An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
HAUSAВООК.COM
BILKISU
HNI 1
ADO BAYERO
HANIFA
BILKISU ADOO
BAYERO
Harafi Publlshers KaAure Ni
BILKISUHAMUHD
BABI NA DAYA
"Allah sarki Aslam koyanzu yana ina?
Allah shi ya bar wa kansa sani"
Hanifa ce take zancen zuci. Tana zaune a
kan dan gadon su na bacci na karfe, amma
maimakon gado mai hawa biyu, kamar yadda na
kowacce makarantar kwana yake kasancewa.
Wannan nasu mai gudadaya ne.
Gadajen guda biyar ne a jere, ko wanne
da dan karamin lokarsa a jikin bango kusa da
gadon. Dakin babba ne, ba wai can can ba. Idan
mutum ya shigo {Orange house} sunan gidan
nasu kenan a makarantar, a kwai dakuna guda
goma a jere {room 1- 10} ko wacce da kofar
shigarsa. Idan ka shiga akwai {wardrobe} ta
ajiye kaya ta raba dakin gida biyu,ya zama
kowanne dakin akwai {part 1& 2}. ko wanne
{part} akwai gadaje biyar-biyar.
Makarantar su Hanifa sananniya ce a.
birnin Dabo, Kano Model Private Secondary
School, kenan. Amma kawai mutane suna
kıranta da Kano MODEL. Makaranta ce ta gani
ta fada domin ta masu da shi ce {Masu kudi),
akwai karatu sosai a makarantar, da kwararrun
malamai. Malaman makaratar sun hada yare da
yawa a kwai farar fata, akwai Hausawa da
Yarbawa kowa da irin fanni da yake karantar wa.
3.
Idan aka shiga makarantar daga gåte na
biyu sai wajen {Parking} ajiye motoci na
malamai, daga bangaren hagu ofishin shugaban
makaranta ne a kusa da shi na Vice dinsa ne.
sai ofishin guardian & council, daga daya
bangaren ofishin malamai ne da kuma store din
makaranta a wajen.
Bangaren dama kuwa wani katon filine na
gaske wanda kana iya hango coach din wasanni.
da kuma wajen basket ball.
Akwai 'yar tazara kadan zuwa ajin dalibai. Daga
an wuce na 'yan aji daya sai na 'yan aji uku. Ko
wanne aji akai azuzuwa uku wato (ABC) (3A
BC). Dayan sashin kuwa ajin 'yan aji biyu ne da
'yan aji hudu sai sashen karshe 'yan aji biyar da
'yan aji shida amma akwai Library a tsakanin su.
Akwai laboratories a dan bayankadan da
azuzuwan dalibai.
Masallacin makarantar ya na gefen
yamma akwai tafiya daga (classes). Masallacin
kato ne sosai har da library aciki,an tanadi
kur'anai da hadisai da dai sauran litattafan addini
Daga wajen masallacin sai an yi tafiyar a kalla
minti biyar sai ka bullo ga Dining hall dinsu inda
a nan ne suke cin abinci da gabatar da tarurruka
idan za'a yi wani wani wasa ko wa'azi.
4.
Daga bayan dinıng din kitchen ne in da masu
aikin abincin suke sannan da wanı dakı
dabandaki saboda amfani (Kitcheners) din.
dalıbai.
Daga dining hall ana hango hostels din
A kwai houses da aka rarraba kowanne
dalibi akwai dakinsa da bandakunansu a gaban
ko a bayan dakunan.
Hostels din guda shida ne kowanne guda
uku suna kallon junansu.
Akwai pink house da yellow house da orange
house ko wanne yana da A da B (Pink A da pink
B) (yellow A da yellow B) (orange A da orage B).
Hanifa tana orange B. shine na seniors
orange A kumana Juniors. Hanifa ajinta biyar,
tana karantar Account wato ajin 5A amma SS2A
shine abin da ake amfani da shi a yanzu.
Suna term dinsu na biyua SS2 saboda
haka, sun yi matukar ba da himma ne kawai a
karatunsu basa wasa sam. Daman ba irin
makarantun da dalibi zai tsaya wasa ba ne, don
idan yaro ya ce wasa zai yi sai ya dau na
karshe don makaranta ce da kowanne dalibi
yace idon ba ka yi ba ni waje, kowa kokari yake
ya wucedan uwansa. Saboda haka babu wanda
zai yarda daga kallon ruwa kwado ya yi wa
mutum kafa.
Hanifa ta fitone daga tsatson wani
hamshakin mai arziki ne, wanda ya yake da
5.
mutumci da sanin ya kamata mai suna Alhaji
Aminu Abubakar
Alhaji Aminu yana zaune ne a cikin garin
kano, a unguwar Babura road. Yana da mata
biyu da 'ya'yansu.
Hajiya amina da Hajiya Salamatu
Hajiya Amina itace uwargidan Alh. Aminu
auren saurayi da budurwa suka yi. mata ce mai
hakuri da juriya ba ta da yawan magana samsam. Kyakkyawa ce ta fita cikin taro, kallo daya
mutum zai yi mata ya tabbatar wa da kansa, an
yi rububinta da tana 'yan matancinta.
Tana da 'ya'ya biyar biyu maza uku mata. Salisu
shi ne na fari; sai Sadiq wato Abubakar sunan
kakansu uban Alh. Aminun, sai Hamida da kuma
Sakina, sai 'yar autarsu Hanifa.
Hajiya Salamatu, Amaryar Haj. Amina
Kamilalliyar mace ce, mai ilimi da kuma kunya.
Tana da 'ya'ya uku, Abdulra'uf sai Salim da
kuma autar gidan gaba daya wato Fatima Binta.
Alhaji Aminu haifaffen garin kano ne,
baban su Alh. Abubakar shi ne limamin unguwar
sharada, yana zaune da matarsa Hajiya Zainab,
ita ce mahaifiyar su Alh. Aminu.
Alh. Aminu sun kasance su biyar ne a wajen
iyayensu, Alh. Aminu shi ne babban sai Alh.
6.
Sani yana binsa, sai Haj. Hafsatu ta ukun su da
Alh. Kabir da kuma autarsu Ummul kursum.
Alh. Aminu babban dan kasuwa ne yana
zuwa irin su Dubai, China, da su Morocco yana
shigo da kayayyakin amfani na gida, kitchen da
kuma office. haka zalika yana shigo da sarkoki
da agoguna irin fashion da kuma gold.
Alh. Sani yana aiki a First Bank of Nigaria
Manager ne shi a wajen.
Haj.Hafsatu ta yi aure amma tana aikin jinya a
asibitin Nassarawa dakin 'yan haihuwa.
Alh. Kabiru Custom ne shi Portharcourt yake aiki
da matrsa Haj. Asabe.
Auta kuwa Ummul Kulthum tana matakin
karshe a jami'a, tana karanta political science.
Salisu shine babba a gidan su Hanifa
yana zaune a Tarauni Quarters da matarsa
Hajara da dansu Amir. Sadiq yana zaune a
unguwar 'yan bulo da matarsa Ikram da
'ya'yansu guda biyu (twins) Hassan da Hussein.
Duk kansu harkar kasuwancin ubansu suka bi
hanya. Sai Hamida yanzu haka tana da 'ya'ya
uku, Hasiya, Kabir, sai A'isha suna zaune a
Zaria da mijinta Ahmad likita ne a Teaching
hospital.
Abdulra'uf yana zaune a Bauchi da matarsa
Rahma da 'ya'yansu uku Pamela, Saddiqa da
Yusra, yana aiki a Bank of the north reshen su
na Bauchi state.
7.
Sakina tana aure a Badawa GRA da danta
Naifal, mijinta yaha aiki a Total gidan mai,
sunansa Aliyu.
Yanzu gida sai Hanifa da Salim da
Zahra'u su ya rage, suna karatu Salim shekarar
sa Ashirin da daya Hanifa kuma shekararta
goma sha shida, sai Zahra tana da shekarar
tara.
Alhaji Aminu mutum ne mai son sakewa
tare da iyalansa, ko da yaushe suna tare, koda
office ya je yana Allah-Allah yamma ta yi ya
dawo, domin ya kasance tare da iyalinsa, domin
suna matukar kyautata mashi da kuma ririta shi,
suna kwantar masa da hankali. Haj. Aisha da
Haj. Salamatu sun hade kansu sun zama
tsintsiya madaurinsu daya, babu abin da suke
boye wa junansu, kullum kansu kara haduwa
yake yi. indai ba 'yan uwa na jiki ba ba'a
tantance 'ya'yan wannan da 'ya'yan waccen,
domin 'ya'yan suma kansu a hade yake.
A takaice dai ga bakin mutane, idan dai
ba'a gaya maka ba sai dai ka kira su a Ya da
kanwa ba dai kishiyoyi ba.
Ba irin kishin wannan zamanin ba da za'a
zauna kamar jahilai. Daga kishiya har 'ya'yanta
su sa amarya a gaba kamar dabbobi, wai su ana
kishin amarya ta zo.
Idan dai ba Jahilci ba ina ruwan 'ya'ya a taya
uwa kishin, ai ko a nan an yi asarar kudin tara da
kudin laraba. Kishin dabbanci kuwa don bakin
8.
hali har yaran ma sai a hana su gai da matar
ubansu, ni a ganina ai ba wáńi suke yi wa ba sai
uban nasu, shi mahaifin nasu, ai shi ya kawo
Amarya to ina laifin amarya, kuma rabon auren
ina za'a kai shi? Ga na 'ya'ya?
Ni ina ganin da uban nasu yaje neman mata, har
bacın rana a kai ga haifo la'anannu, ai a yi auren
yafi. Wannan kuskure ne babba mu ce za mu yi
kishin dabbobi idan mun hana 'ya'yan zuwa ga
matan ubansu za mu hana su matan uban nasu
haihuwa ne? kuma ma dai 'ya'ya ai na kowa ne
da wanda ya haifa da wanda bai haifa ba, duk
dai ubangiji muke bautawa. shi ne kuma ya
bamu 'ya'yan to takamar ta menene? Idan kai ka
haifesu to kai ne ka halicce su?
Hanifa tana makaranta a kano Model,
yayin da salim ya shiga Jami'a a Uni maid
(university of Maiduguri). Zahra kuwa tana Excel
primary, class 5.
HANIFA AMIN, yarinya ce kyakkyawa,
son kowa kin wanda bai samu ba Hanifa Allah
ya yi mata kirar jiki mai kyau ita ba doguwa ba
can haka nan ta zarce matakin gajeru. Fara ce
tas da ita, ga hancin dogo har baka, bakinta dan
dai-dai fuskarta. Gashin kanta ba shi da yawa
sosai amma duk da haka idan ta sake shi yana
kwantawa a kafadarta. Kyan Hanifa sai wanda
ya gani. Ga ta da son addininta don ta sauke
9.
alkur anı da litattafai da dama tun tana (JSS
class): Hanifa ba ta da makusa a jikinta dá
halinta sai dan abin da ba za'a rasa ba, don
mutum tara yake bai cika gomaba.
Kawayenta a makaranta sarauniyar kyau
suke ce mata. Tana da kawaye a makaranta da
dama don ba ta da abokin fada, idan har ka kaita
makura ta gwammace ta gayawa babba ya yi
maka magana a kan ta tanka maka.
Hanifa tana da farin jini a wajen samari da
duk wani cikakken namijin da ya hada ido da ita.
Har ta kai yanzu a garin kano duk wani saurayi
da ya san ya hadu, ya kwana ya tashi da sanin
Hanifa Amin. wala'Allah yana takama shi wani
ne, ko kuwa babansa wani ne, ko mamansa
wata ce, da wanda ba kowan kowa ba ma, ina
tabbatar wa da mai karatu yana daya daga cikin
masoyan Hanifa ko a boye ko a bayyane.
Hanifa tana da wani hali wanda duk
wanda ya santa to ya santa da shi. Wannan hali
kuwa shine, duk wanda ya tako kafarsa ya zo
gidansu ko makarantasu, ko ya aiko ko ya
rubuto yana sonta, to bata taba wulakanta
mutum. Da yawan kawayenta a makaranta suna
ce mata wai zara ne da ita, wasu kuma su cе
mata ya ya za'a yi duk kyan nan nata ta tsaya
tana kula tsamaye da 'yan karya? Wasu kuwa
cewa suke yi da su ne da matsayinta, kyanta da
kudinta wallahi ko dan waye a garinnan sai sun
10.
ga dama su saurareshi, kuma ko da ace ya
samu zasu dan' kula shi to sai sun ja masa rai,
sun kuma ja masa aji, sannan ya kaskantar da
kansa a wajensu, ita kuwa duk wanda ya tare
sai ta yi murmushi ta ce "to ai ku kenan, ni kuma
ni ce!" iyakar amsar ta da su kenan.
Hanifa ta yi makarantar ta ta prinary a
Bennie nursery & primary school. Yarinya ce mai
kokari sosai, har yanzu da ta shiga SS 2 ba ta
taba daukar na uku ba daga ta daya sai ta biyu.
Idan ta yi na biyu ma sai ta shafe term guda tana
kukan bakin ciki wani term din kuwa sai ta dau
kofi don tsananin dagewa.
Saboda kokarinta kowa yake yaba mata, ko da
yaushe iyayenta suna cikin shi mata albarka.
Tun daga aji biyu na karamar Secondary Jss 2
Hanifa samari suka yi mata caa aka, kowa ya zo
idan ba ita ba sai dai rijiya amma idan an rabu:
ba wanda yake kara tuna guga ma ballantana a
tafi ga batun fadawa rijiya.
Duk da samarinta amma ba ta yadda da
zancen soyayya ita dai karatu shi ne a gabanta.
A lokacin da ta shiga SS 1 ta yi wani saurayi
Anwar, ya zo da kokon bararsa gabanta, Allah
da ikonsa sai tashi daya ta ji tana son sa, amma
sam karatunta ne a gabanta sai dai a bayan
fage to ya samu dan wajen rakabewa
zuciyarta.
a
11.
Allah ya dorawa Hanifa wani hali a cikin
ranta bangaren soyayyarta da ma' śsoyanta. Nan
da nan idan kun hadu kana sonta za ta ji ka
shiga ranta haka nan idan ta samu wani za ta
canza ra'ayi daga kanka. Amma da wuya
masoyinta ya gane hakan don ba za ka taba
ganin canji ba a wajenta, don tana ganin idan dai
ta yi hakan, mutane za su ce ta zama maci
amana, hakan kuma ko kadan ba yin kanta bane
halinta ne. (Ba kuma Hanifa kadai ba,
'yammatan yanzu matsalar tana addabar su,
yarinya tana ganin ko wacce rana tana da sabon
saurayi (new catch) to akwai rana zata zo, zaku
daina jin son ko wanne saurayi a kowanne wata
(new catch). Ranar za ta zo da son nan zai tsaya
a ranku na sati, zuwa wata, daga nan sai ya
zarce har shekara, har kuma karshen rayuwa.
Lokacin da wannan son ya tabbata to an samu
abokin rayuwa, tabbas wanda son nasa ya
kamaka shi ne abokin rayuwarka wanda za ka
so kasancewa gaba dayan rayuwarka. Kada
matasa ku dauka .shi ga cikin soyayya, daya
yakeda kasancewa a. soyayya.abin dubawa da
tunani a nan shine yaron ko yarinyar da aka
hadu wancan satin, shine?ko itace? Zai iya
kasancewa, idan kukashiga cikin soyayya
sannan kaunar junanku ta zama kun kasance a
cikin soyayyar. Kuma ina tabbatarwa da mai
karatu don mutum ya ce "Ina son ki/ka" yana da
masifar sauki a baki, amma kalmar "Nima ina
12.
son ki/ka" yana kasancewa tabbas ka sami
masoyin kwarai)
Hanifa da farko ba ta farga ba sai da 'yan
group din ta suka dameta da suka da nasiha
Duk da haka Hanifa gani take kamar dai kawa
ra'ayinsu kawai suke fada, sai a hankali da ta
kuma girma ta kara hankali yanzu kuma take
fahimtar gaskiyarsu.
Hanifa koda yaushe rokon Allah ta ke yi
don ya fito mata da masoyinta na gaskiya don
tasoshi har karshen rayuwarta. Ta kuma kara da
rokon Allah, Allah ya yaye mata wannan hali don
ba ta son abin da za'a sako wulakanci a
harkarta. Ba ta son ta yi wulakanci, kamar yadda
taki jinin wani ya yi mata wulakanci.
ANWAR yana kaunar Hanifa sosai a
ransa, duk bayan ko wanne minti sai son ta ya
dada shiga cikin ransa don super market
babanshi ya bude mashi a beinnit "ANWAR
SHOPPING CENTER" aka zuba masa kaya duk
ribar a account dinsa take zarcewa. 'Yanmata da
yawa sun mato a kan sonsa amma sam ba sa
gabansa sai dai Hanifa.
Lokaci guda sai Hanifa ta canza son
Anwar ya fita daga kanta, sai dai hakurin
kasancewa, har dai Anwar ya fahimta. To da
yake yaro ne mai ilimin zaman duniya sai ya
hakura, ya kama gaban shi. Ba wai don ya daina
13.
sonta ba sai dai kawai turbar lafiya a bita da
shekara. Ba kamar måzan yanzu ba da sai dai a
bude sabon babin naci, kamar kutare.
Bayan Anwar ya kama gaban shi, sa
Allah da ikonsa ya hada Hanifa da wani tsalelen
saurayi dan kwalisa, mai ji da kansa. Suhal
shima ya fada cikin so da kaunar Hanifa kamar
zai ci babu. Hanifa dai karatun ta ne kawai ranta
sai dai dan abin da ba'a rasa ba da ya zama
dole tun da samari ba'a sati biyu sai an zo
makaranta, ranar visiting day kuwa har buya
take a bayan Library ko kuma ta tafi masallaci
sai dai idan an tsananta bincike a gano ta.
Da farko Hanifa ta nuna wa Suhal itama
tana kaunar shi, amma da suka fara soyayya,
sai ta ce wai ya takura mata a harkar makaranta,
saboda haka sai ta daina sonsa. Ubangiji da ya
sa mata sonsa haka kuma soyayyar ta zo
karshe, kamar yadda ta kasance da Anwar
shima hakan ta faru gareshi, sai kawai ya tattara
tsumman rayuwarshi yakama gabansa.
Hanifa abin duniya ya dameta don
hankalinta ya yi masifar tashi, ganin yanda cikin
lokaci soyayyarta take watsewa. Ita dai a kan
kanta da zuciyar ta yanzu duk kansu ba su
gabanta, sai dai wani zazzafan tausayinsu da
yake damunta.
Abin da yafi damunta da wannan halin
nata kuma yake kara sa ta a halin damuwa bai
14.
wuce tantamar ta a kan wai shin haka rayuwarta
za ta cigaba yau ga wannan gobe ga wancan ga shi lokaci yana tafiya tabbas nan da shekara daya za ta gama makaranta, ta san kuma tabbas daga gama karatu sai aure. Don a
danginsu mace ba ta cigaba da karatu sai dai a
gidan MIJINTA.
BABI NA BIYU
Hanifa suna makaranta a zaune a bayan
library ranar asabar, ana ta hira da kawayenta,
'yan set dinsu ne, Hafsat ce ta fara katse Umma
Amin wadda ke. ta zuba kamar kanya, tana
labarin wata fitinanniyar yarinya new comer da
cewar:
"Wallahi tunanin Auwal nake tun dazu ni sai
wani jin haushin zaman makarantar nan nake yi,
makarantar da zaka gama, a yi maka aure". Ta
dan yi ajiyar zuciya a hankali. Za ta kara
magana ne sai Halwa ta katse ta "Wallahi Hafsat
daniceke Allah babu abin da zai dame ni, ina da
15.
miji a hannu, ai niko yanzu na samu mai aure
na, wallahi 'na bar makaranta...." Gaba dayansu
suka kwashe da dariya
Umma ta ce "Allah Hafsat Auwal din ki,
wani bagidaje ne shi....
Caraf Hafsat ta katseta da cewa:
"Lallaikam na gode, Amma dai duk
haduwar Hamisun ki ai bai kai haduwar Inuwan
Rahma ba".
Rahma ta budebaki za ta yi magana sai
Halwa tariga ta, a can cikin muryar ta zaki ji
alamar dariya ta ce:
"Gaskiya an zagi Rahma, don Wallahi duk
cikin su Auwal da Hamisu da Inuwa, ba wanda
ya kai haduwar Abdul din Hanifa"
Ai kuwa sai Hanifa ta daka mata duka
tana dariya ta ce:
ne?"
"Kin ji na saka muku baki a maganar ku
zancen yaushe kuma gashi nan kin shigo
layin". Sai suka kwashe da dariya.
Hanifa ta kalle su a lokaci daya kuma ta
waiwaya ta kalli filin wasan makarantar tasu, ta
kuma kara da cewa:
"An gama (games) fa, ina ganin mu tashi
mu tafi dining hall".
Hadiza Aliyu ta ce:
"Wallahi ni dama yunwa nakeji Allah yasa a kada
(bell) dinner yansu"
suka dada kwashewa da dariya a tare.
16.
Kai Hadiza ciki a ka kawo duniya "In ji
Halwa "Ko don ba'a ambaci Mansur dinki ba, shi
yasa kike son a tashi?".
Hadiza ta kalleta tace:
"Shiyasa nagake anfadi Sanin ki ko?"
Suka karasa dining hall har 'yan Juniors
sun bi layin "Zokar" (abincinda suke gayawa
haka, wake da shinkafa).
Bayan sun yi Magrib da Isha a masallaci
anayi musu wa'azi harzuwa 9:00 na dare, Imam
din masallaci. Amma yawancin wasu daliban ba
sa tsayawa, saboda ranar lahadi da safe ma
anayin M.S.S. safe zuwa azahar.
Su Hanifa suna zaune da yamma ranar
Juma'a a hostel dinsu sai ga Sa'a Gambo. Sa'a
ta cewa Hanifa:
"Wallahi Hanifa ba ki kyauta mini ba, ace
zuwa na gidan ku uku, amma ke ko tambaya ta
hanyar gidanmu ba ki taba yi ba. Kin kyauta
kenan?",
Hanifa kunya tai bala'in kamata don Sa'a
Gambo kam ta nuna mata halacci, sannan sai ta
dago kanta a hankali ta ce:
"Don Allah Sa'a ki yi min Afuwa Wallahi
ina son nazo, kawai dai Allah ne bai nufa, don
17.
Wallahi nima wanı lokacin har kunyar ki nake ji.
'Don Allah ki yi hakurı wallahi zan zo".
Sa'a Gambo class captain din suce.
Kuma room mate dinta ce.
Halwa tayi caraf ta cе:
"Lallai Sa'aye, ai in dai Hanifa ce kya gaji
da jirgi irin nata. Ni kaina sai na kirga miki
zuwanta gidanmu. Ba tasan mutane sam!".
Hanifa ta ce:
"Halwa banda kari, ke da ya kamata ki
tayani ba ta hakuri kya batani a wajenta?"
Halwa ta ce:
"to tsaya Hanifa karya zan miki?"
Hanifa ta ce:
"Ba wai batun karya, amma kin san ba'a
barin mu fita ne shi yasa".
Sa'a Gambo ta ce: "to mu din barin mu
ake yi, ko mu ba 'ya'ya ba ne? amma sada
zumunci ai ba'a hana zuwa".
Hanifa ta ce da Sa'a tare da nuna
tsananin damuwa a fuskarta:
"Don Allah Sa'a kyale Halwa hada mu
kawai take son ta yi, na ce miki zan zo in sha
Allah, zan bawa Halwa mamaki, don yini zan yi
miki".
Halwa ta tuntsire da dariya ba
kakkautawa, ta ce da Sa'a:
18.
"To Sa'a, ba girin-girin ba dai tayi mai Allah ya tabbatar"
Hanifata gama kulewa da Halwa sosai,
Sa'a na fita, ta hauta da duka. Kamar ta Sani sai
ta fada karkashin gado, tana dariya.
"Allah ya isa Halwa" in ji Hanifa. Suka
cigaba da shrin kwanciya saboda an kada (bell)
light out.
Halwa Nafi'u Ringim, Kawar Hanifa ce tun
suna JSS 2 a lokacin aka kawo Halwa daga
oxford school, Lodon a can ta yi Nursery dinta
da primary, za su tafi JSS 2 ne sai suka tarkato
daga London suka dawo Nigeria shine Daddyn
su ya samar mata Kano Model.
Halwa 'yar wani Babban likita ce, da ya
kware a fannin aikinsa. Bai cika zama a Nigeria
ba, koda yaushe sai an aiko mishi da transfer
daga wannan. Kasa zuwa wata, ko wanne lokaci
idan yatafi ya kan yi shekara daya zuwa biyu a
duk garin da aka turashi.
Alh. Nafi'u mahaifin Halwa yana da mata
guda biyu, Haj. Ladi da Haj. Hadiza suna zaune
matan fada road, a Kano. Sai dai sukan ziyarci
Ringim wajen dangin mahaifinsu.
a
Haj. Ladi uwargida ita ce matar Alh, Nafi'u
ta biyu, kasancewar matarsa ta farko, ta zo
haihuwa Allah Ya karbi ranta. Tana da 'ya'ya
19.
uku Aslam. Ilham, da Abba. Aslam shine babban
yana da shekara Ashirın dà biyu. Ilham tana da
shekara ashirin, ta yi aure bayan ta gama
makarantar st. Louis Secondary da yake ita ta
zauna ne a wajen yar babarta a katsina road,
tana aure a lodge road No. 12. Abba kuwa
shekararsa goma sha biyar.
Haj Hadiza Amarya ita ce maman Halwa,
tana da ya'ya hudu duk mata. Halwa, A'isha,
Rahma, da Maryam.
Alh. Nafi'u yana da son 'ya'ya, sosai.
Amma duk da hakan ya fi damuwa da Aslam
yana sonsa sosai da sosai. Kowa kuma a
gidansu Halwa yana kaunar 'ya Aslam" haka
suke ce masa. Duk da kawancen Hanifa da
Halwa ba ajinsu daya ba, domin ita Halwa
commerce take karanta. Amma ko da yaushe
suna tare da junansu, wasu a makaranta har
(twin sisters) suke ce da su.
Ranar da su Hanifa suka samu hutun
good Friday, Ester Monday sun yi mutukar farin
ciki domin duk kwana hudun ya zamar musu
kamar visiting day. Ko wacce rana sai an zo
musu, azo daga gida sannan da yamma samari
su zo.
Bayan zun idar da sallar Isha'l ne suka
zauna suna addua'r samun saukin karatu da
20.
kuma neman sa'ar Jarrabawar da aka kafe
musu time table, za su fara sati daya!
Wannan hutun ne su Hanifa za'a shiga form Six
(SS-3)
Bayan sun fito suna tafiya ne Halwa ta
fara ba da labarin 'yan gidansu (as usual) Hanifa
har ta haddace farkon zancen Halwa in dai hirar
gida za a yi.
"Allah sarki ya Aslam, ko yana tuna wa
dani kuwa, 'yan Paris sun dauke min yaya". Shi
ne abin da Hala ta ke fara fada a duk lokacin
daza'afara hirar gida.
Hanifa ta ce da Halwa
"Kai ni dai gaskiya Halwa na gaji da wannan
zancen Aslam - Aslam, wai shi kadai ne a gidan
ku ne? kullum ba ki da wata hira sai ta Aslam! Ni
Wallahi har so nake na ga yayan nan naki".
Halwa tayi shiru tana kallon Hanifa, а
hankali. Hanifa ta cigaba da cewa
"Kuma na san bani kadai ba ma duk
wanda yakejin hirar Aslam a wajenki, yana
muradin ya ganshi, saboda kullum zancen sa
ake yi".
Halwa ta yi murmushi sannan ta ce;
"Ke kuwa Hanifa idan ban yi hirar Ya
Aslam, to hirar wa zan yi? wallahi don ba ki ga
yanda na matsu a yi mana hutu naje na ganshi
21.
ya ganni don na san yanzu shima yana ta tunani
na ya damu ya' ġanni.
Hanifa ta yi wata isashshiyar dariya,
sannan ta ce da Halwa:
"Kin ji ki da wata irin magana wai yana
tunaninki ya damu da ya ganki sai kace wata
matarshi".
Caraf Halwa ta karba ta ce:
"Ai wallahi bari ná gaya miki ni nasan nafi
matar ya Aslam, don na san da su Mama za su
barni, ba abin da zai hana, idan ya Aslam ya yi
aure mu tafi tare ba, don ba zai iya zama babu ni
ba, kin gakuwa ai kinsan nafi matar sa matsayi.
Don wallahi wata