An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
1
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
2
SARAUTAR MUTUWA
Rubuta Labari
MANSUR USMAN SUFI
sarkin Marubutan Yaƙi
Haƙƙin Mallaka
SUFI
Shekarar bugu
2023
Rubuta Labari
GODIYA
Ta tabbata ga Allah (SWT) bisa iko da ya ba ni na
rubuta wannan littafi mai suna SARAUTAR MUTUWA.
Tsira da amincin Allah ya ƙara tabbata ga Annabi
Muhammadu (SAW) da iyalanshi tsarkaka da sahabbanshi
masu haske.
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
3
SADAUKARWA
Wannan littafi sadaukarwa ne ga ɗaukacin masoya Annabi
Muhammadu Sallallahu alaihi a ko ina suke a faɗin duniya.
Tsarawa da bugawa SUFI PUBLISHING COMPANY
R/lemo L/ Pol KanoNigeria
BABI NA ƊAYA
A ƙarni na biyu bayan yaƙin duniya na ɗaya, a yankin
arewacin larabawa anyi wani ƙasaitacce birni da ake yiwa
laƙabi da zawatul-ifdar.
Birnin zawatul-ifdar ya bunƙasa a harkokin kasuwanci, noma,
kiwo da ƙarfin tattalin arziki.
Sarkin dake mulkin birnin ya kasance gawurtaccen matsafi
kuma mashahurin attajiri ana yi mashi laƙabi da Lazwar ibn
kaulat.
A gaba ɗaya nahiyar larabawa babu mashahurin sarki
tamkar shi bisa wannan dalili ne ya sanya ya zamto
GAGARABADAU a tsakanin sarakunan nahiyar.
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
4
Duk waɗannan abubuwan da sarki Lazwar ya tara da ya
danganci ƙarfin sihiri da tarin dukiya gami da ƙarfin masarauta
ya tashi a banza, domin a daren kowace rana sai na kulle ƙan
shi a turakarshi ya yi ta kukan takaici da baƙin ciki, har sai
kuyanginshi sun shayar da shi barasa sannan yake samun
barci.
Ba komai ne yake sanya sarki Lazwar wannan kuka ba
face wani dalili guda ɗaya jal!
Dalilin kuwa shine bisa binciken da ya gudanar bisa halarar
tsafin shi ya gano cewa har abada ba zai samu haihuwa da
kowace 'ya mace ba face ya karya wani sihirin da abokin
gabar shi sarki Darwazu ya yi mashi.
Matsawar kuwa ya yi ganganci ya sadu da wata 'ya
mace koda kuwa kuyangarshi ce, take dukkanin sirrikan
tsafinshi da duk abin da ya mallaka zai ƙare zai dawo talaka
(faƙiri).
Tsawon shekaru biyar sarki Lazwar yana cikin wannan
baƙin ciki dare da rana.
Kwatsam! Wata rana sai kawai aka ji ya ƙwalla ƙara sannan
ya bushe da dariya, sautin dariyar tashi ya amsa kuwwa izuwa
gidan sarautar baki ɗaya.
Al'amarin da ya yi matuƙar bawa kowa mamaki kenan, domin
yau tsawon shekaru biyar ba'a taɓa jin shi ya yi hakan ba.
Abin da mutane ba su sani ba shi ne bakomai ba ne ya
sanya sarki lazwar wannan dariya ba,
sai domin yau ne ya gano hanyar da zai lalata sihirin da
abokin gabarshi sarki darwazu ya yi mashi.
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
5
Abu na farko da zai mallaka shi ne hawayen wani
gawurtaccen dodo dake zaune a dajin Darul-shatir dodo
Murgazu ya kasance hatsabibi wanda ya addabi fatake da
biranen dake maƙwabtaka da dajin Darul-shatir.
Abu na biyu shine tsumin tsafin bokanya Lazira,
bokanya Lazira ta shafe tsawon shekaru dubu biyu tana tsuma
tsumin tsafin domin ta cika burin ta na tashin kakanta sarkin
bokaye daga cikin kushewarshi, domin ya sanar da ita
waɗansu sirrikan tsafi da zata mulki duniya da su.
Abu na uku shine ruwan tekun Bahar-dawa'u, tekun
Bahar-dawa'u na yamma maso arewacin duniya, yana ɗauke
da waɗansu irin musifaffun kifaye da macizai da adadin su ya
kai dubu biyar, tsananin ƙarfin damtsen ɗaya daga cikin
halittun ya nunka na bil'adama sau hamsin.
Abu na huɗu shine alƙyabbar sarkin bokayen duniya na
ɗaya boka Murkatul-azab, a halin yanzu alƙyabbar na ajiye a
fadarshi dake ƙarƙashin tekun Bahar-maliya, matsafa, bokaye
da masu hasashe sun tabbatar da cewa a halin yanzu a
duniya babu wani waje mai tattare da musibu tamkar fadar
sarkin bokayen duniya.
Abu na ƙarshe shi ne wata jaruma da ake yiwa laƙabi da
Sharifa bintu Usman.
A halin yanzu Sharifa na bauta ne a ƙarƙashin masarautar
birnin Istanbul a matsayin baiwa, mahaifanta sun rasu ne a
bisa KANGIN BAUTA a masarautar.
Baiwa Sharifa ce kaɗai zata iya taimaka mashi ya samu
nasarar mallakar waɗancan abubuwa.
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
6
Sa'adda darki Lazwar ya ga wannan al'amari sai ya cika
da matuƙar farin ciki, sai dai wani abu daya dugunzuma
hankalin shi, shine halarar tsafinshi ta bayyana mashi cewa ba
zai taɓa samun nasarar saduwa da baiwa Sharifa ba har ya
samu damar bayyana mata buƙatar shi na son taimaka mashi
ya samu don mallakar waɗancan abubuwan da zai karya
sihirin ba, face shima ya mayar da kanshi bawa ya yi bauta a
ƙarƙashin masarautar na tsawon shekaru.
Sannan ma inda gizo ke saƙar shi ne, ba lallai ne Sharifa
ta iya amincewa da buƙatar shi ba, tunda a halin yanzu ta rasa
dukkan wani farin cikin rayuwar ta.
Kasancewar masu iya magana na cewa biyan buƙata yafi
dogon buri, kuma inda rai da rabo.
Kawai sai ya yanke ranar da zai fita farautar baiwa
Sharifa.
BABI NA BIYU
Kashe gari tun da duku-dukun safiya sarki Lazwar ya fara
shirye shiryen tafiya izuwa birnin Istanbul , a dai-dai lokacin da
rana ta fara haske ne ya kammala shirin tsaf!
Tun daga kuyangi masu hidima, dakaru, gami da bayi.
A can fada kuwa jama'a sun cika maƙil babu masaka tsinke.
Duk inda mutum ya kalla kawunan bil'adama ne rututu babu
saka tsinke tamkar dandazon kiyasai.
Kowa ya zuba idanu ana jiran fitowar sarki domin ganin wane
zai baiwa riƙon sarautar shi.
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
7
Tsawon daƙiƙa latalin ana cikin wannan hali sai daga
bisani ne aka jiyo bushin algaita haɗe da bugun tambura.
Daga can sai ga sarki Lazwar tafe tare da tawagarshi yana
sanye cikin surutu na alfarma da sukayi matukar yi mashi
kyawu, kai tsaye ya huce izuwa kan karagarshi ta mulki ya
tsaya sannan ya fuskanci jama'a ya yi gyaran murya ya ce "ya
ku mutanen wannan fada tawa mai albarka ku yi sani cewa a
yau ne zan yi gagarumar tafiya izuwa nemo abubuwan da za
su warkar da ni daga sihirin da abokin gaba ta sarki Darwazu
ya yi mini.
A bisa al'adar wannan masarauta sarki da kanshi yake zaɓar
wanda zai bawa riƙon sarautar shi.
Bisa ga nazari da kuma hasashe da nayi babu wanda zai riƙe
sarautar wannan birni da amana face magajin gari Yasiran".
Sa'adda sarki Lazwar yazo nan a zancen shi sai jama'a
suka ruɗe da shewa da jinjina domin suna ganin shike nan
sun huta da mulkin zaluncin sarki lazwar.
Kaico! Tabbas masu iya magana sunyi gaskiya da suka ce
rashin sani yafi dare duhu, inda a ce jama'a sun san wane ne
magajin gari Yasiran da sun gwammace gwara sarki lazwar
sau ɗari.
Bayan an ɗora Yasiran a bisa karagar mulki sai kawai sarki
Lazwar ya buɗe bakinshu ya ƙwala wa wani hadimin aljanin
shi kira sau uku, yana gama rufe bakinshi sai kaga wata halitta
shirgegiya na ketowa daga cikin gajimare tana sauka daga
sararin samaniya. Nan fa suka ɗimauce suka fara guje-guje da
ifice-ifice tamkar sun hango mutuwarsu, wasu ma saboda
razani har sakin fitsari suke a wando basu sani ba.
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
8
Aljanin ya sauka a turba yana mai shimfiɗe fuka-fukanshi a
ƙasa, shi dai aljanin ya kasance shirgege tamkar tsauni yana
da rafkeken kai mai ɗauke da kwala-kwalan idanu jajur tamkar
garwashin wuta, hancinshu ƙato ne kofofinshi tamkar bututun
shaƙar iska, bakinshi yana da girma tamkar bakin rijiya,
maƙale a kwiɓin hamatarshi yana ɗauke da manyan fuka-fukai
guda huɗu.
Haƙiƙa wannan aljani yakasance mummuna kuma abin tsoro
ga duk wata halitta mai numfashi.
Aljanin ya kwashi gaisuwa cikin girmamawa ga sarki Lazwar.
Sannan ya ɗago da kanshi ya dubi sarki Lazwar cikin ladabi
ya ce cikin wata irin kakkausar murya mai kama da kukan jaki
ya ce "ya mai duniya gani na amsa kiran ka me kake da
buƙata ya shugabana?
Wani alfahari ya shiga kwanyar sarki lazwar jin aljanin ya
ambace shu da mai duniya,
cikin BAƘAR IZZA Lazwar ya ce " ya kai Za'aratun-layal ka yi
sani cewa bakomai ya sanya na kira ka nan ba sai domin ka
ɗauke ni da tawaga ta domin gudanar da wata gagarumar
tafiya mai matuƙar haɗari.
Sai dai ina so ka yi sani cewa wannan shine aikin ka na
ƙarshe da zan 'yan ta ka ' daga ƘANGIN BAUTA a gare ni".
Ko da jin wannan batu daga bakin sarki Lazwar sai aljani
Za'aratun-layal ya bushe da dariyar farin ciki, dariyar tashi ta
haddasa wata gagarumar girgizar ƙasa mutane suka fara
halaka, sai da sarki Lazwar ya daka mashi tsawa, sannan ya
tsuke bakinshi, a sannanne komai ya samu dai-dai ta.
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
9
Ba tare da ɓata lokaci ba sarki Lazwar da tawagarshi su ka
hau bisa kan Za'aratun-layal da ya haɗar da sarkin yaƙin birnin
da waɗansu zaratan bayi gami da kuyangi masu hidima suka
zauna aka ɗora abin guzuri akai.
Sannan aljani Za'aratun-layal ya yunƙura ya tashi sama
yana mai kaɗa fuka-fukanshi tare luluƙawa cikin gajimare yana
mai tsala azababban gudu, tun jama'a na daga masu hannu
har suka dai na hango su.
Sai da aka shafe tsawon sa'a bakwai ana tafiya a sararin
samaniya ana keta gajimare cikin matsanancin gudu tamkar
giftawar tauraruwa mai wutsiya.
Lokacin da sa'a ɗaya ta shuɗe ne aljani Za'aratun-layal
ya saki fuka-fukanshi ya sauka a turba,inda ya saukar
yakasance wani daji ma'abocin kwarjini daban tsoro tun da
aka shiga dajin kowa yasha jinin jikinshi, domin dole ne a
samu wani abu mai cutarwa a cikin shi.
Ana cikin wannan hali ne kwatsam! Sai aka ga waɗansu
irin masifaffun kibiyoyi suna sauka a dajin, duk da irin
ƙwarewa ta dakarun sarki Lazwar kafin su yi wani yunƙuri sai
da kibiyoyin suka hallaka fiye da mutum ɗari.
Al'amarin da ya fusata sarki Lazwar kenan ya karanta
waɗansu ɗalasiman tsafi amma bisa mamaki sai kawai ya ga
ya zama hayaƙi.
Al'amarin da ya yi matuƙar bashi mamaki kenan kuma ya
ɗaure mashi kai kawai sai ya zare takobinshi ya kama kallekalle da dube-dube a dajin cikin matuƙar fushi.
Kwatsam! sai aka jiyo motsawar ganyayyakin bishiyun daga
wani ɓangaren dajin, daga can sai a kayi arba da wata
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
10
kyakkyawar yarinya mai kimanin shekaru goma sha biyu,
zaune a bisa kan shirgegiyar damisa jikin ta sanye da kayan
fata riga da wando da takalmi, a gadon bayanta tana rataye da
wata zabgegiyar takobi, a hannunta na riƙe da wata irin kwari
da baka, nan fa aka fara kallon kallo tsakanin su sarki Lazwar
da yarinyar.
Lokacin da aka shafe tsawon daƙiƙa latalin ana kallon-kallo
tsakanin wannan kyakkyawar yarinya da su sarki Lazwar. sai
Lazwar ya katse shirun da ya wanzu ta hanyar duban yarinyar
cikin matuƙar fushi yana mai nuna ta da tsinin takobinshi cikin
kakkausar murya ya ce "ya ke wannan 'yar ƙaramar ƙwaruwa
shin wane irin rashin hankali ne ya sanya ki aikata wannan laifi
a gare ni? Ina so ki bani amsar wannan tambaya kafin na zare
miki ruhinki daga gangar jikinki kiyi mutuwar wulakanci.
Ko da jin wannan tambaya sai kawai kyakkyawar yarinyar
ta bushe da dariyar mugunta.
Al'amarin da ya bawa kowa mamaki kenan kuma ya fusata su
ainun, bisa ganin cewa yarinya ƙarama da bata huce ayi mata
kwab ɗaya ba amma ta yi GABA DA GABA da dandazon
mayaƙa amma bata razana ba.
A Lokaci guda yarinyar ta murtuke fuska sannan ta dubi sarki
Lazwar cikin wata irin zazzaƙar murya mai ɗan karan daɗi
tamkar sarewa ta ce
"Ya kai sarki Lazwar ibn kaulat na birnin zawatul-ifdar ka yi
sani cewa fiye da shekaru biyar baya na san da labarin ka
kuma zaka yaɗa zango a wannan daji domin ka gudanar da
tafiyar ka ta nemo abubuwan da za su warkar da kai daga
sihirin da abokin gabar ka sarki Durwazu ya yi maka.
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
11
Ko da jin wannan batu daga bakin kyakkyawar yarinyar
sai sarki Lazwar ya cika da matuƙar mamaki ya dubi yarinyar
ya ce "shin ya aka yi kika san ko ni wane ne kuma mene ne
buƙatar ki agare ni.
Yarinyar ta ce "mahaifina mafarauci Murrasu kafin rasuwar shi
ya sanar da ni labarin ka kuma ya bayyana mini cewa kai ne
zaka iya taimaka mini na samu nasarar saduwa da mahaifiya
ta dake ƘANGIN BAUTA a can birnin Istanbul bayan na
taimaka maka ka sadu da Baiwa sharifa wacce za ka je
farautar ta a cikin birnin Istanbul.
Ko da jin wannan batu daga bakin kyakkyawar yarinyar
sai sarki Lazwar ya sake cika da matuƙar mamaki,
kuma ya taka da ƙafafuwanshi ya durfafi inda take ya yin da
ya rage saura taku goma a tsakanin su sai ya ja ya tsaya.
Cike da matuƙar mamaki ainun ya sake duban ta ya ce "ya ke
wannan yarinya mai abin al'ajabi shin mene ne labarin ki?
Kuma mene ne ya kai mahaifiyarki bauta a birnin Istanbul?
Da jin waɗannan tambayoyi sai hawaye suka kwaranyo
daga idanun yarinyar.
Al'amarin da ya yi matuƙar bawa sarki lazwar mamaki kenan
ya ce a ran shi, shin ina dalilin wannan hawayena yarinyar?
Yarinyar ta share hawayen ta cikin alamun matuƙar
damuwa ta ce "da farko dai suna na Shuraiba bintu Murrasu,
ya kai Lazwar ka yi sani cewa mahaifina mafarauci Murrasu
lokacin yana raye yakasance babban hadimi ga sarkin birnin
Istanbul, shi ne mai kula da abin da ya shafi tufafin da sarki ke
sanyawa da ma sauran iyalan gidan sarautar birnin baki ɗaya.
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
12
Wata rana mahaifina ya fita farauta daji domin farauto
wata dabba da sarki ya ce ke bukatar a yi mashi alƙyabba da
ita.
Tun safe ya tafi amma har la'asar ta shuɗe bai dawo ba nan fa
ni da mahaifiyata mu ka shiga cikin matuƙar damuwa, muna
cikin wannan hali ne kwatsam! Bazato babu tsammani sai mu
ka jiyo haniniyar dawakai a can ƙofar gida
Kafin mu yi wani yunƙuri sai muka ga dakarun sarki sun shigo
gidan, ina ji ina gani su ka kama mahaifiyata ta ƙarfin tsiya
suka tafi da ita.
Ina ta rusa kuka tamakar raina zai fita a daren wannan rana
ne mahaifina ya dawo daga farauta hankalin shi a tashe
idanunshi sharkab da hawaye kuma jikinshi duk jini.
Ko da mahaifina ya ganni a cikin wannan hali sai ya janyo ni a
jikinshi ya rungume a lokaci guda mu duka biyun mu ka fashe
da matsanancin kuka mai tsuma zuciya daban tausayi.
Sai da muka ɗauki tsawon lokaci a cikin wannan hali sannan
daga bisani mahaifina ya janye jikinshi daga nawa.
Bata re da ya ce mini ƙala ba ya ɗauki wata jakar fata sai
KWARI DA BAKAN shi da ke rataye a gadon bayanshi kawai
sai ya kama hannuna muka fice daga cikin gidan muka nufi
Kofar gari, har muka fice daga birnin muka nausa izuwa cikin
daji, a kowacce rana sai nayi kuka wiwi ina mai tambayar
mahaifina ina ummana ta ke. Amma sai ya lallashe ni ya
kwantar min da hankali cewa ba wani abu ne ya same ta
bazata dawo gare mu cikin ƙoshin lafiya.
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
13
Bakomai ya sanya mahaifina yaƙi sanar da ni labarin
mahaifiyata ba, sai domin ganin cewa ni yarinya ce ƙarama
bansan komai a rayuwa ba.
Sai bayan na girma ne mahaifina ya bani labarin irin zaluncin
da sarki ya yi masa na mayar da ummina baiwarshi da yake
saɗaka da ita, saboda al'adar sarki duk macen da ya ƙyallara
idanu ya gan ta in dai har ta yi mashi to ko matar wane ne sai
ya kwace ta ya aure ta ta ƙarfin tsiya.
Baƙin cikin rashin mahaifiyata shine abin da ya yi sanadin
mahaifina cutar ajali ta kama shi.
A daren ranar da zai rasu ne ya mallaka mani KWARI DA
BAKAN shu da dukkanin kayan farautar shi bayan ya sanar da
ni dukkan sirrikan birnin Istanbul da shi kanshi sarki Ladiyas
kuma ya ba ni dukkanin labarin ka ya kai Lazwar.
Tun bayan rasuwar mahaifina ne na sha alwashin ceto
rayuwar mahaifiya ta daga hannun sarki Ladiyas, dare da rana
ina rayuwa a cikin ƙunci da baƙin ciki, babu abin da ke ɗebe
mini kewa face wannan damisa da na gada daga wajen
mahaifina.
Sa'adda kyakkyawar yarinyar tazo nan a labarin ta sai ta
fashe da kuka mai matuƙar tsuma zuciya da ban tausayi ga
duk wanda ya ji shi.
Bisa mamaki sai sarki Lazwar ya ga wannan damisa da
yarinyar ke zaune akan ta ita ma ƙwalla na zubowa daga
idanuwanta.
Al'amarin da ya sanya Sarki lazwar da sauran tawagarshi suka
ji sun kamu da matuƙar tausayin yarinya Shuraiba kenan shi
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
14
kanshi aljani Za'aratun-layal da ya kasance aljani sai da ƙwalla
ta zubo mashi saboda tausayi.
Sai daga can sarki Lazwar ya dubi yarinya Shuraiba ya ce "
ya ke wannan yarinya mai abin al'ajabi haƙiƙa labarin ki cike
ya ke da ban tausayi matuƙa, kuma tabbatas sarki Ladiyas ya
cika baƙin AZZALUMI, ina mai ɗaukar miki alƙawarin cewa
zan taimaka miki har sai na ga kin cika burin ki na saduwa da
mahaifiyarki da kuma ɗaukar fansa a kan sarki Ladiyas".
Ko da jin wannan batu daga bakin sarki Lazwar sai yarinya
Shuraiba ta cika da matuƙar farin ciki maral musaltuwa.
Ba tare da wani ɓata lokaci ba aka kafa sansani,nan fa
kuyangi suka shiga aikin dafa abin kalaci, bayan an kammala
ne kowa ya kimtsa cikinshi aka huta sai aka sake ɗunguma wa
aka hau bisa kan aljani Za'aratun-layal aka cigaba da tafiya
tare da yarinya Shuraiba tare da damisar ta.
Ana cikin wannan tafiya ne kwatsam! Bazato babu
tsammani sai sai a ka ga waɗansu zaratan dakarun aljanu
ɗauke da waɗansu miyagun makamai da idanu basu taɓa
ganin irin su ba, gaba ɗayan su suna shirye cikin wata irin
gagarumar shigar yaƙi mai matuƙar kwarjini daban tsoro,
adadin su ya kai dubu ɗaya da ɗoriya.
Nan fa tawagar sarki Lazwar suka firgice, wasu daga cikin su
har suna sakin fitsari a wando saboda firgici, sarki Lazwar ne
kaɗai bai razana ba shi ma a matuƙar firgice ya ke, kawai dai
ƙarfin hali ne da ƙi faɗi irin ta hamshaƙan sarakai.
Shi kan shi Za'aratun-layal duk da kasancewar aljani sai da ya
ɗimauce, domin iya tsawon rayuwarshi ko a labari bai taɓa
ganin aljanu masu kwarjini da ban tsoro tamkar su ba.
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
15
Nan fa aka fara kallon-kallo tsakanin su na tsawon daƙiƙa
latalin, sai daga can wani mummuna daga cikin aljanun wanda
da alama shi ne shugaban su ya buɗi baki cikin wata irin
kakkausar murya mai ban tsoro yace "ya ku waɗannan
bil'adama ku yi sani cewa ban zo gare ku tare da rundunar
mayaƙa na ba domin na yaƙe ku ba sai don ku ba ni yarinya
Shuraiba, mu kai ta ga sarkin mu mai girma Zammar, domin
ya yanka ta ya sana'anta jininta don ya yi wa matayen mu
maganin cutar da ke damun su ta makanta fiye da shekaru
hamsin.
Ya ku waɗannan bil'adama ku yi sani cewa
matsawar ku ka yi taurin kai wajen damƙa Shuraiba a gare
mu, ina mai tabbatar maku da cewa ɗayan ku ba zai ƙetare
daƙiƙa goma a raye ba.
Ko da jin wannan batu daga bakin shugaban dakarun aljanun
sai sarki Lazwar ya yi ƙarfin hali ya tari numfashin shi yana
mai daka mashi tsawa ya dube shi ya ce " ya ke wannan
ƙaramin ƙwaro tabbas ƙaryar ka ta sha ƙarya, kuma ka yi
ɓatan basira da ka ke tunanin cewa za ka iya raba mu da
Shuraiba.
Ina mai umartar ka da ka janye waɗannan rafkanannun
mayaƙan na ka ka koma izuwa ga matsoracin sarkin ku ga
faɗa mashi cewa bakin rijiya ba wajen wasan yaro ba ne".
Kafin sarki Lazwar ya gama rufe bakinshi jikin aljanun ya
kama tsuma yana kyarma tamkar za su ci babu.
Kawai sai su ka yi wani irin ihu da kururuwa mai firgitarwa
suka ɗauki kan su.
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
16
Ko da ganin hakan sai su sarki suka zare makaman su, ana
haɗuwa aka yamutse da azababban yaƙi mai matuƙar muni
ban tsoro da tashin hankali.
Kaico! haƙiƙa tashin hankali ba'a sa ma sa rana, kuma
duk wanda ya taɓa fita filin yaƙi shi ne ya gama ganin tashin
hankali.
Nan fa karafniyar ƙarafa gami da ihu da kururuwar dakarun
aljanu da bil'adama ta cika dodon kunne, duk sa'adda
makaman yaƙin ɓangarorin biyu suka haɗu sai ka ga walƙiya
gami da tsawa tamkar za a ke ce da ruwan sama.
Ana fara wannan arbu ne sai wani abin mamaki ya faru
domin kuwa yarinya shuraiba ta zame wa dakarun aljanun
alaƙaƙai kuma ƙadangaren bakin tulu, ya zamana cewa duk
wajen da ta sanya a gaba sai ka ga aljanun na zubewa ƙasa
matattu.
Duk wannan artabu da ake yi tsakanin su sarki Lazwar
da dakarun aljanun sarki Zammar ya gani a cikin madubin
tsafin shi, a lokacin da yake zaune a fadar koda yaga cewa an
kashe gaba ɗaya tawagar shi sai ya cika da matuƙar baƙin
cikin maral musaltuwa kuma ya takarkare ya kurma ihu.
A ɓangaren su sarki Lazwar kuwa bayan sun samu nasarar
hallaka dakarun aljanun sarki Zammar, sai kowa ya shiga
sanya magani a raunukan shi, amma aƙalla anyi asarar
dakarun yaƙi mutum ɗari biyu da ashirin.
Bayan komai ya samu dai-daituwa ne ba tare da wani ɓata
lokaci ba sai aka sake ɗunguma aka ci gaba da tafiya.
Ana fara wannan tafiya ne sai fira ta ɓarke tsakanin yarinya
Shuraiba da aljani Za'aratun-layal,
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
17
A inda Shuraiba ta dubi Za'aratun-layal tayi gyaran murya ta
ce " ya kai wannan dattijon aljani wai kuwa idan ba za ka
damu ba nayi maka wata tambaya mana.
Ko da jin wannan batu sai Za'aratun-layal ya ce " faɗi
tambayar ki ya ke Shuraiba
Shuraiba ta ce "wai kuwa a yanzu a cikin jinsin ku na
aljanu akwai wanda yafi ka yawan shekaru?
Koda jin wannan tambaya sai Za'aratun-layal ya bushe da
dariya har da kyakyatawa ya ce "a halin yanzu ni ne ɗan auta
a cikin jinsin mu na aljanu a ƙalla zan kai shekaru dubu ɗari
uku da haihuwa'' .
Cikin matuƙar mamaki shuraiba ta ce "ai kuwa in dai haka ne
jinsin aljanu sun fi kowa daɗewa a duniya.
Za'aratun-layal ya ce "kwarai kuwa zancen ki dutse".
Shuraiba ta ce "amma kuwa mai yasa kuke yiwa
bil'adama bauta alhalin kunfi su sanin halin da duniya ke ciki
Za'aratun-layal ya ce "Tabbas ke yarinya ce ba ki san komai
game da halin duniya ba amma bari na ba ki hikayar
sarauniya ABIDAT ta birnin Sin wata ƙila ki shaida batu na.
Za'aratun-layal ya yi gyaran murya sannan ya fara da cewa
BABI NA UKU
Wata mace 'yar kimanin shekaru ashirin da uku ɗauke
tsohon ciki a jikinta sanye da tufafi na fatun dabbobi riga da
wando.
RANAR MUTUWA MUKHTAR KWALISA
18
Zaune take a bisa kan wani ingarman doki baƙi, tafiya
take a cikin wani irin daji mai tattare da sarƙaƙiya,
kwazazzabai gami da duwatsu.
Kallo ɗaya za ka yiwa mata ka fahimci cewa tana cikin
mawuyacin hali.
Kaico! Tana cikin wannan hali ne sai ta ji alamun
naƙuda sun bijiro mata, kawai sai ta ja linzamin dokin ta tsaya
cak sannan ta kama ta sauko ƙasa kawai sai ta taka da ƙyar ta
durfafi kofar wani kogon dutse.
Kafin ta isa sai kawai ta yanke jiki ta faɗi ƙasa, a cikin
wannan hali ta haife abin da ke cikin ta.
Cikin matuƙar farin ciki maral-musaltuwa ta ɗauki abin da ta
haifa domin ta ga mene ne, ai kuwa sai ta ga wata santaleliyar
yarinya ce kyakkyawa ta gaban kwatance,
duk da cewar tana cikin halin laulayi, ba ta san sa'adda
hawayen farin ciki suka kwaranyo daga idanuwanta ba, a daidai wannan lokaci ne kukan jaririyar ya cika dajin baki ɗaya,
cikin hanzari ta ɗauki