rana dole matar tashi ta tafi
idan zaman ta ya kare! Ni kuwa fa? Duk rintsi
muna a tare da shi".
Hanifa ta nisa ta ce da Halwa
"Ba wani nan, Allah yanzu haka ma ya mantada
.wata Hala a rayuwarshi".
Halwa na jin Hanifa, sai ta yi banza da ita
don ta san Hanifa tsokanarta take yi.
Can dai har sun shiga dakinsu suna shirin
bacci sai Halwa ta ce:
"Amma dai Hanifa kin ci mutunci na! Ai na
tabbatar miki da cewa in dai Ya Aslam zai manta
22.
da ni to zai manta da rayuwarsa. Don baki san
yanda ya ke mutuwar kauna ta ba!"
Hanifa ta yi sauri ta zauna a kan godo
hade dadafe kirjin ta (wai ita razana) sanna ta
ce:
"Ke halwa ko dai da gaske zuciya ta
take? Anya kuwa Ya Aslam din nan wanki ne?
ko dai friend dinki ki ke boye min".
Halwa ta yimurmushi sannan ta ce:
"Lallai ma Hanifa kin samu lafiya, wan
nawa ne saurayina? Wallahi Tallahi kin ji na
rantse miki, Wa na ne ubanmu daya da shi,
kawai dai haduwar jini ce"
Hanifa ta kuma takalarta da cewa:
"Eh mana wanki ne amma wan... mhm
dai bari na yi shiru ba'a bakina ba".
Halwa ta kufula ta ce:
"Fadi mana 'yar iska, ai gwanda na fara ji
daga bakinki, a kan wani ya fada"
Hanifa dai ta share ta kamar ta mance da
ita a dakin ma. Sai da Halwa ta ga da gaske
Hanifa kyale ta za ta yi sai ta fara nemo labarai
tana fada duk dai don Hanifa ta yi mata magana.
23.
(Halwa yarinya ce mai son magana da
barkwanci).
"Hanifa kinga new comer din nan da aka
kawo hostel dinmu dazu 'yar unguwarmu ce fa!"
in ji Halwa".
"Ke Halwa Wallahi kalan dangi ne da ke,
kowa kin sanshi" sai ta kyalkyale da dariya,
Hanifa ce.
Haka su Halwa aka cigaba da hira kamar
gaske, can sai aka kuma dawo wa ruwa.
Halwa tafara zancen Aslam as usual sai Hanifa
ta ce:
"Gaskiya Halwa na gaji da hirar Aslam din
nan, ke kullum ba ki da wata hira sai ta Aslam.
To Wallahi in dai hirar sa za ki yi, to sai dai ki yi
ke kadai don Wallahi sai na tafi wani hostel din
na kwana a can" ta dan sha mur sannan ta kara
da cewa:
"Kinga a can ma. yi hirar arziki da
mutane".
Halwa ta daga ido ta ce da Hanifa
"Wallahi Hanifa nima na lura kin kosa da
hirar Ya Aslam, amma ai hirar arziki ce, a kan
mu zauna mu yi ta hira har mu shiga yi wa
junanmu karya ai gwanda mu yi hirar 'yan
gidanmu". 24.
Tadan daga idonta ta kalli Hanifa ta kara da cewa:
"Kuma Wallahi Hanifa da ace ba mu da
zance a rayuwar mu sai yi da mutane ai gwanda
ace kullum zance daya muke yi. don kin san
idan hirar 'yan makaranta za mu yi kamar muna
cin naman mutane ne fa".
Hanifa ta ce:
"To Halwa mu yi hirar Ya Aslam, kin san.
wanki wana ne nima, wana kuma naki ne. kuma
daga yau kullum ma idan muka hadu hirar ya
Aslam za mu yi safe, rana, dare". Sai suka sa
dariya.
Ranar Asabar saura kwana biyu su fara
Jarrabawar su, Hanifa tana kwance a dakinsu,
sai wata (Junior girl) ta zo ta ce da ita:
"Aunty Hanifa wai kizo an zo miki.
Hanifa ta tashi ta gyara jikiņta ta saka
(house wear) dinta ta yi gate.
Tana zuwa sai ta ga ashe su Abdul ne da
shi da abokinsa Mustapha.
Hanifa ta karasa inda suke, ta tarar da su,
suka gaisa daAbdul.
Su Abdul ba su dade ba suka ce za su
tafi saboda daman da kyar aka barsu suka
ganta, saboda sun kusa fara (exam)
25.
Sai da su Abdul suka dan shiga motane
sannan sai ya ce da Hanifa:
"Gimbiyar matsayi ya ya na ga kamar ba
ki yi farin ciki da zuwan namu bane?"
Hanifa ta yi murmushi sannan ta ce:
"Ba haka ba ne Abdul, kawai dai bana jin
dadin jiki na ne, sannan ga karatu, ka san yanzu
ba mu samun isasshen hutu sai karatu".
Haka dai suka yi sallama da shi ta juya ta
koma makaranta da 'yan kayan provision da ya
zo mata da su. Su Abdul kuma suka dau hanyar
bairn makarantar.
Gaskiya Abdul yana son Hanifa sosai; yanzu
kayan ma da hado ya. kawo mata masu yawa
datsada. Ba'a magana.
Bayan Hanifa ta koma hostel, sai ta fara
tunanin anya ba abin ba ne yake neman fadawa
a kan Abdul. Tabbas gaskiyar shi sam ba ta yi
farin ciki da zuwan nashi ba ko me ya sa? Don
da can idan Abdul ya zo har ba ta son ya ce zai
tafi amma yau sai ta dinga jin kamar ta kwala
ihun bakin ciki, sam ba ta son ko ganinsa.
Hanifa ta ceda zuciyarta "Son Abdul ya.
fara raguwa. Gaskiya kan na yi la'akari da hakan
don yanzu ko tuna shi ba na sonna yi a raina.
26.
*
Bayan su Hanifa sun gama Jarrabawar su sai aka ba su hutu.
Da Hanifa ta kwana bakwai a gida sai tahada kayanta ta tafi hutu gidan yayarta Sakina
Ranar Laraba Hanifa suna zaune a falo tare da
yayarta sakina suna hira, sannan a gefe T.V a
kunne tashar (Zee music) sai ga mai gadansu
Sakina ya shigo,
Bayan ya yi sallama sannan sai ya gaishe da
uwargijiyar sa da kąnwarta. Bayan ya tashi sai
ya ce da Hanifa.
"Hajja wai ki zo inji wata mata a waje,
tana motarsu a zaune"
Hanifa ta yi sauri ta'ce da Baba maigadi
(Haka suke ce masa):
"Ni aka ce? Baka san su waye ba kuma?"
Ya ce da Hanifa "Wallahi ban sansu ba".
Ta ce asanyaye "To ga ni nan".
Har ta tashi za tatafi sai Sakina ta ce da ita a
yayin da ta tsira mata ido:
"Wallahi Hanifa babu ruwana idan kikа
fita aka sace ki ace, ai gidana kikazo,tun da ba
kisanko waye ba kada ki fita. To wai ni waye ma
ya san ki a nan wajejen balle ya zo nemanki?
Kika sani ma ko 'yan yankan kai ne, yadda garin
27.
nan ya baci da satar mutane ba namiji babu
mace. Wallahi kađá ki fita".
Hanifa ma dai jikinta ya bata cewarkada
ta je tun da basu san ko waye ba. Sai suka buga
waya bakin gate din, wajen Baba mai gadi.bayan
ya dauki wayar, sai Sakina ta ce da shi ya
kirawo mai neman Hanifa ta dau waya.
Baba maigadi yayi wa matar magana ta
zo tadauki wayar, ashe ma Salimat ce anan fa
aka yita dariya, Hanifa ta ba wa Salimat labarin
yadda suka yi a cikin gida ita ma ta yi ta dariya.
Sannan sai da suka gaisa da Sakina sai take
cewa da Sakina abin da yasa ba za tashigo ba.
Hanifa ce batazo mata sunan 'yarta da akayi ba
bayan sun yi da ita za ta zo. Sakina ta ce da
Salimat:
"Salimat ki yi hakuri da Hanifa amma za
tazo insha Allah. Sanin ta ce mata ta shigo mana
ko ruwa ta sha. Salimat ta ce "A'a sai dai idan
kin zo din nima nazo". Sai ta ce da Hanifa:
"Amma yanzu wajenki na zo, don Allah
Unguwa za ki rakani yanzu zamu dawo ki
gayawa yaya Sakina".
Hanifa ta ce "to gani nan fitowa".
Suka yi sallama, Hanifa ta gaya wa yayarta.
sannan ta fita suka tafi ita da Salimat.
28.
Bayan sun dauki hanya sai Salimat tace da Hanifa.
"Bari mu fara zuwa Hotoro G.R.A
tukunna". Bayan sun je Hotoro suna zuwa aka
bude musu kofar gidan suka şhiga sai Salimat ta
ce da Hanifa tana zuwa ta shiga cikin gıdan,
Hanifa kuma ta zauna amota. Bayan mintina
biyar sai Salimat ta dawo, suka bar gidan.
Bayan sun hau hanya ne sai Salimat ta
cewa da Hanifa:
"Hanifa gidanmu fa Zamu". Sannan ta
Kalle ta lokaci daya kuma ta mai da kallonta ga
gaban motar.
"Hanifa tace da Salimat
"Ai ba matsala duk daya ne".
Su Hanifa suka tafi state road, sukaci
abinci, sannan suka kwashi hira san ransu, har
dai bacci ya.dauke Hanifa.
Bayan ta tashi suka yi salla sannan ta yi
wanka ta shirya, suka kunna TV a falonsu
Salimat aka shiga kallo.
Haka dai suna zaune sai aka ce da
Salimat ta zo ga Zubairu ya zo. Zubairu yayan
Salimat ne, saboda shi dan 'yar babarta ne.
29.
Bayan ta je wajen Zubairu ta dawo ne sannan
take cewa da Hanifa
"Hanifa bakonki ne fa"cikin dariya ta fada,
Hanifa kuwa sai ta kalle ta kawa, a can cikin
kwayar idonta ta hango alamar tambaya.
"Wallahi tun ranar da kuka je asibiti da yaya ta
haihu to a ranar ne ya fara ganinki. Shikenan ya
nace min, kullum sai ya zo idan bai zo ba, zai
bugo waya. Kawai don ya tambaye ni ke. Shi
Wallahi yana sonki". Salimat ta dada kallonta
sannan ta kara da cewa;
"To shine ni kuwa na ce da shi ya zo
yau,zan gayyato ki,idan ya so sai ku hadu da shi
ku ga junanku.to ga shi yanzu ya zo".
Hanifa ta yi dariya ta ce"To banda abinki
ba sai ki gaya mini bа".
Hanifa ta tashi suka tafi falon da Zubair
yake itada Salimat. Suna shiga suka tarar da
Zubair a zaune a daya daga ciķin kujerun falon.
Falon dai kato ne dai-dai misali nan aka
shigo koridor ne a farko sai Sliding door a
tsakiyar koridor din. A koridor din akwai wani
teburi da aka saka flower mai kyau irin taroba
sannan ga madubi a rataye.
A kofar Sliding door din irin door mat ce a
shimfide. Kujeru ne set biyu a falon ko wanne da
teburi a tsakiya ko wanne teburi kuwa akwai
30.
flowera kai. Kalar kujerun duk blue ne haka zalika labulen d'a door mat din. A can wani dan stef an kawata shi da kujerun dining ga kuma dinning table din a tsakiya.
Akwai wani katon tangaran a tsakıyar dining table din saboda zuba fruit a ciki. (kamar lemo da
apples)
Akwai TV stand na silver afalon da TV da video
duk suma na silver a kan stand din.
Sai kanshi ne yake tashi a falon saboda
irin electric refiw " din da aka saka guda biyu a
falon. Ya kayatu.
Hanifa ta sami waje a falon ta zauna,
kujeru biyu ne a tsakanin su da Zubair. Bayan
sun dan gaisa da juna sai suka dan taba 'yar
hira a tsakanin su:
Ba su dade ba sai Zubair ya ce zai tafi
dama ba dadewa zai yi ba suka yi sallama ya
dauko bandir din N500 guda daya ya bata, ta
amsa ta ce ta gode. Ya tafi a motarsa.
Hanifa ta gaya wa Salimat yanda. suka yi
dashi. Ta kuma nuna mata kudin da ya bata.
Salimat ta yi matukar godiya sannan ta ce da
Hanifa to ya ya kika gani kina sonsa ne? kada ki
boye min komai Hanifa". Hanifa ta ce ina son shi
Salimat, meye abin ki a jikinsa". Salimat ta yi murmushi ta ce to sai a kular mana da shi Allah
ya hada kawunanku".
31.
Da daddare bayan sallar Isha'l sai
Salimat ta sa direban su ya måyar da Hanifa
gida, saboda ita ba ta son fita da mota da
daddare.
Bayan an ajiye Hanifa a gida sai ta shiga
ciki ta sanar wa da Sakina duk abin daya faru
tsakaninta da Zubair ta kuma bata kudin da ya
bata, dubu Hamsin ne.
Haka dai itama Sakina ta yi wa Hanifa
'yan tambayoyi a game da Zubair din, har daga
karshe ta gamsu ta kuma bata shawarwari.
Zubair da Hanifa soyayya ta kullu a
tsakaninsu. Sosai da sosai. Ko wannensu yana
nuna wa dan uwansa kauna tsantsa ko a gaban
waye.
Ranar juma'a da yamma sai Hanifa ta
shirya ta dauki mota ta tafi gidan su Halwa. Da
zuwanta gidan sai ta tarar da maman su Halwa,
bayan ta gaishe ta, sannan sai maman su Halwa
ta ce da Hanifa:
"Sannu da zuwa Hanifa; gashi kun daki
gurbi ba ta nan, yanzun nan na aki ta, gidan
kanwata a zoo road".
Hanifa tace da maman su Halwa
"Mama za su dade ne?"
32.
"Wallahi Hanifa ban sani ba ko za su dade. amma dai ba ta cika zama ba idan'ťa je.
Ko za ku jira ta ga mukullin dakinta nan" in ji
maman su Halwa.
Hanifa ta sha ruwan da aka kawo mata
sannan ta ce:
"Mama Wallahi sauri nake yi da na zauna
mun jirata, amma zan dawo
sai ta tambayi Aslam, sai maman su
Halwa ta ce da Abba ya nemo Aslam. Abba ya
je dakinsu da bakin gate ya duba Aslam, motar
Aslam din ma ba ta nan. Wannan ya tabbatar wa
da Abba cewar Aslam baya nan.
Abba ya koma ya ce da mama "Aslam din
ba ya nan".
Hanifa ta yi sallama da mutanen gidansu Halwa
ta dauki hanyar gida.
Umar Faruk wani yaro ne dan kwalisa,
gidansu a nan Badawa yake, wato makotansu
Sakina ne.
Umar mahaifinsa ya rasu, yanzu shi yake rike da
dukiyar su gaba daya kasancewar su biyu ne
mahaifiyarsu ta haifesu a gidan, da kanwarsa
Yahanasu.
33.
Kyakkyawa ne shi son kowa kin wanda bai samu
ba. Ya kasance yana kaunar Hanifa tun farkon
ranar daya fara dora idonsa a kan ta.
Sam Hanifa bata dauke shi da wani
muhimmanci ba, tana dai sonshi a ranta amma
ba irin son da take yi wa masoyanta ba. Babban
matsalar ta da shi bai wuce yawan 'yan matan
shi ba.
Umar yana da 'yammata a ko da yaushe kuma
suna biyo shi har gida nemansa.
Abdul ya zo wajen Hanifa ranar litinin, ya
kawo mata (cards) na (birthday) din shi. wanda
za'a yi (22 June) zai shiga shekarar Talatin.
Hanifa ta karba nata da na friends dinta
wadanda za ta rabawa.
Bayan sun yi hirarsu ta masoya sai Abdul ya yi
mata sallama ya tafi. Sun tsayar da shawarar
cewa idan ranar party din ta zo shine zai zo ya
daukę su.
Ranar da za'a yi party din Abdul, Hanifa tun da
safe ta tashi ta fara girke-girke duk da dai ta san
sun yi order din kayan party din a Daula Hotel.
Bayan sun kammala komai da komai ne sai
kuma ta shiga daki ta kwanta tun da sai yamma
za'a tafi.
Bayan an yi sallar la'asar ta tashi itama ta yi
sallar ta sannan ta shiga wanka. Da ta gama
34.
wanka bata saka kayan da za'a tafi party da su
ba sai ta dauko wata doguwar riga kawai ta saka.
Da ta fito falo ne sai Sakina ta ke ce mata:
"Yanzu Umar ya zo wajenki, amma na ce
agaya masa kina bacci don ban san kin tashi
ba
Hanifa tace:
"Ba rabon mu gana ne kawai".
Hanifa tadauki wayar falon ta fara lallatsa
nambobin, can aka dauka a daya bangaren
bayan sallama da 'yan gaishe-gaishe sai Hanifa
ta ce:
"Don Allah Halwa na nan?"
Aka ce da ita
"Halwa batanan Wallahi, yanzu ta leka makotanmu"
Hanifa ta ce da mai maganar:
"To Aslam fa? Kirawo shi don Allah sai na
bar masa sallahu in yaso idan ta dawo sai ya
gaya mata"
Aka amsa mata da. "To".
Bayan 'yan mintina ne sai Aslam ya dauki kan
waya bayan an isar masa da sakon.
Aslam ya fara da cewa:
"Hello!, Inagajiya? Don Allah wake
magana?".
Hanifa ta yi dariya ta се:
"Oh Aslam baka gane ni ba ne?
35.
Ya ce
"Eh wallahi ban gane mai maganaba".
Hanifa ta ce sake cewa:
"Lallai ma aslam. Okey tun da baka gane
ni ba sai anjima".
Aslam cıkin saurin bakı ya ce daita:
"Don Allah tsaya kada ki ajiye wa yar.
Don Allah ki gaya min wa ke maga".
Hanifa takara da cewa:
"Wallahi ba zan gaya maka ko waye ba
tunda dai har ka manta da murya ta, ka-ga ni
kuwa ko a barci na dauki wayar ka na san kai
ne. Sai dai ka canka da kanka".
(Hanifa ba ta san Slam, haka nan Aslam
bai san Hanifa ba. Sai dai dukansu kulum sauna
jin labarin juna a wajen Halwa.
Hanifa ba wai ta buga wayar nan ba wai don
Aslam ya santa ba, a'a ta ce a kirawo shi ne
kawai don ta tsokane shi. Kuma a can cikin
zuciyar Hanifa ba ta son ya san ko. wace ce ita
har su ajiye wayar).
Aslam ya cigaba da rokon mai magana a
kan a fada masa ko waye. Shi Wallahi bai gane
mai magana ba har yanzu, yana kuma 'yan fadar
sunayen iska kawai (wato sunayan mata kawai
36.
don dai ko zai dace ya canki sunan mai magana).
Hanifa kuwa sai dai ta ce: a'a, ba ita ba ce, ba
ka canka ba har yanzu. Ta riga ta san komai canke-canken da zai yi ba zai taba gane ta
ba,tun da bai santa ba. Amma dai duk da hakan
ta dage a kan lallai sai ya canka.
Amma ita ba za ta fada mishi ba.
Aslam ya numfasaya се:
"To shikenan yanzu dai a ina kike?"
"A gidanmu nake mana".
Aslam ya yi murmushi ya ce da ita:
"Ba wai haka nake nufi ba, a waссе
unguwar kike yanzu?".
Hanifa ta ce da shi
"Au ho, ina nan GRA ne"
sai ya yi sauri ya ce
"Gashinan na canka daman na ce Samira
ce kin ce ba ita ba ce".
Hanifa ta ce:
"Wallahi na gaya maka ba Samira ba ce,
Allah da gaske nake ba ita ba cе
Aslam ya се:
canka".
"To wacece nabaki gari, na ji na kasa
Hanifa ta ce tana murmushi
37.
"Bazan dai fada ba, wai kai wayo ba.
Kuma Wallahi na ce maka duk waďanda ka ba
da sunansu ba su ba ne".
Aslam ya ce da ita a cikin kosawa:
"To na yarda, amma don Allah ke da
waye yanzu a zaune a nan".
Ta amsa masa
"Ni da wata (Senior sister) yaya ta ce".
Ya ce da Hanifa:
"To Yaya sunan yayar ta ki".
Ta ce da shi
"Sunanta Sakina".
Sai ya ce da ita
"To don Allah bata mu gaisa da ita".
Hanifa ta nisa ta ce da Sakina ta zo ta karbi
waya za su gaisa da yayan Halwa.
Sakina ta karbi kan waya a hannun Hanifa,. suka
fara gaisawa da shi:
"Ina yini" ta ce "Lafiya lau" ya ce da
Sakina: "so, yaya kike,, ya gida?" tace da shi
"Lafiya lau muke ya ya mutan gidan?" ya ce
"Lafiyar mu kalau".
sai Sakina ta ce
"Ai Ina jinku kai da Hani.
kawai sai Hanifa ta katse layin da sauri ta ce da
Sakina:
38.
"Haba Aunty Sakina, kina in dai ban gaya masa ko wace ce ba tun dazu shine za ki bata mini shiri na"
Sanan ta ce da ita
"Allah shikenan kin fallasa ni".
Sakina ita duk bata gane komai ba sai da Hanifa
ta fayyace matakomai sannan ta ce:
"To ni ai ban sani ba, ni na dauka ai
kunsan juna, kawai dai wasa kuke, oho! Ni ban
gane ba yi hakuri".
Hanifa tana zaton bai ji an fadi sunanta ba, sai ta dada lallatsa nambobin, ringin daya sai
aka dauka a can bangaren aka fara da cewar:
"Oh Hanifa ya ya kika katse layin wayar
kuma?"
Hanifa ta dafe kanta da hannu daya sannan ta
ce "Ai ni ba sunana Hanifa ba, wayar da kanta ta
katse".
Aslam ya ce da Hanifa cikin numa jin dadi a
muryarsa:
"To yanzu dai don Allah Hanifa, zancen
wasa ya wuce, ai kin wahalar da ni sosai.kin san
Allah Hanifa tun lokacin da nake jin labarin ki a
wajen Halwa nake jin sonki da kaunar ki suna
shiga cikin jikina, da jinina da bargona duk wani
sako na jikina ya kwana ya tashi da begenki.
39.
Yanzu don Allah ya ya kike ganin za'a yı?
Wallahı da gaske na ke yi™
Hanifa ta amsa da:
"Ban gane ya ya nake ganin za a yı ba
Aslam ya ce da ita:
"To gaskiya ni dai ina sonki ina kuma
kaunarki, kuma don Allah ina son na ganki yau
ko gobe".
Hanifa ta ce da Aslam:
Gaskiya dai ni yanzu ba a gida nake ba,
ina nan Badawa gidan ya ya ta"
Aslam ya yi sauri ya се:
"To ai ba komai duk daya ne zan zo
anjima, yanzun nan zan zo na ganki"
Hanifa ta yi dariya ta ce:
"To sai na ganka ina jira".
Bayan sun yi sallama. suka yi ta dariya ita da
Sakina.
Hanifa ta tashi ta shiga daki saboda ta shirya
zuwan wajen party.
Hanifa ta dauko wani cordless baki an yi mata
riga da skirt irin mai shape ya dameta, dinkin ma
40.
ya yi masifar yı mata kyau. Daman gata fara a
saifatar nan tata ta dada fito da ita Akwai fele mai yallo da ratsin bakın bakı a jiki Ta dauko bakin takalmi da jakarsa ta saka Felen ta daura daya a kan ta dayan kuma zai zauna a matsayin mayafi ne. fuskarta babu komai idan ka dauke dan mai da ta goga a
lebenta sai kwalli da ta goga a saman idonta. maimakon sakawa a cikin idon. Idan ka hango Hanifa ba abin da zai hana ka yi tsammanin ba Amarya ba ce wacce za'a kai dakin mijinta masoyinta.
Hanifa ta shirya tsab sannan ta kawo
turaren channel tafesa ajikin ta bayan ta yi amfani da hugo woman deodorant ta fito fes, sai
kamshi ke tashi ta ko ina a jikinta.
Suka zuna jiran su Abdul, shiru-shiru bа
su zo ba ga shi har shida saura kwata, sai ta dauki mota suka tafi gidansu Fa'iza don su taho
tare. Suka je aka dauko su har da su Rahma da Hafsat.
Maimakon su dawo gida kawai sai suka yanke shawarar su tafi wajen da a ka rubuta
za'a yi party din.
Da zuwansu sai suka tarar babu kowa suka
tambayi masu gadin wajen,sai aka sanar dasu ba'a nan bane.
41.
Hanifa ta yi bakin ciki ba karami ba kuwa,
dadin dadawä ga kawayen ta da ta gayyata ba
za su ji dadi ba.
Haka dai su Hanifa suka ware redion cikin motar
su suna shan kida. Suka koma badawa tare da
kawayenta, suna zuwa aka ce da su yanzu aka
zo neman Hanifa, amma ance basa nan sun tafi.
Hanifa ta rasa ko waye ya zo wajenta.
Ta tambayi Sakina ko ta san wanda ya zo
nemanta sai ta ce da ita ai Zubair ne, kuma ya
ce gobe zai tafi Sokoto kuma sai ranar Monday
zai dawo
Hanifa bata so ba sam, saboda su ranar Sunday
zasu koma school. Shi kuma gashi sai ranar
Monday zai dawo, yanzu shikenan ba za su
hadu ba.
Anan ne fa su Hanifa suka kunna radio a
falon Sakina suka yi ta tikar rawa ita da
kawayenta.
Sannan suka dan ci Snacks din da lemo.
Da magariba sai ga Umar ya shigo
1
alokacin su, suna sallah. Bayan sun gaisa da
Sakina da su Hanifa aka dan yi hira sai kuma ya
fita waje.
Da fitarsa sai Sakina ta ce da su Hanifa to
ko za su je fatin bikin nan ne da aka kawo daga
gidan su Ahmed (mijinta).
42.
In yaso Umar ya kai su. Hakan kuwa aka yı. suka shirya suka fito 'tare da kawayen Hanifa Fa'iza da Hafsat dai gida za'a ajıiye su.
Bayan sun fitane sai mai gadin nasu ya ke cewa da Hanifa gaba ko yana nemanta
Hanifa ta ce wa da Umar don Allah ya tsaya taje ta ga ko suwaye. Bayan ta fita daga
motar tana zuwa da ganin su ta tabbatarwa da kanta cewar su Aslam ne.
Aslam kyakkyawa ne sai ka ce balarabe
ga gashinsa mai sulbi ne irin na indiyawa. Ya
hadu karshe. Don ina kyautata zaton ko su
indiyawan ne suka ganshi sun san ya hadu
ballantana mu. Aslam ya zo ne tare da wani
abokinsa. Kuma amininsa Sani.
Duk da Hanifa ba ta san Aslam ba, ko hotonsa
bata taba gani ba, amma ta tabbatarwa da kanta
wannan (handsome) din Aslam ne.
Suka kalli junansu na dan lokaci sannan sai
Hanifa ta yi murmushi ta kawar da kanta.
Aslam ma ya yi murmushi mai kayatar wa
sannan ya fara da gaishe ta. Ya kuma gabatar
mata da Sani a matsayin babban Amininsa
Aslam yakuma gabatar da Hanifa a wajen Sani.
A nan ne Hanifa suka kara gaisawa da Sani,
sanan ta sanar musu da cewar zą su je unguwa
43.
ne ita da yayarta da kawayenta. Sai yaushe
kènan za ku dawo.
Aslam ya ceda Hanifa
"To Gimbiyata, daman muma sauri muke
yi amma za mu dawo a satin nan in sha Allah".
Bayan sun yi sallama dasu Aslam sai
Hanifa ta dawo mota ta shiga Umar ya ja suka
tafi.
Hankalin Umar ya tashi ganin su Aslam
sun zo ganin Hanifa ya kuma lura da yanda
Aslam yake nunawa Hanifa kauna a fili.
Bayan ya hau titi, ne sai ya dan dubi
Hanifa ya dan harare ta ya cigaba da tukinsa.
Da suka isa wajen da ake yin party din ma arufe
yake suka sauke su Fa'iza a gida sai suka taho
gida suma suka je aka sauke Sakina agidan
surukan nata. Hanifa ta bude mota kenan za ta
fita sai Umar ya ce da ita:
"Hanifa ina son .don Allah ki rakani
unguwa, yanzu za mu dawo"
Hanifa ba ta yi magana ba sai dai kawai ta dawo
ta zauna ta rufe kofar motar. Suka harba kan titi
suna tafe Umar yana janta da hira tana amsa
masa sama-sama domin Hanifa ita duk haushi
ya cika mata ciki fal, ranta ya gama baci.
44.
ce da ita
Umar ya kıra sunanta ta amsa masa ya
Hanifa
"Wannan wanene ya zo wajenki dazu? ta се
"Wan wata kawata ne Ya ce da ita
"Wan kawarki. amma me ya kawo shi wajenki?".
Hanifa ranta ya baci ta ce da shi "To ubana son junanmu muke yi shi yasa ya zo wajena ko da magana".
Daga jin maganar da take yi masa ya san ranta
a bace yake kawai sai ya ja bakinsa ya tsuke.
Suka je gidan abokinsa basu same shi ba, daga
nan suka koma ya kaita Badawa.
Ta shiga ta fara kuka a kan gadonta
Bakin cikin Hanifa daya, duk abin da ta
shirya yau baya yiwuwa.
Sun fita Zubair ya zo basu hadu ba, sun je
wajen fatin Abdul ba kowa. Sun dawo gida
Aslam ya zo ta sallame shi saboda wani
fatin.
Sun je wajen nan ma akulle.
Abdul ya jirga su har yanzu bai zo ba. Ga kayan
fati a jibge a gida.
Ga kunya da taji ta kawayenta ga Umar yana
mata wasu tambayoyi marasa kan gado.
45.
Sun je gidan abokin Umar din nan ma basu
same shi ba
Tana ganin idan ba kukan ta yi ba zuciyar
ta ba za ta yi sanyi ba.
46.
WATAN RAMADAN
Muna murnar watan Ramadan.
sati Hudu na barakah, kwana talatin na yafewa,
720 hrs. na tsarkakewa, 43,200mins na kivayewa, 2,592,000sec na haske.
Ramadan kareem !!!!
Asharuwa lafiya
Siyama Ado Bayero
47.
@Friends Compputer
K/Nassarawa Kano
Tel 064-331074
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su