ginin cewa Shuraiba ta ƙwato
masu 'yanci a hannun miyagun dakarun.
Wannan shi ne abin da ya faru da yarinya shuraiba.
BABI NA SHA UKU
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
89
Al'amrin matsafi Shamrul kuwa lokacin da ya rabu da yaro
Imran bayan ya kunyata ta shi a gaban mabiya addininshi.
kai tsaye sai ya nufi hanyar da za ta sada shi da ɗakin abin
bauta gunki Zallas.
Da shigar shi ya zube ƙasa ya kwashi gaisuwa yana mai yi
mashi sujjada, a karo na farko sai matsafi Shamrul ya ji wata
irin kakkausar murya ya mamaye ɗakin baki ɗaya
"ya kai Shamrul ma'abocin biyayya a gare mu dago kanka
sama domin ka ji abin da zamu sanar da kai.
Cikin matuƙar al'ajabi matsafi shamrul ya dago daga
sujjadar, domin tsawon shekaru saba'in yana bauta ga gunki
Zallas amma bai taɓa jin ya yi mashi magana ba sai a yau.
Kakkausar muryar ma'abociyar tsoro da firgitarwa taci gaba da
cewa "haƙiƙa mun san kana cikin matuƙar fushi da damuwa
akan abin da ya faru tsakanin ka da hatsabibin yaro Imran, na
kunya taka a barnar jama'a, haƙiƙa yaro Imran ya taɓo tsuliyar
dodo, domin ba zai taɓa samun nasarar yaɗa addinin
musulunci a wannan birni namu ba.
Kuma lokaci ya yi da zamu kawar da dukkan wani
musulmi a doron ƙasa.
Abin da muke so da kai shine ka kwantar da hankalinka
tamkar tsumma a randa, a ranar da za a gabar da bikin bauta
zaka sha mamaki da idanunka, na mai tabbatar maka da cewa
a ranar zai zamto gawa dama dukkanin wanda ya kwaɗaitu
da shiga addinin shi.
Sa'adda da muryar ta zo dai-dai nan azancen ta sai
matsafi Shamrul ya cika da matuƙar farin ciki ya sake yin
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
90
sujjada a karo na biyu ga gunki Zallas. Sannan ya miƙe ya fice
daga ɗakin bautar.
Wannan shi ne abin da ya faru da matsafi shamrul bayan
ya rabu da yaro Imran.
Lokacin da su sarkin yaƙi Darusu suka cigaba da tafiya
a cikin birnin Istanbul ɗauke da sarki Lazwar, ɗaure a kan doki
cikin halin suma sai suka ci gaba da tafiya babu sassauci,
tafiyar daƙiƙa latalin kacal kaɗai su ka yi suka iso kofar gidan
sarautar birnin.
Gidan sarautar yakasance mai dogayen gine-ginen
zamani masu ƙayatarwa, koda isowar su sai waɗansu irin
girɗa-girɗan samudawan dakaru dake shirye cikin gagarumar
shigar yaƙi suka wangame makekiyar ƙofar shiga.
Inda za'a sanya katti majiya ƙarfi mutum saba'in ba za su iya
ture kofar ba,
Kai tsaye Sarkin yaƙi Darusu ya kunna kai izuwa ciki dakarun
shi na biye da shi, duk inda ya gifta a cikin gidan sai di ka ga
dakaru, kuyangi, barori, bayi na zube ƙasa suna kwasar
gaisuwa a gare shi
Daga cikin gidan sarautar ya kasance ƙasaitacce
tamkar aljannar duniya, babu wata halitta walau mutum ko
aljan da za ta tsinci kanta a cikin wannan gida face ta tabbatar
wa da kanta cewa gaba da gaban ta aljani ya taka wuta.
Shin yanzu idan har gidan sarautar birnin Istanbul ya
kasance haka to ya y turaka, da fadar sarki Ladiyas za su
kasance.
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
91
Tambayar da gimbiya mashlira ta yi wa kanta kenan
wacce ta saje cikin dakarun ba tare da an gane ta ba
Aka cigaba da tafiya har aka iso wani ɓangare a gidan
sarautar, kawai sai sarkin yaƙi Darusu ya yi umarni aka shigar
da sarki Lazwar izuwa ciki sannan ya dubi waɗansu dakaru
mutum biyar daga cikin su ya ce da su "ku tsaya anan har
izuwa lokacin da wannan baƙon jarumi zai farfaɗo, ku tabbatar
da cewa wani abu mai taɓa lafiyar shi ba".
Koda gama faɗin hakan sai sarkin yaƙi Darusu ya juya ya nufi
hanyar da za ta fitar da shi daga gidan sarautar sauran
dakarun suka mara mashi baya.
wannan shi ne abin da ya faru da sarki Lazwar a lokacin
da su sarkin yaƙi Darusu suka ɗauke shi a cikin halin suma.
Al'amarin abokan tafiyar sarki Lazwar sarkin yaƙi da
bawa Shamsal kuwa, koda ficewar su daga masaukin sai
sarkin yaƙi ya dubi bawa Shamsal ya ce dashi "wai kuwa me
ka fahimta game da hadima khadijat akankallon da naga tana
yi maka?
Koda jin wannan tambaya sai Shamsal ya yi shiru kamar mai
tunanin wani abu, daga can sai ya ɗago da kanshu ya dubi
sarkin yaƙi ya ce "ya sarkin yaƙi ka yi sani cewa haƙiƙa ban
fahimci wani abu ba game da kallon da khadijat ke yi min ba,
sai dai a lokacin da muka haɗa idanu na ji zuciyata ta buga da
ƙarfi".
Da jin wannan batu sai sarkin yaƙi ya yi murmushi ya ce
"ai kuwa dukkanin ku kun faɗa tarkon so ne ba ku sani ba,
lallai nan da wani lokaci za ku cigaba da kasance a kogin
SOYAYYA, amma wani hanzari ba gudu ba kai a yanayin da
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
92
kake kallon khadijat kana ganin cewa halin talauci ne ya sanya
ta yin aikatau a ƙarƙashin sarkin kasuwa Sha'aran?
Jiki na ba ni cewa tabbas akwai wani ɓoyayyen al'amari a tare
da ita.
Ko da jin wannan batu daga bakin sarkin yaƙi sai bawa
Shamsal ya yi shiru karo na biyu sannan ya dube shi ya ce
"tabbas maganar ka akwai ƙamshin gaskiya a ciki, domin a
lokacin da muka sauka a rumfa su muna cin abinci na ga
kallon da khadijat ke yiwa yaro Imran ya zarta misali. Bisa
nazari da nayi haƙiƙa kallo ne mai ɗauke da tsantsar tausayi
irin na 'yan uwa na jini. Amma dai ko ma dai mene ne komai
zai bayyana domin masu iya magana na cewa, komai nisan
jifa ƙasa zata faɗo, kuma a juri zuwa rafi wata rana tulu zai
fashe.
Sarkin yaƙi ya ce "tabbas zancen ka dutse ya abokina";
Daga wannan furuci ne kowannen su ya yi shiru.
Wannan shi ne abin da ya faru da tsakanin sarkin yaƙi da
bawa shamsal a masaukin su.
Al'amrin yarinya Shuraiba kuwa lokacin da gimbiya
Lamrat ta ɗauke ta a cikin keken dokin ta suka durfafi hanyar
da zata sada su da gidan sarauta, sai ya zamana cewa duk
inda suka gifta a cikin birnin Istanbul sai dai ka ga jama'a na
faɗuwa ƙasa suna gaisuwa tamkar za su yi mata sujjada.
Haka dai aka cigaba da wannan tafiya har aka iso ƙofar
gidan sarauta aka kunna kai izuwa ciki.
Bisa wani ƙasaitacce ɓangare da yafi ko ina ƙawatuwa a gidan
sarautar, keken dokin ya sauke su gimbiya Lamrat, kai tsaye
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
93
ta kutsa kai izuwa ciki, hannun riƙe da na yarinya shuraiba
dakaru na take mata baya, ɓangaren cike yake da kuyangi,
barori, hadimai da bayi suna ta kai komo suna ta hidima.
Nan fa ya zamana cewa yarinya Shuraiba ta zamto
cikakkiyar 'yar ƙauye, ta kama kalle-kalle da dube-dube
tamkar ɗan ƙauye ya shigo birni.
Wata kyakkyawar budurwa daga cikin kuyangin ta rugo izuwa
inda suke ta zube ƙasa ta kwashi gaisuwa ga gimbiya sannan
ta ɓuɗi baki cikin ladabi da girmama ta ce "ya shugabata shin
me kike da bukata?
Gombiya Lamrat ta ce "ya ke Lazura ki yi sani cewa abi nda
nake buƙata shi ne ki tafi da wannan yarinya a tsaftace mata
jikinta a sanya mata tufafi masu kyawu, sannan a haɗa mana
abin kalaci".
Ko da jin wannan umarni daga baƙin Lamrat sai kuyanga
Lazura ta risina ta ce "an gama ya shugabata"
Tana gama faɗin hakan sai ta miƙe tsaye ta kama hannun
yarinya Shuraiba ta shige da izuwa wani ɓangare na daban.
Sannan gimbiya ta shige izuwa turakarta dakaru masu tsaron
lafiyar na biye da ita.
Wannan shi ne abin da ya faru da yarinya Shuraiba da
gimbiya Lamrat matar sarki Ladiyas.
Al'amarin yaro Imran kuwa, lokacin da ya isa izuwa
masaukin su sai ya shiga kewaye ya watsa ruwa kuma ya
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
94
ɗaura alwala, sannan ya gabar da Sallar magariba, bayan ya
kammala ya yi godiya ga Ubangiji
Koda gama aiwatar da hakan sai ya ji an ƙwanƙwasa Ƙofar
dakinshi.
Kawai ya tashi ya je ya buɗe domin ya ga wane ne, sai ya ga
a she hadima khadijat ɗauke da abin kalaci da taceccen
ruwan inibi bisa kofin azurfa.
Bayan ta ajiye a gaban shi sai ta samu waje ta zauna shi ma
ya yi koyi da ita.
Khadijah ta dube shi ta ce "na samu wani labari dake yawo
a gari akan abin da yafaru tsakanin ka da matsafi Shamrul,
tabbas idan hakan ya tabbata dola ne mu kasance cikin shirin
ko ta kwana domin a kowane lokaci dakarun farmaki zasl su
dunga kawo mana ziyara don ganin bayan ka".
Koda jin wannan batu daga bakin khadijat sai yaro Imran ya
jinjina al'amarin a cikin ranshi
sannan ya dubi khadijat ya ce 'tabbas maganar ki gaskiya ce
ya 'yar uwanta, kuma Ubangiji yana tare da mu a kodayaushe
yanzu bari na yi kalaci sai ki dawo mu gabatar da sallar isha'i.
Da jin hakan saikhadijat ta miƙe tsaye ta juya ta fice daga
ɗakin tana mai waigen Imran.
Wannan shi ne abin da ya faru da yaro Imran lokacin da
ya isa masaukin su.
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
95
BABI NA SHA HUƊU
Lokacin da dare ya tsala sai sarkin yaƙi Darusu ya ɗauki
sarki Lazwar ya gurfanar da shi a gaban mai girma Ladiyas
Ladiyas, a lokacin da ya ke zaune a cikin wata ƙasaitacciyar
turaka. tsayawa musalta tsaruwa da ƙawatuwar turakar zai iya
zamowa ƙauyanci sai dai abin da idanu suka gani kawai komai
ƙasaitar BASARAKE ko attajiri idan ya tsinci kanshi a cikin
wannan dole ne ya zamto bagidaje kuma cikekken ɗan kauye.
Bisa wata ƙasaitacciyar kejera wani mutum zaune a kai.
Mutumin ya kasance mai ƙirar sadaukai ya tara ƙwanji,
kyakyawa ne na gaban kwatance kuma ma'abocin kwarjini da
haiba, Sanye yake da tufafi riga da wando irin na hamshakan
sarakai, kallo ɗaya za ka yi mashi ka fahimci cewa ya kasance
GWARZON DUNIYA mai ƙarfi na Allah ya isa.
Ba wani ba ne wannan mutum ba face sarki Ladiyas ibn
Fairuz. A wannan lokaci yana zaune yana hangen wani
ɓangare na lambun shaƙatawar daga tagar turakar. Yana cin
kayan marmari dake ajiye akan faranti na zinare bisa wani
madaidaicin teburi na azurfa.
Koda bayyanar sarkin yaƙi Darusu sai ya ajiye tuffa dake
hannunshu ya juya yana mai fuskantar shi. Gami da ƙarewa
sarki Lazwar kallo a lokacin da suke durƙushe a ƙasa bisa
gwiwoyinsu kuma sun sunkuiyar da kawunansu ƙasa.
Lokacin da sarki Lazwar ya ji shi durƙushe a gaban sarki
Ladiyas sai baƙin ciki da takaici suka mamaye zuciyarshi, ya ji
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
96
kamar ya ƙwalla ihu, wai yau a ce shi ne durƙusawa wani sarki
saboda kawai neman biyan bukata, a matsayin shu na
hamshaƙin sarki mai cike da taƙama da BAƘAR IZZA.
Tsawon daƙiƙa ana cikin wannan hali, sai daga bisani sarki
Ladiyas ya buɗi baki cikin wata irin kakkausar murya mai
tattare da jarumtaka ya buɗi baki ya ce "ya kai dirkar birnina
alamu sun nuna min baƙom bawan da ka zo da shi zai iya
kasance ɗaya cikin masu tsaron lafiyar gimbiya, amma sai dai
ba zai yiwu na amince da hakan ba face ya shiga izuwa ɗakin
duhu kuma ya samu nasarar cin jarabawar FARAUTAR RAI,
lallai ne gobe da safe ka gabatar da shi a fada domin yi mashi
jarabawar";
Koda jin wannan umarni daga bakin sarki Ladiyas sai
sarkin yaƙi darusi ya risina cikin ladabi ya ce "an gama ya
shugabana".
Yana gama faɗin hakan ya tashi tsaye ya juya ya fice
daga turakar sarki Lazwar ya yi koyi da shi yana mai bin
bayan shi, suka durfafi wani ɓangare daban.
Wannan shi ne abin da ya faru da sarki Lazwar a
lokacin da aka gabar da shi a gaban mai girma Ladiyas.
Al'amarin yarinya Shuraiba kuwa, lokacin da kuyangi
suka kammala yai mata wanka da ado kuma suka ciyar da ita
daddaɗan abinci, sai barci mai nauyi ya ɗauke ta.
Ba ta farka ba sai da dare ya tsala, a wannan lokaci gimbiya
na zaune a kusa da ita bisa kan gadon da take kwance.
Sa'adda ta ga Shuraiba ta farka daga barci sai ta sanya
hannayenta biyu tashe ta tsaye ta ja hannun ta izuwa wata
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
97
ƙasaitacciyar kujera, da a gaban ta aka ajiye wani teburin
azurfa mai ɗauke da nau'ikan abinci, bin sha da tanɗe-tanɗe.
Cikin matuƙar farin ciki gimbiya ta shiga ɗibar abinci da abin
sha tana bawa Shuraiba a baki.
Nan take Shuraiba ta ji tamkar mahaifiyarta ce ke ciyar
da ita, ita kuwa gimbiya farin cikin ta ba zai misaltu ba, bisa
ganin cewa yau ita ce ke ciyar da 'yarta da hannunta da ta
shafe tsawon shekaru tana kewar ta.
Bayan gimbiya ta kammala bata abincin, ita ma ta
kimtsa cikinta, sai Shuraiba ta shiga bawa gimbiya labarin
rayuwar ta, tun daga lokacin da sarki Ladiyas ya raba ta da
mahaifiyarta ya mayar da ita baiwar shi, har izuwa sa'adda
suka koma rayuwa a daji ita da mahaifinta, har kawo lokacin
da ta haɗu da su sarki Lazwar, tun daga farko har ƙarshe ta
zayyane wa gimbiya.
Sa'adda gimbiya ta ji wannan labari daga bakin yarinya
Shuraiba ba ta san sa'adda ta rungume ta ba su duka biyun
suna masu fashewa da matsanancin kuka mai tsuma zuciya.
sai daga bisa ne gimbiya ta janye jikinta daga na Shuraiba
suka fuskantaci juna.
Kawai sai gimbiya ta sanya hannunta ta ya ye mayafin dake
kanta fuskarta ta bayyana a fili ƙarara.
Sa'adda Shuraiba ta yi arba da fuskar gimbiya ba ta san
sa'adda ta sake rungume ta ba a karo na biyu tana mai fashe
da kukan murna.
Ba komai ne ya sanya ta hakan ba sai domin arba da ta yi da
fuskar mahaifiyarta Lamrat,
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
98
tana mai cewa ashe zan sake ganin ki ya ummina ashe
daman kina raye?
Daƙyar gimbiya Lamrat ta lallashe ta tayi shiru ta share mata
hawaye, bayan ta samu nutsuwa ne sai ta dube ta cikin
annashiwa da farin ciki ta ce "ya 'yata kuma farin zuciyata
Haƙiƙa ina raye ban mutuwa, a kowace rana idan dare ya
tsala sai nayi kukan baƙin ciki tare da roƙon abin bauta akan
ya kare min ke kuma ya kawo min lokacin da zan ɗauki fansa
akan BAKIN AZZALUMI da ya lalata rayuwar mu wato sarki
Ladiyas. Sai gashi abin bauta ya dawo min dake cikin ƙoshin
lafiya, ina so mu ɓoye sirrin dake tsakanin mu har izuwa
lokacin da zamu ɗauki fansa.
Saboda hakan ma ya sanya na ɓoye miki fuskata a lokacin da
muka haɗu a kasawu, domin matuƙar wani ya gane hakan har
sarki ya samu labari tofa dukkan shirin mu ya tarwatse.
Sa'adda gimbiya ta zo dai-dai nan azancenta sai yarinya
Shuraiba ta cika da matuƙar farin ciki maral-musaltuwa, tana
mai cewa tabbas na aminta da ke ummina kuma za mu ɗauki
fansa akan sarki Ladiyas.
Wannan shine abin da ya wakana tsananin yarinya
Shuraiba da mahaifiyarta gimbiya Ramlat.
Al'amarin yaro Imran kuwa tun sa'adda ya yi bankwana
da hadima Khadijat bayan sun sun tattauna akan abin da ya
wakana tsakanin shi da matsafi Shamrul a cikin kasuwa, sai
ya shiga kimtsa cikin shi bayan ya kammala ne Khadijat ta
dawo gare shi suka gabatar da sallar Isha'i
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
99
Bayan kammala wa ne ya kwanta domin ya huce gajiyar dake
tattare da shi.
Wannan shi ne ya faru da yaro Imran ma'abincin addinin
Musulunci.
BABI NA SHA BIYAR
BIRNIN ISTANBUL
Kashe gari tunda duku-dukun safiya fadar sarki
Ladiyas ta cika ta batse da jama'a maza, mata yara da manya,
duk inda mutun ya duba kawunan bil'adama rututu babu
masaka tsinke, tamkar dandazon kiyasai.
Domin a yau ne aka samu labarin cewa za'a gudanar da gasar
farautar rai, domin tsallake matakin ƙarshe da zai bawa sarki
Lazwar damar kasance ɗaya daga cikin masu tsaron lafiyar
gimbiya Lamrat.
Bayan jama'a sun hallara kuma sarki Ladiyas ya
hakimce a bisa karagarshi ta mulki, sanye cikin ƙasaitacciyar
shiga ta kece raini. Ana cikin wannan hali ne kwatsam! Sai
aka hango sarkin yaƙi Darusu ya shigo izuwa fadar tare da
dakaru sun tuso ƙeyar sarki Lazwar ɗaure a cikin sarari na
baƙin ƙarfe.
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
100
Sa'adda jama'a suka yi arba da sarki Lazwar sai fadar ta
kaure da shewa, sai da sarkin yaƙi ya ɗaga hannunshi sama
sannan fadar tayi tsit tamkar mutuwa ta kawo ziyara.
Sannan ya fuskanci mutane bayan ya yi gyaran murya sai ya
buɗi baki ya ce ''ya ku jama'ar wannan fada mai albarka ku yi
sani cewa ba komai ne ya sanya muka tara ku anan ba sai
domin a yau ne mai girma Ladiyas ya bayar da umarnin a
saka jarumi Lazwar izuwa ɗakin duhu. Domin ya yi
gwagwarmaya da miyagun halittun da suke ciki kuma idan ya
samu nasarar tsallake matakin zai zamto daya cikin masu
tsaron lafiyar mai martaba sarki.
Sa'adda sarkin yaƙi Darusu ya zo dai-dai nan a zancen
shi, sai fadar ta sake kaurewa da shewa a karo na biyu, sai
daga bisani ne sarkin yaƙi ya umarci waɗansu dakaru mutum
hamsin suka wangame wata makekiyar kofar dake jikin
bangon fadar, take wani makeken ɗaki ya bayyana mai ɗauke
da waɗansu nau'ikan halittu dangin kuraye da zakuna gami da
macizai.
Cikin hanzari waɗansu dakarun na daban suka buɗe
ƙofar ɗakin, su ɗauki sarki Lazwar suka jefa shi izuwa ciki,
kana suka kwance sarƙoƙin dake riƙe da halittun, suka mayar
da ƙofar suka rufe ruf!
Sa'adda gimbiya Mashlira dake sanye cikin tufafin
dakaru cikin ɓaddakama, ta ga an sanya masoyinta Lazwar a
cikin ɗakin duhu sai takaici da baƙin ciki suka mamaye
zuciyartq taji kamar ta ƙwallawa ƙara.
Amma sai ta danne saboda ta san cewa ba don komai
masoyin nata ya shiga wannan hali ba sai domin kawai ya
sadu da baiwa Sharifa da zata taimaka mashi wajen mallakar
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
101
abubuwan da zasu warkar da shi daga sihirin da abokin gabar
shi ya yi mashi, sai kawai ta shiga yi mashi fatan samun
nasara, amma har yanzu hankalin ta a matuƙar tashe ya ke
ainun.
Nan fa aka fara kallon-kallo tsakanin sarki Lazwar da
halittun, kuraye biyu zakuna biyu sai waɗansu rin mucizai
masu kawuna biyar.
Duk da kasancewar sarki Lazwar GWARZON MAYAƘI kuma
GWARZON DUNIYA sai da hankalin shi ya dugunzuma
ainun, domin iya tsawon rayuwarshi bai taɓa gani ko jin labarin
halittu masu kwarjini da ban tsoron tamkar su ba.
Tsawon daƙiƙa hamsin halittun na kewaye lazwar suna
gurnani gami da hargagi mai matuƙar ban tsoro, sai daga
bisani ne suka yi ɗauki kan shi suna kururuwa da ihu mai
ɗimauta DANDAZON MAYAƘA suna masu kai mashi cizo da
yakushi da faratansu, macizan na kai mashi sara gami da
furzar da dafi daga bakunansu cikin wani irin baƙin zafin nama
da ya ɗimauta hankali.
Shi kuwa sarki Lazwar ya wanzu ya na zillewa tare da
kaucewa hare-haren halittun cikin zafin nama JURIYA DA
BAJINTA. Sai da sa'a ɗaya da rabi ta shuɗe ana wannan
ɗauki ba daɗi ba tare da ɗaya daga cikin su ya samu nasara
ba, a dai-dai wannan lokaci ne halittun suka fara galabaitar da
Lazwar ya zamana cewa ba ya iya mayar da martani sai dai
ƙoƙarin kare kanshi.
Ana cikin artabun ne wani daga cikin zakunan ya
yakushe shi a cinyarshi ta hagu take ya yi mashi mugun rauni,
sarki Lazwar ya kurma wawan ihu sakamakon tsananin zafi da
zugin da ya ji jini ya kwaranya.
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
102
Kafin ya sake yin wani yunƙuri wani maciji ya kafta mashi
wawan sara a gadon bayanshi, saboda matuƙar azaba sai da
sarki Lazwar ya faɗi a ƙas yana nishin wahala.
Nan fa masoyan sarki Lazwar suka cika da matuƙar baƙin ciki
har waɗansu na zubar da hawayen takaici bisa ganin halin da
jarumin su ke ciki.
Shi kuwa Sarki Ladiyas dake hakimce bisa karagar mulkin
sai ya shiga ɓaɓɓaka dariyar mugunta har da kyakyatawa nan
fa sauran 'yan majalisa da fadawa suka yi koyi da shi.
Al'amarin da ya sanya zuciyar gimbiya Mashlira ta karaya
kenan har kwalla ta cika mata idanu, bisa ganin halin da
masoyinta ke ciki amma saboda tsoron kar wani ya gane halin
da take ciki asirinta ya tunu sai ta yi sauri ta goge hawaye
dake kan fuskarta, dai-dai lokacin ne ta hango bawa Shamsal
da sarkin yaƙi a cikin jama'ar gari suka zubar da hawayen
takaici bisa ganin halin da shugabansu ya tsinci kanshi a ciki,
da koyaushe zai iya rasa rayuwar shi.
Lokacin da sarki Lazwar ya tsinci kanshi a tsakanin
RAYUWA DA HALAKA, kuma ya tabbatar da cewa haƙiƙa a
koda yaushe zai iya sheƙawa barzahu, sai kawai ya fara
amfani da zallar ƙarfin sihirin tsafinshi, amma sai ya zamana
cewa tamkar yana inziga miyagun halittun wajen kai mashi
farmaki.
Kwatsam! sai yaro Imran ya faɗo masa a rai zuciyarshi
na raya mashi cewa kawai ka nemi taimakon Ubangijin yaro
Imran tun da dukkanin wata dubara ta ƙwace maka, domin
masu iya magana na cewa da asara gwara gidadanji. Kuma
wanda ya faɗa teku ko KAIFIN TAKOBI aka miƙa mashi sai ya
kama domin ya tsira.
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
103
Tun da a halin yanzu ba wanda zai gane cewa ka
nemi taimakon Ubangijin Imran sai kai kaɗai. Sa'adda sarki
Lazwar ya zo nan a tunanin shi sai kawai ya yi kabbara yana
mai ambaton sunan Allah a cikin ranshi yana mai cewa "ya
Ubangijin imran ka tseratar da ni daga sharrin miyagun
halittun nan".
A dai-dai wannan lokaci ne wani ɗaya daga cikin zakokin ya
wangame bakinshi da nufin ya cinye yan yatsun Lazwar na
hannu.
Kwatsam! Bazato babu tsammani sai aka ga Lazwar ya
kurma wawan ihu cikin wani zafin nama na ban al'ajabi yana
daga kwance ya kama wuyan zakin da hannayen biyu ya
murɗe wuyan shi, take ya karye ya yi ƙara ji kake ruƙus! Ƙas
ya sheƙa barzahu ko shurawa bai yi ba, sannan ya miƙe tsaye
zumbur aka sake yin wani sabon kallon-kallo tsakanin shi da
sauran halittun.
Nan take fadar ta ruɗe da shewa masoyan sarki lazwar
suka cika da matuƙar farin cikin bisa ganin gwaninsu ya miƙe
tsaye.
Shi kuwa sarki ladiyas fuskarshi a murtuke take babu
annuri domin tsawon shekarun da aka shafe ana gwada
jarumai, ba a taɓa samun wanda ya kashe dabba ɗaya daga
cikin halittun ba.
Daga can sai dukkan halittun suka afkawa Lazwar aka
sake ruguntsume wa da azababban yaƙi mai matuƙar muni da
ban tsoro.
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
104
A wannan karon sai ya zamana cewa duk wanda Lazwar ya
gabza wa naushi a cikin halittun sai kaga ya yi sama tamkar
an janye shi da ƙungiya sannan ya faɗo ƙasa tim.
Amma saboda na ci da zafin nama irin na halittun sai su
miƙe tsaye zumbur su sake afka mashi da dukkanin
tsagwaron ƙarfin damtsen su.
Kafin cikar rabin sa'a sarki Lazwar ya kashe gaba ɗaya
halittun ya jefar da gawarwakin su a ƙas, nan fa fadar ta kaure
da shewa da ihu jama'a suna ta mamakin wannan jarumtaka
ta sarki Lazwar, domin a tarihin gasar shi ne mutum na farko
da ya taɓa kashe miyagun dabbobin baki ɗaya.
Ita kanta gimbiya Mashlira 'yar sarkin maridai bata san
sa'adda murmushin farin ciki ya suɓuce mata ba.
Al'amarin da ya sanya zuciyar mai girma Ladiyas ta ci gaban
da tafarfasa tamkar zata ƙone kenan.
Kodasamun wannan nasara da sarki Lazwar ya samu
sai sarkin yaƙi Darusu ya umurci waɗannan dakaru mutum
Hamsin suka je suka buɗe ƙofar ɗakin aka fito da sarki
Lazwar, likitoci suka shiga ba shi taimakon gaggawa domin
tsayar da jinin dake zuba a jikinshi tare sanya mashi magani
akan raunukan shi .
Ana cikin wannan hali ne kwatsam! Bazato babu tsammani sai
aka hango waɗansu dakaru mutum arba'in shirye cikin
gagarumar shigar yaƙi sun tuso ƙeyar yaro Imran da hadima
Khadijat, ɗaure cikin sasari na baƙin ƙarfe hannu da ƙafa.
A gefe guda kuma matsafi Shamrul ne tare tawagar
malaman addininsu sanye da tufafi irin na bauta.
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
105
Lokacin da ya zamana tazarar dake tsakanin su da
karagar mulki bai huce taku goma ba sai matsafi shamrul da
sauran bokaye suka zube ƙasa bisa gwiwoyin su suka kwashi
gaisuwa ga sarki ladiyas. Suna masu sunkuiyar da kawunansu
ƙasa.
Sai da suka ɗauki lokaci a cikin wannan hali sannan daga
bisani matsafi Shamrul ya dago da kanshi sama ya buɗi baki
cikin ladabi da girmamawa cikin wata irin kakkausar murya
mai kama da kukan jaki ya ce "ya shugabana haƙiƙa
abinbauta ya bada umurnin a yanka waɗannan mutane biyu
mace da namiji da suka shigo mana da wani sabon addini mai
suna musulunci wanda suke jan hankalin mutane wannan birni
mai albarka, wanda a dalilin hakan zai janyo mana musiba da
annoba da zata haifar da suɓucewar mulkin ka".
Sa'adda da sarki Ladiyas ya ji wannan batu daga bakin
matsafi Shamrul sai zuciyarshi ta kama tafarfasa tamkar zata
fasa ƙirjinshi ta fito waje, yaji ya tsani hadima Khadijat da yaro
Imran.
Kawai sai ya dubi Khadijat da fuskar ta ke rufe da rawani ya
ce ''ya ke baiwa Sharifa haƙiƙa kin yaudare ni kin ci amanata
da kika zo da wani sabon addini a wannan birni nawa, na aika
ki zuwa ga sarkin kasuwa domin ki gane ki zamto 'yan leƙen
asiri, domin ki taimaka min na samu nasarar ganin bayanshi,
haƙiƙa a yau zan yanke miki hukunci dai-dai da laifin da kika
aika ta a gareni";
Sa'adda da mai girma Ladiyas ya zo nan a zancen shi
sai sarki Lazwar dake gefe guda likitoci na duba lafiyar shi ya
cika da matuƙar al'ajabi da mamaki ainun, bisa jin sarki
Ladiyas ya kira hadima Khadijat da suna baiwa Sharifa.
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
106
Shin dama Khadijat ita ce baiwa Sharifa da ya fito farautar ta
ruwa a jallo?
Tabbas tsugunne bata ƙare ba wai an saci ɗan ɓarawo.
Haƙiƙa dole ne ya yi sabon gumurzu domin ceton rayuwar
Khadijat.
Sarkin yaƙi, Bawa Shamsal da aljani Za'aratul-layal
dake cikin siffar bil'adama tare da gimbiya Mashlira dake
sanye da tufafin dakaru cikin ɓaddakama, sai suka cika da
matuƙar mamaki bisa jin ashe hadima Khadijat ita ce baiwa
Sharifa,
wannan fa shi ne masu iya magana ke cewa "rashin sani kaza
ta kwana akan dami".
Ashe sarki Lazwar na tare da abin da yake nema bai sani
ba har ya shigar da kanshi cikin uƙubar sarki Ladiyas.
A ɓangaren jama'a kuwa sa'adda ji