauood, Ibn Majah ne suka
rawaito.
Hanifa ta koma gidansu, bayan kwana
uku aka koma makaranta. Yanzu basu da
isasshen lokaci nasu na kansu sai na karatu
{Final exam} din da za su rubuta an kafe musu
{time table}.
Ya kasance kullum su Hanifa ana class
area, sannan ga practical dinsu da aka fara.
Kullum Hanifa tana karanta Bismillah kafa (786)
da asuba dab da bullowar alfijir tasha a ruwa {ta
tofa}. Duk wanda ya jure yin wannan addu'ar
hakika zai haddace duk abin da aka koya masa
a kansa. Ana karanta wa yaro ko yara a ba su
har tsahon kwana bakwai mujarrabi ne.
Lokacin jarrabawa ya kawo kai Hanifa har rama
ta yi, saboda ko abincin kirki ba ta iya ci sosai.
Aka dauki wata guda ana rubuta jarrabawa
sannan ranar {final paper} dinsu aka yi send off
party da yamma bayan send off kowa ya bi
iyayensa ko 'yan uwansa suka tafi motar Ya
Aslam suka shiga bakinsu kowa har kunne an
kammala secondary school.
3.
Ranar speech & prize giving day ta zo duk
'yan candy suka taro, an dinka masu wata riga
irin ta graduation koriya da ash (ruwan toka) a
gaban rigar.
Ranar kowa yana cike da farin ciki da
annashuwa har sauran 'yan makarantar ma
saboda a ranar aka yi visiting.
Hanifa ta samu kyaututtuka sai ka zata
don ita aka gina makarantar saboda takarbi
lambar yabo ta kowanne bangare. Kyautar ta
kuwa an bata sama da goma.
Hanifa ta ga gata sosai kowa ya nuna mata
kauna, yayyanta maza da mata kowa ya
bayyana. Mazan sun zo da matansu da 'ya'yansu
hakana matan duk da 'ya'yansu da mijinsu suka
zo mata, kowa da tasa kyautar zuwa gareta.
Bayan an watse aka kuma ware gangar
bature a rediyo aka saki kidan Celinedion da
Janifer Lopez.
Hanifa na zuwa gida bayan ta yi Sallah sai
ta dauko carbinta ta yi addu'a kamar yadda ta
saba, sannan ta fara addu'a ga mahaliccin kowa
da komai. Hanifa ta yi godiya ga Allah, ta yi kirari
ta yabi Annabin rahma ta kuma roki alherin
duniya da lahira.
4.
Hanifa ta yi sujjada bayan ta yi salatin Annabi goma sai ta fara da:
"Rabbana laa tu'akhidhnaa' in nasiina au
akhta'naa. Rabbana wa laa tahmil alainaa isran
kamaa hamaltahu alal ladhiinamin qablinaa.
Rabana wa laa tuhammilnaa maa laa taaqata
lana bihi, wa afu-anna waghfir lanaaa war hamnaa, Anta maulaa naa fansurnaa alal
qaumil kaafiriin". Sau uku sannan ta kara da
salatin Annabi goma ta dago ta shafa fatiha.
Tun da ta kwanta ba ta tashi ba sai da
aka kira sallar Asuba. Tana tashi ta shiga ta yi
wanka ta zo ta yi sallah, ta riga ta saba duk
lokacin da ta tashi daga barci sai ta yi wanka
tun a makarantarsu.
Ta kan hada da wankan janaba a yayin wankan
ta, kasancewar bata iya tuna mafarki idan ta yi
sai ta yanke wa kanta wanka kafin salla,
saboda gudun kada ta kamu da janaba yayin
baccin ta bata sani ba ta yi şallah.
Bayan tabi masallacin unguwarsu aka
idar da sallah, sai ta dauki kur'aninta ta fara
bitar karatu.
Bayan an kwana biyu sai Hanifa tashirya
domin ta tafi Zaria tare da yayarta Hamida,
suka shirya, Zaria ta diba.
5.
Dasuka isa Zari'a sai suka tarar da mijin
Hamida ya tafi'Yola sai bayan sati daya zai dawo
Sannan Hadiza wata makociyarsu take gaya
mata zancen auren kanwarta Hafsisy wanda
ranar laraba za a yi kamu. Tare da aiko mata da
goron bikin.
Sun shirya zuwa bikin ita da Hanifa sannan suka
shiga cikin gari da yamma.
Ranar kunshi suka je gidan da ake
kunshin amarya suka tarar da gidan a cike.
kamar hadin baki sai Hanifa ta fita kofar gidan
don ta dan tattaka, tana fita sai ga motar Umar a
kofar gidan Hamida, ta yi matukar mamakin
hakan sosai.
Hanifa ta karasa wajen Umar da fara'arta.
ta ce da shi:
"Yallabai ka ban tsoro fa" ta dan rike habar
ta tare da girgiza kai sannan ta sake cewa da shi:
"Don Allah daga ina kake, kuma yaya aka
yi kasan ina nan?
Umar ya dan kauda kai ya gyara muryar
sa sannan ya ce da ita:
"Daga Kano nake, kuma wajenki na taho.
ba ko sallama aka taho shi ne ni kuma na je
gidan Sakina ta gaya min kin taho nan ta kuma
bani address din nan".
6.
Hanifa ta yi dariya sannan ta cе:
"Wallahi ba haka ba ne Umar, kawai dai
tafiyar ce ta zo amma ai ranar Juma'a zan
dawo.
Umar ya dada gyara tsaiwarsa sannan
ya ce tare da sanyayar da muryarsa
"Hanifa kin dauke mini tunani na gaba
daya, kin gama tafiya da ruhina ina tabbatar
miki da cewa akalar rayuwa ta a hannunki take,
ki yarda da ni don girman manzon Allah na zo
na dauke ki na mai da ke gidana a matsayin
mata ta ke ce kadai burina a rayuwa".
Hanifa duk abin nan tana sauraronsa
yayin datake kallon kasa, sam hankalinta yabar
jikinta, tana dai jin maganar da yake yi samasama.
Ta dago kanta daga kallon kasa sannan
ta ce da Umar.
"Ina son. ka bari sai ranar litinin da
yamma kaje gidan mu,ka same ni, sai mu
karasa magana".
Umar ya kawo wani (envelop) ya bata
sannansukayi sallama da junansu. Ko da
Hanifa ta koma bata tsaya a gidan bikin ba
kawai sai ta tafi gida ta shiga daki ta zauna ta
hau tunani.
7.
A gaskiya akwai abin da Hanifa take
hangowa a rayuwarta, duk data san ba ta da
wani 'yancin yin abin da ta ga dama, tun da tana
da iyaye da na gaba da ita A kan kanta da ita
take da iko da kanta, wannan yana cikin abin da
ta ke bukata a wajen irin mijin da y kamata ta yi
rayuwarta da shi
Na farko dai ya kamata ta samu wanda yake
sonta saboda ita, wato don wacece ita: ya iya
kasancewa tana da kudi, amma ba kudin nata
kake so ba. Ka sota idan sunanta Zainab, ka sota
saboda ita Zainab ce, mummuna ko kyakkyawa.
Sannan kuma ta sami namijin da zai
kasance mai sa ta farin ciki a ko da yaushe.
Tabbas ko wacce mace tana da burin mijin ta ya
kasance mai kyautata mata da faranta mata. Ba
wacce za ta so ta bata lokacinta da namijin da zai
sa ta bakinciki a ko wanne lokaci, duk tsahon
lokaci. Farin ciki yana sahun farko a rayuwar mu
ta 'yan Adam, masu 'yanci Tabbas kuma akwai
bukatar yarda a tsakani. yarda da juna ya taka
rawar gani a neman nagari. Ko wanne mutum.
mace ko namiji, yaro ko babba yana neman
wanda zai yarda da shi. Tana matukar bukatar
kasancewa da namijin da za ta kasance ya
zamar mata madogara a duk lokacin da ta bukaci
wani a kusa daita ko wanda za su yi magana da.
8.
Surar datafi bukata a wajen maza kuwa ya
kasance ba wai mai kiba ba,' ko ramme ko
muna kasusuwa. A'a wanda yakeda nama a jiki.
Mata suna bukatar maza masu murdadden jiki.
Ya kansa mace ta ji ta zama cikin sanin cewa
atsaretake a kowanne lokaci kuma a ko inakuke
tare. Hakannan wanda zai kasance ya sa ta ta
dogara da kanta ta tsaya a kan kafarta.mata
sun kasance masu kosawa da mazan da duk
wani motsin mace sai sun saido a kai. Namiji ya
kasance mai yawan kawo sabon salo na
rayuwa,ko wasanni da sauransu.
Akwai kuma abin da ya fi tayar mata da jijiyoyin
hankali yanda ta lura da mazan yanzu da basu
dauki hulda a koda yaushe, tana mai neman
namijin dazai kasance mai hulda da ita a ko da
yaushe, wala'Allah a waya ko a wasika, ko da
ba ku yi magana ba idanun ku za su fidda muku
maganar a tsakaninku. Mata suna saurin
gajiyawa da mazan da suka kasance ga sunan
ne dai.
Sannan kuma Namijin da zai kasance
mai yarda da kansa. Namijin da ya kasance ko
da yaushe yana jin kunyar jikinsa, (musamman
can kasa) yana zubar da kansa a wajen mata.
Rashin yarda da kanka yana nufin, yana kuma
nuna cewa ba ka cika isasshen namijin ba.
9.
Kuma yana nufin ba za ka iya daukar nauyinta
ba
Ya kuma kasance wanda zai karbi jikin ta a
yanda yake, ramammiya, mai kiba, a'a katon
mazaunai. manyan mama. Abin da yafi sauki a
zaman takewa shine kai namiji ka koyi yabon
matarka da jikınta. yanda ta zama ta yı
kyau.kayan sunyi mata kyau ko da yaushe don a
zaman tare ba'a girma kuma ba'a gajiya. Kamar
yanda ka dauke ta a matsayin wacece ita.
* * *
Ranar da Hanifa ta koma gida da yake
sunje kano da wuri, saboda a gida suka yi sallar
la'asar. Wanka kawai ta yi sai ta shirya ta dauki
mota suka tafi gidan su Halwa ita da Zahra.
Da isar su gidan su Halwa sai ta tarar da
ita tare da mamansu a falo suna kallo. Halwa ta
tashi ta tari Hanifa tana nuna matukar farin cikinta
da dawowar Hanifa ta riko.hannun Zahra suka
dawo wajen mamansu Halwa.
Hanifa ta durkusa ta gaishe da mamansu
Halwa. Suka tashi suka nufi bangaren su Halwa
suka zauna a falo, Halwa ta tafi kicin ta hado
musu abinci da abin sha kala-kala. Ta dawo.
10.
Bayan sun kammala sun yı sallar
magriba sai ga Aslam ya shigo yana shigowa
kofar gida ya ga motar gidansu Hanifa ya san
cewar ta zo.
Ya shigo tare da sallama. sannan ya ce da
Hanifa yayinda ya ke neman zama:
"Ranki ya dade. Gimbiyata. saukar
yaushe?" yana fada yana dariya irin ta
hadaddun 'yan maza.
Hanifa bata amsa masa ba sai dai tayi
kasa da muryarta sannan ta ce da Aslam:
"Barka da dare an dawo lafiya?" ba ta ko
jira ya amsa ba ta fara kade mayafinta tana
niyyar yafawa tare da dauko jakarta da take a
gefe.
Halwa tana kallonsu bata ce komai ba
don ta san kanun zance, ai ba su yi aune ba sai
Aslam suka gani a gaban ita Hanifar gwiwa
biyu a kasa yana faman daga hannunsa duk
biyun,. wato yana neman afuwa sannan ya
samu ya.ce da muryar tausayi:
"Don girman Allah Hanifa kada ki yi mini
haka, wallahi bani da lafiya ne shi yasa ban zo
ba. Don girman soyayyar ki da manzon Allah ki
koma ki zauna".
11-
Hanifa duk tausayinsa ya kama ta tabbas
Aslam yana kauna ta. don Hälwa ma ta gaya
mata cewar baı da lafiya
Ita kuma ta yi masa hakan ne kawar don ta
nuna masa bata ji dadın saba alkawarın da ya y
mata ba Ya ce zai je Zari'a amma ko mai kama
da shi ba ta gani ba
Aslam ya zauna a kasa a kusa da Hanifa
sannan ya ce da Halwa dan bamu waje
sahibata".
Halwa ya ja hannun Zahra suka shiga cikın
dakinta. yayin da Hanifa da Aslam suka kasance
a falon Aslam ya ce da ita yana mai sanyayar da
muryarsa:
"Hanifa ki yi Hakuri ina kwance Ulcer ta
kayar da ni. shi yasa ban cika miki alkawarin da
na yi ba
Hanifa ta saki fuskarta sosai sannan tace
da shi:
"Wallahi Aslam na hakura komai ya wuce.
ya ya jikin naka?"
ya ce da ita:
"Na samu sauki sai dan abin da ba'a rasa
ba"
"Allah ya kara sauki ya kuma kare ka da
karewarsa".
12.
Aslam da Hanifa suka ware ana ta diban
hira, har'sai wajen tara saura kwata sannan su
Hanifa suka kama hanyar gida ita da Zahra.
yayin da Aslam da Halwa suka yi musu rakiya
har waje, wajen motarta.
Ranar laraba ne.har Hanifa tayi shirin
kwanciya sai ga Salim ya shigo, yake ce mata
ga Zubair ya zo yana waje a falon baki.
Hanifa ta dauki irin hijab dinnan mai ribi
biyu baki da yalo ta saka mayafin ma mai kala
biyun ne amma rabi da rabi ne ko wanne zaka
iya sawa.
Ta dauki lemo da kofi guda biyu ta sa a
kan faranti, sannan ta tafi dakin da aka ce mata.
Ta shiga ta sami Zubair a zaune a tsakiyar 3
seater. Ta ajiye lemon a gabansa sannan ta
koma gefe ta zauna tana murmushi.
Bayan sun gaisa ne, ta zuba lemon a
kofin ta sha kadan sannan ta zuba masa.
Suka samu lokaci suna hira sannan sai
Zubair ya ce da Hanifa:
"To Hanny ni zan gudu don dare ya fara
yi kada su mama su ga kin dade.
Hanifa ta yi dariya sanan ta ce da Zubair:
"To mai sanyina Allah ya kaika gida
lafiya
13.
suka yi sallama cikın kauna da begen juna suka
rabu da alkawarin dawowa jibi
Ya bata wasu kaya a cikin kwali guda biyu
ya ja motarsa ya fita daga gate din. yayin da ita
kuma Hanifa ta kama hanyar cikin gida yayin da
kayan suka riga ta shiga.
Ranar da Abdul ya zo ya ga kamannin
Hanifa na tsoro wanda bai taba gani ba a
rayuwarsa. Sai da suka dau awa biyu yana bata
hakuri a kan abin da ya faru.
Hanifa dai dama da biyu ga sonsa da ya
fita a gabanta ga kuma haushin yanda suka yi
ranar party.
Dole suka rabu a sanyaye.
Ranar da ya zama wata daya dai dai da
kammala makarantar su Hanifa yaya salisu ya zo
suka tafi zaga gari da salim da Hanifa sannan
auta Zahra aka je well-care da see sweet &
bakery aka kwaso kayan zaki da Ice cream. Suna
dawowa gida aka yi bajet na kayan kwalama
wasu kuma aka saka a freezer don karsu narke.
Aka sha hira aka yi kallo har dai sai da
dare ya tsala sannan aka kwanta.
14.
Hanifa abin duniya ya sha mata kai
sosai, domin yanzu duk kullum sai ánzo ance
ana sallama da ita. Idan dare ya yi kuwa ta
kwanta ko bacci bata iya yi don tsabar tunanin
halin da take ciki. Har bata sanin lokacin da
bacci ya ke saceta.
Hanifa babban abin da yafi damunta a rayuwa
bai wuce yanda aurenta zai kasance ba, ta san
yanzu lokaci ne kawai iyayenta suka bata,
kuma tana da yakinin ranar duk da Abbansu ya
yunkuro bata da katabus. A ranta da jikinta ta
riga ta san cewa dole dai miji daya za ta kawo a
aura mata. To amma a gaskiya Aslam daZubair
duk kansu sun cancanci zu sama abokan
rayuwarta.
Duka wasu samari da manyan mutane
da suke zuwa wajenta ita basa gabanta sai su
biyun nan ne kawai suka ciri tuta.
A can wani garin kuma a cikin zuciyarta,
banda tunanin halin da za ta shiga idan bata
auri Aslam ba ba bu wani tunani. "Gaskiya ina
son Aslam ina muradin na zauna tare da shi,
kamar yanda na san haka ne a nasa zuciyar".
Ranar ta kasance Juma'a mai taken ta
na babbar rana.
Bayan an sakko daga masallaci sai ga Aslam
da Sani. Wato babban abokinsa, da kuma
Halwa.
15.
1
Halwa ta shiga suka gaisa da mamansu Hanifa
sannan 'aka kaiwa su Aslam ruwa da lemo mai
sanyi.
Halwa ke sanar da ita cewar suna so ta raka su
gidan yayarsu wato Ilham. Hanifa ta ce:
"To Allah ya sa mama ta barni".
Hanifa ta fita, ta sami mamansu ta gaya mata.
Sai maman nasu ta ce:
"A'a Hanifa, ki zauna a gida sai dai wata
rana kya je ku gaisa"
Hanifa ta fara shagwaba tana cewa:
"Haba mama, ga Halwan nan fa tana daki,
yanzu sai na koma nace kin hanani zuwa? Ai
baza ta ji dadi ba tun da ita tana ganin duk mun
zama daya a wajenki".
Mama dai ta ce ta amince a je amma a
dawo da wuri:
Bayan sun fita sai suka shiga bayan mota
suka nausa. Daman sai da suka kara yin kwalliya
a dakin Hanifa kafin su fito.
Tun da Hanifa ta shigo motar Aslam ya
kasa dauke kansa daga kallon ta, har kara saita
madubin motar yake yi a gaskiya shigar ta Hanifa
16.
ta tafi da ruhin Aslam ba Aslam ba ma duk mai
rai zai so ya kalli wannan tauraruwa ya kara.
A haka dai suka karasa gidan Ilham suka
tarar da ita tana kallon film din Hausa na
kamfanin Maishunku Movies, wato film din sa
na Tangarda.
Ilham ta yi murna sosai da zuwan su, ta
karbe su cikin farin ciki tare da nuna musu
kauna.
Gidan ya hadu sosai kamar ba a Nigeria ba,
hatta da kicin dinsu na girki sai da aka sa (AC
air condition) guda biyu. Sannan ga wani inji a
kusa da (cooker gas) wanda ake saka shi daga
sama, in dai ana girki aka bude shi to duk
hayakin da turirin girkin zai bi ta ciki, ba zai
wanzar da shi a kicin dinba.
Gidan ya yi masifar yi wa Hanifa kyau. Ilham ta
ringa nunawa Hanifa kauna, tareda haba-haba
da ita.
Nan da nan aka kawo musu kayan snack da
lemo da soyayyun kaji.
Aka dauko musu album suka kalla, da lokacin
sallar la'asar ya yi suka je suka yi salla a dakin
Ilham, sannan Ilham ta hadawa Hanifa sha-tara
ta arziki.
Cikin kayan da Ilham ta bawa Hanifa har
da Less da super holland sannan ga takalmi da
17.
jaka da daı kayan kwalliya irin na mata har da
turare
Bayan an yi sallar'magrihba sai suka fito
domin a kai Hanifa gida.
Aslam ya ji dadi sosai shima don yana ganın duk
wanda ya yı wa Hanifa hidima kamar shi ya yi wa
Suka kaita gida sannan aka sauke Sani a
gidansu shima. Ya Aslam da Halwa suka dau
hanyar gida suma.
Bayan Hanifa ta shiga gida sai ta zarce
dakin Haj. Amarya kamar yanda suke gaya mata,
ta kai mata kayan da llham ta bata ta kuma gaya
mata yanda aka yi ta na ciki da bata labarin irin
haduwar da gidan ya yi da kuma irin mutumcin da
ta nuna mata..
Washegari da daddare sai ga Abdul ya
bayyana, bayan ya aika ta fito sai suka koma
falon gidan suka zauna. Ba su dade da zama ba
sai mai gadi ya zo ya sanar da Hanifa cewar ta yi
bako.
Cikin sauri tace da Abdul tana zuwa ta fito
don taga mai neman ta. Tana fitowa sai suka yi
ido hudu da Aslam.
Aslam yana jingine da jikin motar sa, yana
kallon ta cikin sakin fuska sai ya ce da Hanifa:
"Ya malama ina gajiya? Ya ya kuma
mutan gida?"
18.
Ta kalleshi yayın da ta lumshe idanun ta ta ta
ce da shi:
"Ina nan kalau da ni, kazalika mutan gida
duk lafiya. Ya naku 'yan gidan ina ka baro min
Halwa?"
ya kalleta ya ce ita tare da murmushi a
fuskarsa:
"Nabar miki Halwa a gida, don har ta
shirya zamu taho na ce kuma na fasa zuwa da
ita. Ko a dawo lafiya ba ta ce mini ba ta koma
gida, na san sai na koma zan tarar ana yi min
fushin nata"
ta bude baki za ta yi magana kenan sai
ga Abdul ya fito daga falon, don ya gaji da jiran
gawon shanu.
Aslam yana ganin Abdul ya fito daga
falon sai ransa ya yi masifar baci, nan da nan
ya canza fuska kishi ya bayyana a tsakiyar
kwayar idonsa.
Sannan ya kalli Hanifa tare da cewa "Wannan
kuma fa" muryarsa da alamun damuwa a
cikinta.
Abdul kuwa can gefe ya tsaya kusa da
motarsa, alamun cewar zai tafi, don ba zai iya
kwasar kwandon bakinciki ba.
19.
Hanifa ta ce da Aslam:
"Ban gane abin 'da kake nufi ba" don ta
lura da yanda fuskar sa ta canza don ganin
Abdul, kuma ta lura da yanda yake magana a
wani gadarance, shi yasa ita ta dan canza fuska
amma ba wai nuna wani abu ba.
Aslam ya се:
nufi ba"
"Oh! Ai dama ba zaki gane abin da nake
Hanifa ta yi 'yar dariyar mugnta fa ce:
"To daman ya ya za'a yi na gane abin da
kake nufi"
Aslam ya gama lura da cewar ta mayar da abin
na wasa sai ya ce da ita yana mai kau da kai
daga kallonta.
"To shikenan tun da ba ki gani ba, to
yanzu dai ya za'a yi?"
sai ta ce da shi:
"Ka. dan jira ni, naje na sallame shi na
dawo!"
ko amsa bai bata ba sai ya koma mota ya
zauna.
Ta juya ta nufi wajen Abdul wanda ya riga ya
gama sarewa da al'amarin Hanifa har zuciyarsa
20.
ta yanke masa shawarar ya saurara haka nan
tun bai zo yana da na sani bа.
Ta karasa wajen Abdul, ta bashi hakuri sannan
ta ce da shi:
"Abdul ba dai tafiya ba na ga ka dawo
wajen mota"
ya yi dan murmushin yake ya ce da ita:
"To Hanifa! Ai gwanda na tafi tun da mai
wuri ya zo sai mai tabarma ya nade ai. Da
alama da wancan za'a dai-daita?".
Ta yi kamar bata san mai yake nufi ba ta kau da
kai sannan tace:
"To Abdul na gode ka gai da mutan gida,
sai da safe".
Daga haka sai Abdul ya shiga motarsa
ya ja. Hanifa kuwa ta juya zuwa wajen Aslam.
Wanda a lokacin da Hnaifa take wajen Abdul
zuciyar Aslam har neman fadowa kasa take ga
wani kululu da ya zo masa wuya
Ta yi kamar minti biyu da tsayawa a
wajen Aslam amma sam bai nuna alamun ya
san ta karaso ba ma, sai da ta ga bai da niyyar
amsa mata sallamar da ta gabatar tun zuwan
nata sannan ta dan buga motar tare da kara
21.
wata sallamar. ya dago a hankali ya amsa tare da
cewar
"Har ya tafi ne?" ya dan saki fuskarsa ba
kamar farkon ganin Abdul bа.
Ta amsa masa da cewar "Ya tafi"
Suka dan taba hira sannan Aslam ya ce
"To rabin ran! Zan gudu sai yaushe kenan
zan ganki?"
"Sai wata rana" in ji Hanifa.
"Yaushe ne kuma wata rana?" cewar
Aslam yana dariya
"To ai ni ban san mezan ce maka ba, ai ni
ko da yaushe ina nan kawai dai sai ka zo" Hanifa
ke fada a cikin farin ciki.
Aslam ya ce da ita:
"To okey!