hannunsa na dama, sannan ya sake yin tsalle ya haye kan dokinsa ya zabure shi shima.
Gimbiya Anisa tana ta faman artabu da wani barde, yayin da wancan barden ya kusanto...
**--- PAGE 22 ---**
...ta da takobinsa zai sauke kanta, sai takobin Sayyar ta sauka a gadon bayansa, ta hudo ta tumbinsa, nan take ya fado tim a kasa kusa da kafar dokin Anisa, hakan ya yi daidai da lokacin da barden da suke fafatawa ya yanke ta da takobinsa a cinyar hannu, zafin yankan ya shigeta, ta saki nata takobin ya fadi kasa, ya daga zai kara mata, Sayar ya yi tsalle ya hau bayan dokin barden ya rike hannayensa tare da karya su a lokaci daya, barden ya yi wata kara sannan ya fado kasa, Sayyar ya diro kansa tare da cake shi da takobi. Nan take ya sungumi Anisa ya fitar da ita daga cikin sansanin yakin, ya nufi da ita can in da wasu daga cikin mutanensu suka boya, ya mika musu ita sannan ya dawo suka ci gaba da fafatawa.
Can! Sayyar ya dubi wani sadauki ya sauke masa kai, koda mayakan suka lura da abin da ke faruwa, sai suka tsorata, ashe shugaban jagoransu ne aka kashe, kuma babban sadauki a cikinsu. Nan fa wuri ya fara lafawa, yayin da wani daga cikin su ya fara kururuwa yana shaida wa mutane,"An kashe shugaban sadaukan birnin Daulatul Sakaf." Nan da nan sai kuwa wadanda suka yi saura suka juya a guje, suka nufi hanyar...
**--- PAGE 23 ---**
...komawa birnin Daulatul Sakaf. Tuni wasu daga cikin 'yan gudun hijirar suka rufa masu baya.
** ** **
Sarki Haiman ya yi zarya, ya kara yin zarya, sai kaiwa da komowa yake yi kamar mazari, hankalinsa a tashe, ransa a bace. Abubuwa da dama sun dame shi, na farko babu 'yarsa Gimbiya Anisa, ba a ganta ba, sannan an zo mashi da labarin abin da ya wakana yayin da ya tura rundunar mayaka don kashe 'yan gudun hijira. A wannan lokaci ne Sarki Haiman ya tura ayo masa kiran Bokanya Amshadatu, kafin dan aiken ya dawo, tun labari ya zo kunnen sarki Haiman cewa ga rundunar mayaka nan zuwa birninsa. Nan da nan ya ba da umarni a yi maza a shirya rundunoni domin rusa duk wasu dakaru da yawan su ba yawa ne na misali ba, da za su zo domin jan daga da tasa rundunar. Kafin wani lokaci rundunonin yaki sun haku, birnin Daulatul Sakaf ya cika makil da mayaka, ta ko'ina idan ka duba su ne babu masaka tsinke, nan da nan suka azalzala da jiran isowar rundunar.
**--- PAGE 24 ---**
Ba a dauki lokaci ba sai ga rundunar su Sayyar ta tunkaro birnin gadan-gadan, nan fa ran sarki Haiman ya kara baci sosai.
Yayin da Bokanya Amshadatu ta iso, sai Sarki Haiman ya umarce ta da ta buga masa kasa domin gano inda 'yarsa Anisa take, nan take Bokanya Amshadatu ta fito da wasu alkalumma ta baje akan kasa, sannan ta zana wani hatimi ta share, ta sake zana wani hatimin ta sake sharewa. Sannan ta tsaya tana wasu sambatu, can sai ga wani hayaki ya bayyana a kusa da su. Can, sai ga hoton Gimbiya Anisa ana saka mata magani a raunin da aka ji mata. Nan take Bokanya Amshadatu ta rinka nuna Sayyar tana fadin "Shi ne, shi ne, ga shi nan, shi ne...."
"Shi ne wa.?" Sarki Haiman ya daka mata tsawa.
"Sa.......yyar.......yar..........yar." Muryarta na rawa take ambatar sunan.
"Sayyar!?" Sarki Haiman ya tambaya cike da mamaki.
"Shakka babu shi ne, zai kwace maka mulki idan ba ka dauki mataki ba yanzun nan." Ta sanar da shi.
**--- PAGE 25 ---**
"Maza ki sa aka mashi." Ya umarce ta.
Nan take ta fito da wata buta ta bakin karfe, ta zazzage wani bakin gawayi a cikinta, sannan ta kalli rana tana wasu sambatu tare da kiran sunan wani Hadimin Aljani, kafin wani lokaci sai ga wani katon aljani ya bayyana, misalta kamanninsa ba karamin tsoratar da makaranta zai yi ba.
Nan take ya yi wata girgiza, sai ga wasu bakaken aljanu suna fitowa daga cikinsa, ya yi wata hamma iska mai karfi ta fito, yayin da ta tunkari inda rundunar Musulmin ke fitowa, nan da nan iskar ta dinga fisge itatuwa tana awon gaba dasu, gidaje kuwa suka dinga bajewa, kasa ta dinga tashi tana barin hako kawai.
"Maza aka wo min Sayyar nan in da nake yanzu." Bokanya Amshadatu ta bukata.
A can kuma yayin da rundunar su Sayyar din take zuwa, sai suka hango wannan iskar ta doso su, nan take sai ya karanto wasu addu'o'i ya karbi ruwa ya kuskure a bakinsa ya furzo, sai nan take iskar nan ta juya ta dawo baya, yayin da su Bokanya Amshadatu suka ga haka, sai hankalinsu ya tashi, nan fa suka fara gudun...
**--- PAGE 26 ---**
...neman tsira, amma kafin wani lokaci tun iskar tazo ta yi awon gaba da Bokanya Amshadatu tare da wasu daga cikin dakarun Sarki Haiman.
Haka su Sayyar suka shigo cikin birnin suka dinga dauki-ba-da-di tsakaninsu da rundunar makafirta.
Kwana biyu ana fafatawa tsakanin su, inda a karshe Sayyar ya shiga cikin kurkukun tare da wasu dakaru 'yan uwansa cikin wadanda suka yi gudun hijira, nan ya samu an sakawa mahaifiyarsa macizai suna kokarin sararta, nan fa suka dauke kawunan macizan, suka kwance ta suka fito da ita. Har a wannan lokacin ita kanta ba ta gane Sayyar danta bane, sai da aka suka fito tsakiyar filin gidan, in da anan wasu dakarun sarki Haiman suka yi masu kawanya. Can sai ga Bokanya Amshadatu itama ta faso gini ta shigo, shima sarki Haiman da wasu dakaru suka bayyana a wurin. Sarki Haiman ya kyalkyale da dariya tare da nuna Sayyar yana mai dakawa wasu dakaru tsawa da yin umarni gare su, cewa su kama su.
Nan fa suka yo kan shi, Sayyar ya dinga saransu da takobinsa ba ji ba gani, duk in da ya kai sara sai kaga an fadi, mutum biyu suka...
**--- PAGE 27 ---**
...kange mahaifiyarsa, yayin da wasu suka shiga suna taimaka masa, ita kuwa Anisa wani aljani aka sa ya damke ta, nan take Sarki ya sa aka je aka jefa ta a wani daki aka kulle bayan an daure ta da sarka.
Kafin wani lokaci sai dakarun dake wurin suka wanzu a kasa, wasu sun mutu wasu suna mirgineneniya a kasa suna magagin mutuwa.
Bokanya Amshadatu ta yi wata kururuwa, ta buga kafarta a kasa, ta kira wani suna, yayin da ta yake baki ta fara sakin wani bakin hayaki, can sai ga wani gabjejen bakin basamudan aljani ya bayyana, ta nuna Sayyar ta ce ya afka masa. Nan da nan Aljanin nan ya nufi Sayyar da wata irin guduma narkekeya a hannunsa, ga wani takobi rike a hannunsa bai fitar da ita daga cikin gidanta. Ya dauki Sayyar da hannu daya, ya cilla shi sama, ya fado kasa ya mirgina sau uku, sarki Haiman ya yi tafi gami da dariyar mugunta, sannan Sayyar ya yi karfin hali ya tashi, yayin da aljanin nan ya sake nufo shi, ya dauko takobinsa ya wurga masa ta cake shi, amma yaga ko gizau bai yo ba, ya zo ya sake daga shi ya yi jifa da shi, Sayyar ya fadi gindin...
**--- PAGE 28 ---**
...dabinon nan in da har yanzu takobin da Sarki Haidar mahaifinsa ya soke tana nan a jiki.
Aljanin nan ya nufo Sayyar gadan-gadan, da ya kusanto shi sai ya zare takobinsa da nufin yana zuwa zai raba Sayyar gida biyu, hankalin Sayyar ya tashi, ya duba yaga babu wani makami a kusa da shi, nan da nan sai ya mike ya isa jikin takobin nan da ke kafe jikin bishiyar dabino, ya kama zai zaro ta, yana kamawa kuwa ya fara ja sai ta taho tare da wani haske matsananci. Hasken yana kaiwa jikin aljanin nan, sai ya fara kara yana komawa da baya, ganin haka sai Sayyar ya ci gaba da zaro takobin hannunsa na kyarma, takobin na jijjiga shi. Nan fa duk sai aka tsaya ana kallon Sayyar cike da mamaki. A daidai lokacin ne mutanen gari suka yo caa! Suka shigo tsakiyar makeken filin gidan. Ganin abin da ke wakana ne ya sa kowa ya ja ya tsaya, har lokacin da Sayyar ya zare wannan takobin a jikin bishiyar dabinon nan, yana zare ta ya yo kan aljanin nan gadan-gadan, nan take sai ga aljanin nan ya narke ya zama ruwa don tsananin azaba.
Mutane suka yi kabbara tare da nufo Sayyar suna murna. Hakan ya yi daidai da...
**--- PAGE 29 ---**
...lokacin da Gimbiya Anisa ta fito a guje, sarkar dake jikin ta, ta kwance babu komai, wasu daga cikin mayakan suka shigo da daurarro wadanda aka ribace su daga rundunar sarki Haiman.
Nan fa murna ta kama mutane, aka kama sarki Haiman da sarkoki tare da Bokanya Amshadatu, da wazirin sarki Haiman, da sauran wadanda suke tare da shi.
A daidai lokacin ne Amar ya shigo bisa wani ingarman doki yana haki tare da kura wa Gimbiya Anisa ido.
Yasan dai ta fi karfinsa, dole kuma ya hakura da cewa zai same ta.
Ta rogo da gudu ta tsaya gaban Sayyar tare da kura masa idanu, hakan ya yi daidai da zaburowar mutane suka daga shi sama ana murna.
Mulkin zalunci ya karfe a: BIRNIN DAULATUL-SAKAF, domin Sayyar zai karbi kujerarsa.
TAMMAT
Naku: IBN SALIS.. (NAFS!)
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels