An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
KAMBUN KARFE
NAFI'U SALISU IBN SALIS
SALIS
**--- PAGE 2 ---**
KAMBU KARFE - 2
ana gaba suna biye da ita cikin takun kasaita da nuna akwai mulki, yayin da kuyanginta suke take mata baya.
Mutane suna yin gaisuwa gare ta cikin girmamawa, yayin da kuma suke bata hanya da gaggawa, duk da cewa ba kan wani abu take tafe ba, balle ace ko suna jin tsoron a bi ta kansu ne a take su, wannan ya nuna tsananin girmamawar da suke yi a gare ta ya wuce wasa.
Gimbiya Anisa kenan.
Tana rike da dan kyakkyawan tsuntsunta, yayin da ta rungume shi a jikinta, kuma hankalinta ya fi karkata izuwa gare shi. Iskar dake kadawa a cikin yammacin, yana busa ta tare da kuyanginta, yayin da hakan ya wanzar masu da nishadi baki dayansu.
Sayyar ya wanzu cikin dan kyakkyawan kejin da Gimbiya Anisa ta mallaka wajen 'yar'uwarta tun tana da rai, wanda a yanzu ta shafe shekaru da yawa da mutuwa, sakamakon ambaliyar ruwa a kasar da take aure.
**--- PAGE 3 ---**
Sayyar, kuma wanda a yanzu yake a matsayin tsuntsu, shi ne abu mafi girman al'amari da ya jefa so da kauna a cikin zuciyar Gimbiya Anisa, ta ji tun da take a rayuwarta ba ta taba son wani abu ba kamar tsuntsun da ta sa a cikin kejin nata ba.
Da farko ta saka kejin ne a cikin wani dan madaidaicin daki, yayin da take kula da shi wajen ba shi abinci da abin sha, haka nan kuma ta ji dadin yadda tsuntsun yake jin duk abin da take fada, duk da cewa bai kasance Aku ba.
Daga baya sai ta dauke shi tare da kejin ta maida dakin kwananta, ta rataye shi kusa da gadonta, kamar yadda ake rataye kwarya akan ragaya.
Ya zamo shi ne abin da ke faranta mata rai yayin da take bakin ciki, ya zamo shi ne abin da ke debe mata kewa, ya zamo shi ne abu na farko wanda idan ta yi tozali da shi take jin nutsuwa a cikin zuciyarta. So da kaunar da take yi wa tsuntsun nan, ya sa ta saka mishi suna, sunan da take ganin ya dace matukar dacewa da shi.
NURUN KALBI (Hasken zuciya).
**--- PAGE 4 ---**
BABI NA BIYAR
Amar yana zaune a bakin gadon barcinsa, ya yi shiru tare da daga kanshi sama yana tunanin labarin da Abusamar Dattijon Makerin nan ma'abocin kira, sannu a hankali abubuwan da ya sanar da shi suke wanzuwa cikin kokon zuciyarsa.
Yana matukar son ya mallaki kambun nan na gidan sarauta, amma ta yaya za a yi ya iya cire wannan takobin dake jikin bishiyar dabinon can da Marigayi Sarki Haidar ya soka a jiki, ya kuma tabbatar wa mutanensa cewar, babu wanda zai iya cire ta sai dansa Sayyar?
Idan haka ne kuwa, to lallai zai yi wuya ya iya mallakar wannan kambu, ballantana har ya sa ran zai iya mallakar Gimbiya Anisa 'yar Sarki Haiman.
Ya yi ajiyar zuciya.
Bayan wasu 'yan shekaru da murkushe dakarun Sarki Haiman da rundunar Sarki Haidar suka yi, sai rashin lafiya mai tsananin karfi ta wanzu akan Sarki Haidar, a yayin da hakan ke faruwa, sai ga rundunar Sarki Haiman babu zato babu tsammani, suka afka cikin birnin Sarki Haidar, suka shiga kashe rayukan Jama'a.
Kafin wani lokaci tuni sun...
**--- PAGE 5 ---**
...hallaka mutane da dama, suka samu damar dauke Aisamatu suka tafi da ita gaban sarki Haiman bayan sun saka mata sarka, yayin da suka baro kasar ana dauki-ba-da-di da mayakan sarki Haidar.
Duk da cewa sun yi mamayar ba zata, amma hakan bai hana jama'ar Sarki Haidar yin nasarar daukar fansa ba. Sai dai tuni sun ci karfin su, domin a wannan lokaci akwai dakarun da suke tsaron Sarki Haidar..." A hankali ya ke tuna irin labarin da Abusamar ya ba shi, dangane da Sarki Haidar. Amar ya sake jin ajiyar zuciya a karo na biyu, sannan ya ci gaba da tunanin labarin da Abusamar din ya ba shi.
".......Dakarun Sarki Haiman suka mamaye kasar Sarki Haidar, yayin da suka fuskanci sun ci galaba akan musulmi, sai suka yi aike ga Sarki Haiman, in da nan da nan ya taho tare da wani ayarin na rundunar mayaka, suka wanzu cikin birnin Daulatul Sakaf, in da suka samu Sarki Haidar rai ya yi halinsa.
Nan take suka kama sauran jama'arsa suka maida su bayi, wasu daga cikin su kuma suka hallaka ta hanyar kisan gillar da Sarki Haiman ya sa aka yi masu.
**--- PAGE 6 ---**
Bayan shekara daya da cinye kasar da yaki, sai Sarki Haiman ya sa aka rushe birnin baki daya, aka yi sababbin gine-gine, ya kuma kafa masarautarsa a nan, shi ne ya sa wa birnin suna, Daulatul Sakaf.
Daga nan ya ci gaba da mulkinsa na zalunci, yayin da talakawa suke jin tsoronsa, haka nan babu wanda yake raga wa maza da mata.
Aisamatu matar Sarki Haidar kuwa, tana kurkuku a tsare daure da sarka.
Sarki Haiman ya sa wata Bokanyarsa, wadda ta kasance tsohuwar matsafiya ce, ta yi masa bincike game da yadda za'a yi a cire wannan takobi daga jikin itaciyar dabinon nan, yayin da ta yi masa binciken cikin ilimin Bokancinta, sai ta shaida masa cewa, lallai sai ya mallaki wani kambu na bakin karfe.
Yayin da ya ji wannan batu, sai ya tambaye ta.
"Ya ke Amshadatu, a ina wannan kambun bakin karfe yake cikin fadin duniyar nan.?"
Bokanya Amshadatu, ta girgiza kai sannan ta yi murmushi. "Shi wannan kambu na bakin karfe, ya na can karkashin wani bakin dutse, yamma da kasar Spain, daga nan zuwa can tafiyar shekara daya ce akan ingarman Doki...
**--- PAGE 7 ---**
...amma ga matashin Aljani kuwa tafiyar sa'a guda ce."
Yayin da Sarki Haimana ya ji haka, sai ya ce, "To na umarce ki, da ki yi gaggawa wajen saka daya daga cikin hadimanki domin su dauko wannan kambu."
"Kar ka samu damuwa ya shugabana, lallai zan cika umarninka, rana ta baka nasara."
Yayin da Bokanya ta yi bankwana da Sarki, nan da nan ta fita zuwa turakar tsafinta, ta kuma umarci wani hadimin aljaninta da ya je ya dauko wannan kambu na bakin karfe.
Washe gari sai ga kambun bakin karfen nan an kawo wa Sarki, Sarki Haiman ya yi murmushi tare da kallon kambun, sannan ya jinjina wa Bokanya Amshadatu.
"Ya ke wannan ma'abociyar sanin ilimin tsafi, maza bani labarin yadda mutum zai yi amfani dashi kafin ya samu damar cire wannan takobi a jikin itaciyar dabinon can."
Bokanya Amshadatu ta kyalkyale da dariya, sannan ta kalli Sarki Haiman ta na mai girgiza kai bayan ta dakata da dariyar.
**--- PAGE 8 ---**
"Wannan al'amari boyayye, domin babu wanda yasan wannan sirri sai Sarki Haidar, kuma ya riga ya mutu." Ta sanar da shi.
Shima yanzu jinjina kai ya yi. "Yanzu ina mafita.?" Ya tambaye ta.
"Mafita daya, sai dai ka bani nan da wani dan lokaci domin in ci gaba da yin bincike game da hakan, amma idan ba haka ba, ban san akwai wata mafita ba tukun, sai abin da alkalumma suka nuna min."
"Je ki, na baki lokacin duk da ki ka ga ya dace da samun mafita." In ji Sarki Haiman.
Daga nan suka rabu akan haka.
Amar ya sake yin ajiyar zuciya, domin da izuwa yanzu ya fahimci al'amarin kambun bakin karfen nan na da girma, sai dai kuma bai san abin da Kakansa yake nufi da ya umarce shi da cewa, yaje gurin Abusamar ya kera masa irin wannan kambu ya kawo masa shi.
Ya tashi cikin sanyin jiki, sannan ya nufi wani bangare na dakin nasa, ya bude wani katon akwatu na bakin karfe, ya dauko kambun Karfen da Dattijo Abusamar ya kera masa, sannan ya dauko hoton wancan kambu na sihiri...
**--- PAGE 9 ---**
...ya kare musu kallo gaba daya, yaga komai nasu iri daya ne.
Ya yi wani murmushi na karfin hali, sannan ya kudurce a zuciyarsa abu daya ne ya rage masa yanzu, zuwa wajen Kakansa da kambun.
**
Aisamatu daure da sarka a cikin kurkuku, yayin da take cikin wani mawuyacin hali na tsanani, alamun manyanta ya fara bayyana a gare ta.
Babu abin da ya fi damunta, face abu biyu, na farko rashin maigidanta, sannan na biyu rashin danta Sayyar, tare da bakin cikin halin da take ciki a yanzu, na kaskanci da cin mutunci, cin zarafi da tozartawa.
Kanta a duke tana zubar da hawaye, yayin da abin duniya ya sha mata kai, ji take yi mutuwa ta fi mata dadi a wannan lokaci, sai dai lokaci-lokaci takan yawaita ambaton Allah; domin ya kawo mata agaji game da halin da ta kasance.
Takun sawun da ta jiyo a wannan lokaci, shi ya yi sanadiyar barin tunanin da take yi, ta natsu tana sauraron tafiyar da ake yi.
Wasu dakaru ne su biyu sanye da wasu jibga-jibgan...
**--- PAGE 10 ---**
...riguna na gashi, suna rataye da manyan takubba a kafadunsu, fuskokinsu babu alamar annuri, kai ka ce wasu ifritai ne.
Dakarun da suke gadin kurkukun, tuni sun mike domin girmamawa gare su, yayin da suka iso wurin sai suka yi gaisuwa gare su cikin girmamawa.
Nan suka ja suka tsaya suna kallon Aisamatu dake daure cikin sarkoki, tare da mika wa masu tsaronta wata doguwar takarda.
Yayin da daya daga cikin su ya karanta, jikinsa na rawa ya umarci dayan da ya bude ya fito da ita, a sakamakon ganin sakon da ya yi a rubuce daga Sarki Haiman, cewa a fito da ita za aje a tsire ta.
"Aisamatu." Cikin tsawa wani ya daka mata tsawa, yayin da ta dago kanta suka hada ido, tuni an bude gangamemiyar kofar wadda aka yi ta da wani murtukeken rodi.
Nan take suka tasa keyarta gaba cikin sarka hannu da kafa da wuya zuwa in da za'a tsire ta kamar yadda Sarki Haiman ya yi umarni, wai rana ce abar bautawar su ta umarci a kashe ta, idan ba haka ba zata hana masu cikar burinsu game da takobin Sarki Haidar.
**--- PAGE 11 ---**
Gimbiya Anisa ta shigo cikin dakinta, tana sanye da rigar alfarma irin ta 'ya'yan Sarakuna ma'abota tarin dukiya da sarauta, gashin kanta ya warwatsu bisa kafadarta, fuskarta tana kyalkyali cikin walwala, kamshin turaren almiski yana tashi a jikinta.
Kai tsaye ta nufi in da (Nurul kalbi) yake kwance cikin keji, kasancewar yau ba ta fita da shi ba, amma yanzu da take kokarin tafiya filin da za'a tsire Aisamatu, dole ne ta tafi da abin kaunarta don shima ya ba idonsa abinci.
Gimbiya Anisa ta ja ta tsaya cike da mamaki, hankalinta ya tashi, mamaki mai tsanani ya bayyana a gare ta sakamakon ganin tsuntsun nata yana kuka. Ta isa gare shi sosai tana mai razana da yanayin da tazo ta same shi a ciki.
"Nurul kalbi me ya faru da kai ne.?" Ta tambaye shi cike da rudewa.
Ya kada fukafukinsa daya, sannan ya yi wani kuka tare da ce da ita.
"Ya abar kaunata, kukan nan da kika same ni ina yi, ba komai bane ya sa nake yinsa, sai wani babban rashi da kike shirin yi yanzun nan...
**--- PAGE 12 ---**
...rashin da idan kika yi shi, ba zaki samu kamar shi ba."
Cikin gaggawa ta ce da shi.
"Maza ka sanar da ni, wanne rashi ne zan yi.?" Ta kura masa idanu.
"Idan kika bari aka tsire matar nan da aka fito yanzu a cikin kurkuku, to lallai zaki rasa ni, sannan kuma rayuwarki zata shiga cikin wani hatsari. Nasan idan ba yanzu da zan sanar da ke wani sirri ba, to baki taba sanin cewa ni garkuwar rayuwarki ba ne..." Kafin ya gama rufe baki, tuni ta juya da sauri ta nufi hanyar fita waje.
Wani bakin kato murjeje ma'abocin manyan kafadu, yana tsaye gaban Aisamatu, yayin da ita kuma kanta ke duke, an daure ta jikin wasu manyan itatuwa da ke kafe, yayin da wani daga gefe yake karanto wasu abubuwa kamar mai karanto laifin mutumin da aka yi kara a kotu. Yana rufe baki sai kuwa bakin katon nan ya daga wani sharbeben takobi zai sauke wa Aisamatu kai, nan take sai ji ya yi an rike takobin da majaujawa, kafin ya ankara sai ga Gimbiya Anisa bisa Doki ta bayyana a...
**--- PAGE 13 ---**
...gabansu.
"Kada ka aikata niyyar ka akanta, domin akwai sauran shan ruwanta a gaba." Gimbiya Anisa ta fada a daidai lokacin da ta tsaya da Dokin.
Kowa da ke wurin ya bi ta da kallo cike da mamaki, nan take ta daure fuska tare da direwa daga bisa Dokin, ba tare da ta tsaya wani dogon bayani ba, ta daka masu tsawa.
"Maza ku kwance ta daga nan, ku maida ita cikin kurkuku." In ji Gimbiya Anisa.
Kafin ta sake wata magana, tuni suka kwance ta suna kokarin juyawa da ita.
**--- PAGE 14 ---**
Gimbiya Anisa ta yi ajiyar zuciya, sannan ta sa hannu ta tura kofar tare da sa kuba ta kulle, ta dawo bakin gadonta ta tsaya tare da kai kallonta in da Nurul kalbi yake. Ta sake cire wannan zoben, sai ga kyakkyawan saurayin nan ma'abocin kyawun sura ya bayyana kamar dazu. Kyawun sura da halitta irin na saurayin, ya matukar rudar da Gimbiya Anisa, nan take ta ji wani irin shaukin so da kaunarsa ya sake mamaye mata gurbin zuciya, ta zaune sosai a gefen gadon nata tana mai binsa da idanu.
"Ka ba ni labari, mutum ne kai ko Aljan.?" Ta tambaye shi.
"Mutum ne kamar ki." Ya fadi haka kawai.
"Sunanka fa.?"
"Sayyar bin Haidar.?" Ya bata amsa.
"Ya akai ka samu kanka a wannan matsayin.?"
"Labari ne mai tsawo." Ya ce da ita.
Ta girgiza kai tare da mikewa tsaye ta ja baya cikin taku biyu, sannan ta juya baya tare da rufe idanunta.
Sayyar ya mike tsaye a hankali yana kallon dirinta.
"Anisa," Ya kira sunanta.
**--- PAGE 15 ---**
"Nurul kalbi." Ta fada cikin sanyi murya.
"Ki juyo gare ni, sannan ki tabbar min da cewa har yanzu kina kaunata a cikin zuciyarki, idan kika yi haka, zan samar miki 'yanci a cikin Addini mai girma, kuma mafi daukaka da daraja, sannan ki samu rabauta a wajen Sarkin da shi kadai ne abin bauta da gaskiya."
"Anisa, juyo ki fuskanci abin da kika dade kina kula da shi, ki dade kina tarairayarshi, ki dade kina begensa, ki wanzu cikin tsantsar so da kauna, idan har kin bada gaskiya da abin bautarki." Sayyar na rufe baki Anisa ta juyo, idanunta cike da kwalla. Yayin da suka hada ido sai hawaye ya fara zubo mata a fuska.
"Me yasa kike kuka ya abar begena.?" Ya tambaye ta.
"Hakika a tare da kai akwai al'amari mai girma, ban taba son wani abu fiye da sonka ba, ban taba kula da wani abu ba, fiye da kai ba. Kai kadai ne abin da zuciyata ta fi kusanci da shi."
"Har addininki.?" Ya tambaye ta.
"Na tabbatar maka da haka." Ta amsa.
Ya girgiza kai.
"To ki gode wa Allah wanda ya saka miki kaunata a cikin zuciyarki, domin yanzu za ki...
**--- PAGE 16 ---**
...fahimci ba Allahn da ya halicci sama da kasa kike yi wa bauta ba, domin kuwa shi kadai ne za ki fi kusanci da shi fiye da komai ki wanzu cikin karama. Anisa yanzu ina so ki yi min alkawari uku, na farko dai ki boye sirrina, ki kuma yi min alkawari za ki kubutar dani da mahaifiyata Aisamatu, sannan ki amince za ki bautar abin da ku ke bautawa. Idan kika yi haka za ki fahimci rayuwar da ki ka yi a baya, tamkar rayuwa ce irin ta dabbobi, sai bayan mahaifinki ya fahimci cewa, mulkin da yake yi ba na shi ba ne, to sannan za ki fahimci dukkan abin da na bayyana miki. Yanzu ki san yanda za ki yi ki fitar da ni daga cikin birnin nan domin cimma burina."
Gimbiya Anisa ta kalle shi cike da mutuwar jiki.
"Kin yarda da duk abin da na fada.?" Ya tambaye ta.
"Na amince, amma ta yaya zan iya fitar da kai daga cikin birnin nan, bayan ina sane da irin matakan tsaron da suke ciki.?"
"Kar ki damu, ina da mafita."
"Menene mafitar ka.?" Ta tambaye shi.
"Matso ki ji in sanar da ke."
**--- PAGE 17 ---**
Ta matso kusa da shi kamar yadda ya umarce ta, ya fada mata abin da yake ganin shi ne mafita, ta kalle shi tare da yin wani murmushin karfin hali, shima ya yi mata murmushin. Sannan ta bukaci ya sanar da ita abin da ya haddasa masa zama tsuntsu. Nan take ya nuna mata bai san komai ba, sai dai ko mahaifiyarsa.
"To ya kai ka ce min labari ne mai tsawo.?" Ta tambaye shi.
"Don kawai na kawar da maganar, domin za ta iya hana mu yi wadda ta fita muhimmanci." Ya sanar da ita.
"Na gamsu." Ta amsa.
** **
Mutum dubu biyar da dari hudu da tamanin ne, suka yo gudun hijira daga birnin Daulatu Sakaf, da niyyar zuwa birnin Hubar kasar Sarki Ushaibat tare da karfafa zuciyoyinsu yin imani da Allah da Manzonsa (S.A.W) wato idan sun wanzu a kasar Hubar za su karbi addinin musulunci, don haka a yanzu da suke tafe wasu a kasa, wasu a rakumma, wasu a dawakai, wasu kuma ana dauke dasu bisa dawakai da rakuma,
**--- PAGE 18 ---**
tsofaffi da marasa lafiya kenan da ba za su iya tafiya ba. Suna cikin tafiya a cikin sahara, sai ga rundunar mayaka daga bayansu, Sarki Haiman ne ya turo a kashe su baki daya. Nan da nan kura ta turnuke ta yi sama, da suka ga haka sai suka kasu kashi uku, kashi daya suka tsare dukiyoyinsu, kashi na biyu suka tsare marasa lafiya, yayin da kashi na uku suka tsaya domin su ja daga da rundunar sarki Haiman, domin su dama sun riga sun yi niyyar bada gaskiya izuwa addinin Musulunci, don haka yanzu zasu tunkari shahada.
Yayin da rundunar mayakan sarki Haiman suka tunkaro ma'abota yin hijira, sai wasu daga cikinsu suka kara saboda ganin yawan rundunar, domin kuwa duk yawan su rundunar ta linka su, kuma babu tsofaffi a cikinsu. A yayin da jagoransu, wanda shi ne ja gaba wajen yin wannan hijira ya fuskanci halin da wasu suka shiga na karayar zuciya, sai ya fara kokarin karfafa masu gwiwa. Nan da nan suka dan samu natsuwa, to a wannan lokaci ne fa Sayyar ya bayyana akan wani Ingarman doki tare da Gimbiya Anisa, itama tana bayansa, ta yi shiga irin ta maza sadaukai, babu wanda zai gane ta...
**--- PAGE 19 ---**
...daga cikin mutanen Sarki Haiman, itama tana haye kan dokinta. Suna zuwa suka ja linzaman dawakan nasu suka tsaya, nan take Sayyar ya yi kabbar domin su fahimci cewa Musulmi ne, suna jin ya yi kabbar sai suka amsa masa tare da bin shi da kallo, nan take ya fara magana da cewa.
"Ya ku ma'abota Imani da Allah Ubangijin talikai, ku wanzu cikin natsuwa da karfin gwiwa nasara tana gare ku ma'abota hijira, kada yawan rundunar makafirta ta tsorata ku, lallai ku sani cewa yawan nan nasu na kwarjini ne, idan dai hijirar ku domin Allah da Annabinsa ce, to ku shirya tarar rundunar ma'abota wanzuwa a gare ku domin yin shahada."
Duk kowa ya bi shi da kallo cikin rashin sanin ko wanene shi da yake magana, Anisa ce dai kawai tasan ko shi wanene, amma baya ga ita ba su san ko wanene ba su.
"Ya ku ma'abota Imani, shin zaku zamo masu mika wuya ne ga wadanda suke kaskantattu a wajen ku? To ku yi sani cewa, Allahn da ku kayo hijira dominsa yana tare da ku, sai dai idan ba dominsa ku ka yi wannan...
**--- PAGE 20 ---**
...hijira ba. Da sannu za ku zamo masu rinjaye akan kafurai."
Nan da nan suka yi sahu-sahu, suka yi shirin yaki, wasu suka tsugguna a gaba suka haka kibiyoyinsu, wasu suka tsaya daga baya rike da masu, wasu suka tsaya a bayan masu rike da mashin, su kuma suna haye bisa dawakai rike da takubba. Jagoran rundunar gudun hijirar, wanda yake dama can Sadauki ne, ya ci gaba da basu umarnin yadda za su fara afka masu da makamai, yayin da shi kuma Sayyar tare da Gimbiya Anisa suna tare da wasu majiya karfin sadaukai daga cikin mahaya dawakai.
Suna cikin wannan shiri, sai ga rundunar Sarki Haiman sun iso dab da su, nan take suka fara yi masu ruwan kibbau, sai dai kaga barade suna kara suna fadowa daga kan dawakansu, su kuwa 'yan gudun hijirar sai sakar musu ruwan kibbau suke yi. Da yake akwai sauran 'yar tazara tsakaninsu, kafin su cimma su, sun yi masu barna da yawa. Ma su harba kibiya suka koma baya yayin da suka iso gare su, ma su mashi suka shige su, nan fa wuri ya hargitse, duk in da ka duba jini ne ke fallatsa kamar feshin ruwa a lokacin da ake tafka ruwan sama. Kura ta tashi...
**--- PAGE 21 ---**
...sama ta fara rufe mayaka, suma su Sayyar suka shigo aka dinga fafatawa da mazaje, duk in da Sayyar da Anisa suka dosa, sai dai ka ga kawunan barade na fadowa kasa, sannan gangar jiki ta biyo baya.
Yaki ya kai yaki, mazaje sun sha kashi, sun wanzu cikin gumurzu da dauki-ba-da-di, yayin da dawakai ke tsalle suna faduwa suna karairayewa, haka nan kukan su ya cika wajen karar takubba da sukekeniya da bugayya sun cika wurin, kura ta turku ta yi sama.
Wani barde da ya lura da Anisa, yadda take kashe mutane, sai ya sako dokinsa a sukwane ya tazo da takobinsa tsirara da nufin tsinke mata kai, Sayyar ya hango shi yayin da suke cikin fafatawa da wani katon barde, da Sayyar ya yi kokarin rabuwa da shi don kawu mata dauki, sai kuwa wancan barden ya buge masa takobi ya yi sama, ganin haka sai Sayyar ya yi tsalle ya diro kasa ya na mai bi takobinsa da kallo yayin da ta yo kasa, tana zuwa ya cafke da