An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
ASHE MATAR AURECE.....1
Rayuwa kenan ni kaina
bansantaba, bansan
daga ina ta fitoba, ban
taba ganin taba, bansan
yar wace ƙabila bace,
bansan halayenta ba,
Amma naji sonta ya
Kamani lokaci guda har
na ɗaukarwa kaina
Alƙawarin Sai na Aureta
kota halin ƙaƙa koda
Duk abinda natara zasu
ƙare Koda rayuwatace
Zan iya sadaukarwa
sabi da in Aureta koda
Aranar da aka ɗaura
Aure Zan Mutu...
Tsaye nake abakin titin
dake
unguwarmu wanda ya
ratsa daga konannan gidan mai zuwa
cikin unguwar bello
dake cikin Dorayi kano
kowa yana ta hada-
hadar kasuwancinsa...
Idan kayi duba izuwa
gareta hakika Allah
yacika kamala da duk
wani Dan'adam zai gani
yaji ya yaba kuma ya
kyasa Allah ya azurta
wannan baiwa tasa da
abubuwa kamar haka
ga kyau ga kamala gata
da kwarjini hade da
daukar hankalin duk
wani ɗa Namiji da
sukayi Arba dashi dole
ta sace xuciyarsa gata
kuma da farin jini
sannan bazaka iya
banbance shin tafiya
take da kafafuwanta
ko kuwa injin ɗin tafiya
ta hau yake yawo da
ita...?
Sannan abin da zai
birgeka da ita shine
Allah ya azurtata da
idanuwa dara-dara koda
cikin duhun darene zaka
iya gane idanunta idan
ta budesu
wani abin haushi da
baƙin ciki shine tare
naganta da wani saurayi
dan kimanin shekara 30
Baƙi mummuna ...
Yayinda sukazo giftawa
ta gabanmu gaba daya
ilahirin mutanan dake
gefan titin kamar su yaya Abbati da
amininsa Ibrahim suraj da wani dattijo
mai suna salisy da malan sagiru dukkan
ninsu
hankalinsu ya karkata
zuwa gareta kai harma da wasu
matan ...
kai nima kaina ba abarni
abayaba wajan kallon
kirar fatar kyawun
halittar dirin da Allah
yayiwa wannan baiwara
Allah ba
yayinda sukazo suka
gifta tare da
Dan'saurayin nan gani
nayi jama'a baki ɗaya
suka bita da kallo kai ka
rantse kauyawane
amma ina sam ba haka
bane ko kaine sai taja
hankalinka wajan kallon
dirin kyawun zubar
gadon halittar da Allah
yaiwa wannan baiwa
tasa
Kubiyoni kuji yadda ta kaya yin comment
naku shine zai bani kwarin gwiwar
cigabaASHE MATAR AURECE........2
...........haka dai tsaya tsawan lokaci, kuma naci
alwashin bazan bar bakin titinba har senaga abinda
ya turewa BUZU nadi.
A wannan rana ko kasuwa banjeba ina tsaye sai
naga dawowar wannan
baiwar Allah koda kuwa zanyi kwana in wuni ne!
domin ta shiga raina....
Cikin daƙiƙu kaɗan misalin 5:00 na yamma kuwa
nahangota tana
tafe ita kaɗai lokacin, anan nacika da farin ciki
mara misaltuwa, koda ta
kusan isowa ƙofar layin mu zuciyata ta fara
ayyanamin na bita kawai, banyi nawaba kuwa
wayan amsa bukatar zuciyata,
nayi niyar binta amma dana juya sai na hango
wannan ɗan mummunan saurayin yana sauri ashe
ya tsaya siyayya ne abaya...
Saboda tsananin Baƙin ciki kawai senaji duk duniya
babu wanda natsana lokaci ɗaya irin wannan
mummunan saurayi da suke tare da wannan
kyaikyawar halitta...
Nan naga yafara kokarin yimata magana, ga
mamaki sai tattausan
murmushi kawai takeyi batare da naga tana bashi
amsaba, hannusa na dama riƙe yake da waya
BLACKBERRY kirar zamani, aikuwa nima tun daga
ranar tuni nasamu abinyi, dan saida na shafe
kusan kwana 26 ina saita lokacin wuce
warsu dana dawowarsu, amma ina duk tsawan
wannan lokaci. shiru kakeji ..
Wata ranar Asabar da yamma na fito kamar yadda
na saba zama a ƙofar layin mu dan jiran
tsammanin sake ganin fuska ma'abociyar haske da
walwala, can Da misalin ƙarfe 5:23 na yamma
zakara ya bani sa'a...
Masu sauraro tabbas idan natswa wassafa muku
halitar wannan baiwar Allah zakuyi mamaki domin
kuwa bazan iya tantace mutumce ko aljanace ba,
"wai shin wacece wannan?" Tambayar da nakasa
baiwa kaina Amsa kenan, Shawo
kwanan danaga sunyi shine yayi
matuƙar jefani cikin yanayi guda 2.
Na farko na kasance mai tsananin Farin ciki da
sake ganin wannan baiwar Allah wadda Rayuwata
tashiga yanayin Ruɗani dominta!
Na biyu kuma na faɗa cikin yanayin ƙunci da baƙin
cikin sake ganinta danayi da wannan Saurayin da
suka wuce Ranar farko dana fara yin Tozali da
ita...
"Shin wannan meye alakarsa da itane" wannan
tambayar ce tasake fadomin cikin zuciya...Tabbas
awannan lokacin na ƙara jin tsanar wannan
saurayin ya ƙara shiga
Cikin zuciyata, duk da. Cewa bansan dangantakar
su da itaba, Yauma kamar ranar sai zuba mata
surutu
yakeyi amma ita banga tana mayar masa da amsa
ba. Kamar kullum murmushi kaɗai naga tanayi yau
ma, da alamun tana matuƙa jin daɗin zantukan da
yakeyi mata....
Ganin haka danayi ya ƙara jefani cikin matsanancin
kishi wanda naji kamar inje in Haushi da duka, to
amma matsalar anan itace bansan menene
matsayinsa awajenta ba, kada naje na aikata aikin
da nasani, wanda hausawa kecewa "qeyace" ahaka
dai zuciyata taita yimin Zantuka marasa fa'ida akan
wannan saurayi, ina wannan tinanin har suka
ƙaraso inda nake, ƙura mata ido kawai nayi na saki
baki tamkar wanda yawu kezuba daga bakisa, ai
tuni najini na faɗa cikin kogin tunani na irin tanadin
da zanyi Mata idan
ta zama matata, dan jinake a raina ko ƙuda bai isa
ya gifta ta gabantaba. ballanta na yataɓa fatar
jikinta batare dana kawar dashi daga doron
ƙasa ba.
sukuwa abinda ke gabansu
Kawai sukeyi, domin nafahimci basusan ma inayi
ba, na fahimci Baƙi ɗayansu suna cikin farin ciki da
annashuwa.
Lokaci guda kuma naji ƙamshin turare ya doki
hancina, hakan yasa na dawo cikin haiyaci na daga
wannan dogon tunanin da na afka, zuciyata ta fara
dukan 3'3!!! Tab.....wannan shine ga koshi ga
kwanan yinwa, Gadai dama ta sake samuwa wajen
gabatar mata da
kaina da irin halin da nashiga a
dalilinta ga kuma wannan saurayin da suke tare na
son zama Barazana wajen Aiwatar da wannan
kudiri nawa Wajen Wannan
kyakkyawar Halitta...
"Qaq Qara Qaqa" zuciyata ta sake fada, wannan
dama da na samu Itace ya kamata nayi amfani da
ita wajen gabatar da kaina agareta dan bansan
lokacin dazan sake ganinta ba, Yauce Ranar da
yakamata na Furta mata kalmar Soyayyata dan
gudun kada nayi Zurfin ciki Har lokaci ya ƙure,
kokuma nayi rashin sa'a ta kuɓucemin..,
Anan na yanke shawar Zuwa na tareta koda kuwa
suna tare da wannan Saurayin yazama dole ya
bani Uzuri idan kuma ba hakaba komai ta Fanjama
fanjam...
Ga mamakina.... Cikin dakakkiyar zuciya na nufi
inda suke, Ina binsu abaya zuciyata na sake bugun
3 3, na riga nagama rikicewa, dan harma na rasa
ta inda zan fara ina cikin wannan yanayin wata
farar dabara tazomin, nayi tinanin bin bayansu har
zuwa inda zasuje haka nata bin
bayansu batare da sun ankara da ina
biye dasu ba har muka isa wani makeken gida,
anan na ja birki na tsaya daga dan nesa kadan dan
ganin ikon Allah zuwa dan wani lokaci, ina tsaye
naga saurayin nan ya fito shi kadai ya nufi
hanyar..........
Kubiyoni kusa labarinASHE MATAR AURECE..........3
........zuwa dan wani lokaci na ga
saurayin nan ya fito shi kadai ya nufi
hanyar da tabi daya bangaren, wato hanyar da bata
inda suka biyoba dazu.
Hausawa nacewa "Rashin sani wanda yafi dare
duhu" Ashe wannan abu daya faru shine farkon
shigata
matsala, domin bai dade da fitowaba
naga itama ta fito, tare suke da wata 'yar karamar
yarinya, 'yar kimanin shekara 9, hakan dana gani
naji zuciyata tayi fari, domin koba komai nasami
sukunin yimata magana.
Cikin tinkaho da farin ciki na doshi
inda wannan kyakyawar halitta take,
kodana karasa kusa da ita banyi
watataba wajen yi mata sallama, ga
mamaki sai naga tayin wani irin kallo me dauke da
zargi, kana ta daga min
hanu batare da ta amsamin sallama ba, ganin haka
nakara bude bakina akaro na 2 tare da daga
murya, dan a tunanina ko bataji sallamar da nakeyi
mata bane, "A'a ikon Allah" Ga mamaki sai naga ta
kara daga min hannu, murmushi kawai nayi da
ganin haka, domin nayi zaton jan ajine irin nasu na
'ya'ya Mata,,,
Na raya hakan a raina, amma kuwa indai haka ake
jan-ajine to lallai wannan jan-ajin baiyiba, domin
duk musulmin kirki idan akayi mai
sallama yazama dole ya amsa, koda
kuwa maiyin wannan sallamar makiyinshi ne, dadai
naga Alamun bata da niyyar amsa wannan
sallamat tawa sai nafara gabatar mata da kaina
kamar haka Da farko nidai Sunana DAHURU, amma
mutane da yawa suna kirana da me Allahu ,,,,
Adai dai lokacin da muka hada ido da ita yamitsa
baki kawai naga tayi, da alamun batani takeyi ba,
dan naga ta dan matsa daga inda nake ta tsaya
daga nesa dani sosai; ganin haka da nayi sai
natambaye wannan yarinyar sunanta tacemi
sunanta SUHAILA, amma kurma ce bata iya
magana, amma kuma tanajin duk
abin da aka fada mata, Yarinyar ta sake buɗe baki
da alamun zataci gaba da magana na dakatar da
ita Da cewa " yaisa, bari haka nagode"
tabbas nayi Matuƙar mamakin ganin irin wannan
kyakyawar suffar da Allah ya azurta
wannan baiwa tasa dashi amma kuma gata Kurma
ce...
Lallai nayarda SO babbar cutace, duk da jin danayi
ance Kurmace bai sanya zuciyata samin tsaiko
dangane da bege wannan mata a raina ba, Saima
jinai tamkar ana kwarara kaunarta azuciyata, Ahaka
na ƙarasa kusa da ita naga tana ƙara ja dabaya
tamkar wadda taga wani mugun abu na dosota,
ashe kuwa kusan hakane,
Domin. Seda nayi danasanin ƙarasawa kusa da ita,
sedana zubar da hawaye mara adadi sana diyar
wannan kara sawa kusa da ita, sedana cizan yatsa
mara anfani a sanadiyar wannan abu,
abindaya faru shine Ina ƙara sawa kusa da ita naga
jikinta yakama karkarwa, kamar taga wata ɓaƙar
Masifa ko bala'i yana dosota, ganin haka yasa na
fara yi mata Magana ina cewa "Lafiyar ki kuwa, Sai
wani guduna kikeyi kamar wanda ya zo miki da
saƙon mutuwa" mamakin yadda naga jikinta yasake
daukar bari...... Sannan naga tanamin nuni da abin
dake Bayana, koda na juya kwatsam.......nayi arba
dashi, bawani bane illa wannan mummunan
Saurayin da suka wuce tare
yanufo inda muke cikin yanayi na fushi da bacin
rai, Ƙarasowarsa keda wuya naga ya wuceni ya isa
inda
take Baiyi watawata ba wajen Wanka
mata Mari yana cewa Waton haryanzu bakiji....ASHE MATAR AURECE....... kashi na 4
.............Ganin kyaikyawan Marin da yayiwa wannan
kyakyawar halitta danai bantsaya jin ƙarashen
maganar dayake yiba, nayi kukan kura na
sungumeshi na ɗaga sama na tafka katan banza
aƙasa, nahau tumurmusarsa mitsiyaci, kafin kace
kwabo tini jama'a sunyi ca akan mu suna ƙoƙarin
kwakuleshi a hannuna,
Saida nayimasa lilis kafin susami damar kwatarsa,
wani babban Abin
mamaki Abin takaici shine koda jama'a suka sami
damar ƙwatarshi awajena ita kuma wadda nayi abin
dan ita se ganinai ta ɗauki wani ƙaton itace ta rafka
min akaina, har saida wajen ya fashe jini ya fara
kwaranya, jiri ya fara ɗibata har nafaɗi ƙasa bansan
inda kaina yake ba......
Daga inda nake a kwance ina iya hangota ta sanya
mutumin nan gaba tana masa kuka tana share masa
jini da majinar da na haɗamasa, hawaye naci gaba da
zuba daga idanunta....
Ganin haka danayi nayi kokarin gyara zama ina
naiman hanyar guduwa, ganin haka jama'ar dake
gurin suka riƙeni aka fara mayar
da magana:- Koda jama'a sukaji abinda yafaru se
suka fara cewa "irinkune ƙwartaye, masu bin Matan
Mutane dama "
Dukda cewa nayi musu rantsuwa akan bansar matar
aure bace amma sukaƙi yarda dani, Suka fara
muhawara a tsakanin su suna cewa "aiwannan kam
bazamu barshi hakaba, domin kuwa laifin nasa 2 ne
ganabin Matar Aure ga kuma na dukan Mijinta
dayayi" Nayi zuru-zuru. Cikina ya kada, narasa abinda
zance
dan tini Har muryata ta dashe wajen rantse-rantsan
Ƙwatar hakina akan cewar Bansan Matar aure bace...
Can bayan wasu ƴan Mintina naga
anɗakko wata sharɓeɓiyar igiya ana
shirin ɗaureni da ita da nifin kafin jami'ano tsaro
suzo, tamkar wanda ya aikata sata,
Ita kuwa SUHAILAT sai sharɓa uban
kuka takeyi, Wani babban abin mamaki danagani a
tattare da ita shine alokacin da nake cikin wannan
tashin hakali saina lura da cewar ƙyawunta har yaso
ya ninka
nada, "ashe garama kukanta da murmushinta kenan
ko?" Wata zuciyar tace dani, dan a lokacin naji wani
Sabon shauƙin ƙaunarta ya ƙara kamani a zuciyata,
har yaso ya ninka nadama, ashe bansani ba da
sauran
Rina a kaba agabana, (ma,ana ashe bala'i na GABA!!!
domin kuwa wannan wanda nake ciki zan'iya cewa
gabatarwa ne kafin inshiga cikin fasalin.
Zuwa can wani dan lokaci saiga hukumar 'ƴan sanda
sun iso gurin kusan mota 3, Da zuwansu kuwa sukayi
arba dani an
ɗaureni tamkar wuwun goro, gashi kuma har zuwa
wannan lokacin jinin raunin da wannan kyaikyawar
halitta tayimin bai dena zubar da jiniba, a haka suka
ɗaukeni suka jefa a Mota batare da sun tausayawa
halin da nake cikiba, Nikuwa ba abinda nakeyi banda
kallonta, har izuwa lokacin da motar ta fara tafiya
hawaye bai daina zuba daga idanunta ba, kafin motar
jami'an tsaran da fara tafiya da sauri seda suka
tabbatar na sume, Bantashi Farkawa ba sai acikin Cell
ɗaure nake a jikin wata kujerar ƙarfe da ankwa, ga
wani Baƙin ɗan sanda waishi GALLOBE wani gajere
dashi kamar na kifeshi da koko a kusa dani, hannusa
yana riƙe da wani ƙaton kulki, Koda yaga na bude
idona da alamun na farka senaga yafara yimin dariya
yana Cewa Nine maganin irin ku....
"Kai yanzu duk 'ƴan Matan da Suke garin nan ka rasa
wadda zakabi Sai Matar Aure...? To yau zakaci Ubanka
kuwa, ai kuwa beyi jira yaji koda kalma ɗaya daga
Bakina ba ya hau Rafkata yata bugamin wannan
kulkin da yake hannunsa, salati da salallami har
nadawo ihu, tun Ina ihu har nagaza ko motsi.
Tabbas nadaɗe inajin Ana cewa 'ƴan sandan basu
Da.......................
Ashe kuwa haka abin yake, dan kuwa masu faɗar
hakan basuyi ƙarya ba, Idan akwai Abin da yafi haka
ma
Idan mutum ya kirasu dashi baiyi
Laifiba a zatona, haka muka kwana da wannan
Azzalumin gajeran dan sanda mesuna GALLOBE har
gari yawaye,
Saboda tsabar dakuwa danayi har bana iya tashi,
Washe gari da Misalin ƙarfe 9:00am Wannan
mummunan Saurayin da suka ce shine mijinta ya
hallata a hukumar 'yan sanda, domin ni agaskiya har
yanzu banyarda da cewar wai shine Mijinta ba,
domin kuwa sam koda wasa basu daceba.. tare suke
da SUHAILAT, sunzone dan rubuta (report) bisa ga
abinda yafaru, basu wani tsaya ɓata lokacinsu wajen
kula da lafiyata ba Gajeran ba Gajeran Ɗan sandan
nan yana shigowa ya kama ƙafata ya fara
Jana kamar wata gawa har zuwa inda za'a ɗauki
report ɗin, Koda muka iso sena lura gabanta yayi
mummunar faɗuwa harda dafe ƙirji ganin irin mugun
yanayin danake ciki, nan da nan naga idanuwanta sun
ciko sunyi jazur hawaye na shirin zubowa, cikin sauri
naga ta kawar da fuskarta daga kaina, ta daina
kallona tana kaɗa kai da alamun nuna matuƙar
tausayawa halin da
nake ciki.
Shikuwa ɗan Banzan mijin nata ko
ajikinshi dan wani kallon ƙasƙanci da
wulaƙanci naga yanayimin, daga nan yafara bada
bayanin ƙarya da gaskiya, dan ya faɗi abubuwa masu
ɗinbin yawa waɗanda ban aikata ba, Ita kanta matar
tasa saida naga ta riƙe baki dataji irin ƙarya
dasharrin daya fara tafkawa akaina, ananne na
Farajin sunansa....
Nikuwa ba abin da nakeyi banda kallonta gami da
murshin nuna bege a zuciyata, harta fice daga police
station ɗin kuwa, Ashe bansani ba akwai wani Sabon
Bala'in da yake tunkaroni wanda yafi wanda nake ciki
a yanzu, Dukda raunukan da suke jikina Wannan
Gajeran ɗansandan bai tausayamin ya ƙyaleni ba Sai
ma ƙarawa dayayi akan na Daren jiya, acewarsa duk
Abinda yake wakana a tsakanina da ita na yanayin
kallan da nake mata akan idansa nake, duk abinda
nayi yariga ya Gama Samin ido, Haka yayi ta jibgata
kamar bazai barni da raiba, yana fadin Wato
haryanzu kai bazaka ƙyale Matar mutane ba ko? Koda
jin Wannan kalma danaji yayi bansan sanda bakina
ya canja daga ihu zuwa sututai ba, ina fadin " wallahi
idankaga na Ƙyale wannan Matar Sai Ranar dana
daina Nunfashi aduniya...
muddin kuwa Ina Nunfashi a ɗoron ƙasa Bazan taɓa
iya haƙura da Soyayyarta a raina ba, koda kuwa
soyayyar tata itace Sanadin Mutuwa ta, nariga na
ɗaukarwa kaina Alƙawarin duk runtsi duk Wahala sai
na cimma Burina na Auran Wannan SUHAILAR...... da
yardar
Allah!!!
kawai saukar kulkin danaji takaru a akaina shi yayi
sanadiyar katse surutan da na keyi, Jirine naji ya
ɗibeni na faɗ ƙasa amma Dukda Haka ban haƙura ba
Sai da na ƙarasa Ambatar sunanta SUHAILAH...
Daga nan na faɗi ƙasa sumamme...
Jama'a ko kusan yadda takaya a gaba kuwa????
Kubiyoni kusha labari,ASHE MATAR AURE CE...? Part 5
FARKON SHIGATA MATSALA
Rayuwa kenan ni kaina
bansantaba, bansan
daga ina ta fitoba, ban
taba ganin taba, bansan
yar wace ƙabila bace,
bansan halayenta ba,
Amma naji sonta ya
Kamani lokaci guda har
na ɗaukarwa kaina
Alƙawarin Sai na Aureta
kota halin ƙaƙa koda
Duk abinda natara zasu
ƙare Koda rayuwatace
Zan iya sadaukarwa
sabi da in Aureta koda
Aranar da aka ɗaura
Aure Zan Mutu...
Daganan suka mayar dani cikin cell ɗina... Komawata
ke da wuya na fito da wannan ledar ta tayar agabana
domin in ɗauka... Ina buɗe bakin Ledar nayi tozali da
abubuwa 2 aciki.., wato Gurasa da wata ƴar ƙaramar
takarda a Anan naɗe.. Ga Alamun dai wasiƙace...
Ganin kwana na 2 ban ɗanɗani koda ruwaba
ballantana Abinci.. Na hau gutsurar gurasannan
Batare da na tsaya Buɗe wasiƙar ba ballantana Nasan
Abinda ta ƙunsa... Ai kuwa ina gama cin gurasar nan
Na ɗauki takardar na fara buɗeta... Inagama buɗewa..
Kafin na fara karantawa naga An fisgeta daka
hannuna...
Ɗaga idona danayi.. Naganshi tsaye akaina... Ba wani
bane Illah wannan Mugun ɗan Sandan da yariga
yagama samin ido... Kafin in furta wata magana naga
ya fitoda Lete daga Aljihunsa ya ɗannawa takardar
nan wuta... Yace ai duk Abinda ya wakana
atsakaninku ina gani... ashe itama Munafu..., Ban bari
ya ƙarasa Abinda yake son faɗaba na sureshi na
ɗagashi Sama ta Tafkashi a ƙasa na hau kanshi nayi ta
dukanshi baji Bagani... Yayita Ihu kafin kace kwabo
Sauran Jami'an ƴan Sandan sun kewayemu.. Suna
ƙoƙarin Kwatar shi... Dadai sukaga bahali.. suka hau
dukana da sanduna har nafaɗi sumamme...
Bantashi farkawa ba Sai washe gari da Misalin ƙarfe
8:43 na safe..
Aka fito dani da Hankoof ɗaure a Hanuna akan
za'akaini kotu...
Jin maganar tafiya Kotun danaji Anyi shiyayi matuƙar
tayar min da hankali har yafi na wanda nake ciki
nasan Tabbas ba makawa Sai natafi Gidan Yari... Dan
bawani Mai goyon Bayana daga cikin 'ƴan sandan
Kuma bana son Koda mutum ɗayane Daga cikin
Dangin mu Yasani... Ballantana
Da misalin ƙarfe 10:00 muka isa Kotu... Mukatar da
Kotu tacika maƙil da jama'a mu kaɗai ake jira..
Shigowar mu ke dawuya tundaga bakin kofa naga
tana kallona har zuwa inda ake tsayar da wanda ake
tuhuma da laifi... Mai gabatar da ƙara ya fara
gabatarwa Kamar Haka...
ANA ZARGIN MUSA DA BIN MATAR WANI ALHALIN
KUMA YASAN MATAR AURECE ASAKAMA KON MIJIN
MATAR YAYI MAI MAGANA YA HAUSHI DA DUKA SAI
DA YA SUMAR DASHI DA ƘYAR AL'UMAR DA SUKA
KAWO AGAJI SUKA ƘARƁE SHI...
ASHE MATAR AURECE...6
sabuwar matsala ta Samu,,,,
Aranar da nafito daga gidan yari Ban
zame koinaba sai Gidah,,,
tundaga Nesa naga Mutanen unguwarmu
suna yimin wani irin kallon Ban mamaki
mai dauke da alamun tambaya,, dayawa
daga cikin su har nunani sukeyi da
hannu,, yara kuwa har guduna naga sun
farayi.. Tabbas nacika da mamakin ganin
wannan sabon lamari dake faruwa har
takai na fara zargin kaina akan kodai
sunji labarin abinda ya faru tsakanina da
wannan mummunan mutumin nan tare
da matarsa kuma Masoyiyata..?
Jikina gabaki daya yayi sanyi daganin
wannansabon lamari har takai na fara
tunanin Kada na Karasa.. Dana isa bakin
kofar gidan mu ina tsaye zuciyata na
bugun 3:3 kwatsam naga kanina AMEER
ya fito
daga cikin gida ganina da yayi naji ya
kwalla wani uban ihu ya juya ciki da
gudu.. Kafin inyi yungurin wani abu naga
Mutanen gidan mu baki dayansu sun fito
da gudu ganina da sukayi baki dayansu
suka cika da Al'ajabi suna cewa SADEEQ
daman kananan da Rai!!!!!...?
Kaikuwa wace duniya ka tafi haka.. Har
kowa ya dauka ka mutu..!!! Yau kimanin
Wata 3 da kwana 2 kenan Tundaga ranar
da kafita da yamma ba wanda ya kara
ganinka ko jin labarinka.. An naimeka a
waya an rasaka.. Ga yanayin garin namu
tashin hankali yau tashin hankali gobe..
Yau sati 3 da kwana 5 kenan da gama
zaman makokinka.... Dariya ce ta
subucemin dajin danayi sunce har anyi
zamanmakokina...
Wannan shine abinda ya baiwa
Mahaifiyata Haushi kenan har takai ta
tafka min Mari... Dukda marina da tayi
ban daina Mamakin cewa da sukayi na
Mutu ba.. Abinda na cikaba da
Maimaitawa shine.. Kallonsu nakeyi Ina
cewa Wai na Mutu..!!! Sai in kyalkyale da
dariya.. Bai fi minti biyar da faruwan
wannan lamari ba kofar gidan mu tacika
makyil da Jama'a sunzo kallona Suma
suna Mamaki Na Mutu na Dawo...
To wata sabuwa amma karku damu kudai
kubiyoni kuji yadda zata kaya bayan
fitowar tawa zanci gaba da son SUHAILAT
ko kuma zan hakura ne
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 1 Chapter of 1