Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 1
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels GUGUWAR ANNOBA -> Madakin Gini Book 2 littafin Yaki 08137237071 Lokacin da kyakkyawar budurwar tazo nan a zancenta sai Sarki Yarduza yai shiru yana tunani da nazari, daga can sai ya dubi kyakkyawar budurwar ya ce, "Yanzu dai zan biyaki kudinki na wannan barewa, amma ki bani zuwa gobe zan dawo nan kamar i yanzu domin na sanar da ke abinda na yanke hukunci". Koda gama fadın haka sai Sarki Yarduza ya sanya hannunsa a cikin aljihu ya fiddo kudi ya kirga dinare dubu ya mikawa budurwar, ita kuwa sai ta karba tana mai murmushi a gareshi irin wanda ka zauta kowanne da namiji saboda tsananin kyawunta. Kawai sai ta juya ta falfala da gudu izuwa cikin dajin. Sarkin ya bita da kallo tun yana iya hangenta har ta bace bat. Ba tare da wani bata lokaci ba Sarki Yarduza ya dauki wannan barewa ya koma inda dokinsa yake ya iskeshi kamar yadda ya barshi a daure jikin bishiya cikin koshin lafiya. Cikin sauri ya kwance dokin ya hau ya kama hanyar komawa gida., Tunda ya fara wannan tafiya ya tsinci kansa a cikin begen wannan kyakkyawar budurwa, yaji babu abinda yake so a duniya sama ita, sannan ya shiga tunanin alfarmar da take nema a wajensa. Ya tambayi kansa a ciki zuciyarsa ya ce: "Wai shin saboda me budurwar za ta nemi irin wannan alfarma tamkar so take tayi masa juyin mulki a wayance?" Wata zuciyar kuma ta ce da shi; "Ta ya ya za a iya yi masa juyin mulki da ransa da lafiyarsa alhalin gunki Salkas na nan?" Koda yazo nan a zancen zucinsa sai yaji zuciyarsa ta buga da karfi. Tsoro ya baibaye zuciyarsa, ba komai bane ya haddasa hakan ba face wata tambaya da ya yiwa kansa, ya ce: "To mene ne dalilin da ya sa a yau bai samu nasarar abinda ya fito yi ba alhalin kuma bai fito ba sai da ya gana da gunki Salkar?" Nan take hankalin Sarki Yarduza ya dugunzuma ainun, amma sai ya kudurce a ransa cewa yana zuwa gida zai gana da gunki Salkar domin ya warware masa wadannan matsalolida yake ta faman wasi-wasi a kansu. Sarki Yarduza na isa gida ya sauka daga kan dokinsa, wani bawa ya karbi dokin da saui ya tafi da shi izuwa Barga shi kuma sai ya wuce kai tsaye izuwa cikin dakin da gunki Salkar yake. Da shigar Sarki cikin dakin sai ya maida kofa ya rufe, sannan yaje ya durkusa a gaban gunki Salkar bisa guiwoyinsa kamar yadda ya saba. Har ya budi baki zai ce wani abu sai wata kakkausar murya daga cikin gunki Salkar ta ce, "Ya kai wannan Sarki mai biyayya a garemu, kamar yadda iyayenka da Kakanninka suka gabata, kayi sani cewa har abada ba zamu cutar da kai ba domin akwai alkawari mai girma a tsakaninmu da zuri'arka. Ina so ka sani cewa wani lokaci shirunmu shi ne mafi alheri a gareka. Ka saurara da kyau ka ji bayanin da zamu yi maka a vanzu, in yaso sai ka zabawa kanka abinda zai fiye mika, amma idan ka nemi shawararmu lallai za baka". Gunki Salkar yai ajiyar numfashi sannan ya ce, "Wannan kyakkyawar budurwa da ka hadu da ita a daji ba wata bace face SHARLISA 'YAR KURAISU, dan uwan mahaifinka wanda ya басе kimanin shekaru talatin da biyar baya, wato tun lokacin da mahaifinka ya hau karagar mulki. Tsananin bakin ciki ne yasa Kuraisu ya dauke matarsa ya tattara inasa-inasa ya bar gari saboda shine wanda ya kamata ya zama Sarki, amma sai aka baiwa mahaifinka bayan an shirya musu wata gasa a tsakaninsu mahaifinka ya lashe gasar. Lokacin da Kakanka ya kwanta cutar ajali ya zamana cewa ciwo ya yi tsanani kullum babu sauki sai hankalin 'yan majalisa ya dugunzuma saboda basu san wanda ya kamata ya gaji Sarki ba tsakanin Yarduza da Kuraisu. Kuraisu shi ne, babba domin ya girmi mahaifinka Yarduza da shekaru uku, kuma ya fi mahaifinka jarumtaka, kwarjini da sanin harkokin mulki. A ranar da ya rage saura kwana biyu kakanka ya mutu sai yasa aka kirawo masa 'yan majalisa ya kadaita da su a cikin turakarsa sai yai tari sannan ya budi baki da kyar ya ce da su, "Ya ku 'yan majalisata kuyi sani cewa ban kiraku ba domin komai sai domin na bar muku wasiyya akan yadda za ku fitar da gwani a cikin 'ya'yana wanda zai gajeni. Abinda nake so da ku shi ne, bayan na mutu a shirya gasar yaki tsakanin 'ya'yana, Yarduza da Kuraisu, wanda duk ya kai daya kasa to shi ne zai zama Sarki". Koda jin wannan batu sai mamaki ya kama ya wuce gaba sauran makarrabansa suka bishi a baya. A sannan ne yarima Yarduza ya matso daf da yarima Kuraisu ya cc, "Ya kai dan uwana ka kwantar da hankalinka ka sani cewa kai ne za ka gaji mahaifinmu tunda kaine gaba da ni, kuma ka fini jarumta da karfi da sanin mulki. Lallai kaine kafi cancanta da ka zamo Sarki ba ni ba. ⚫ Ni kam nayi maka alkawarin cewar zan kasance mai biyayya a gareka koda kuwa ba zan sami mulkin komai ba a cikin mulkin naka". Sa'adda yarima Kuraisu yaji wannan bayu sai ya kyalkyale da dariya, lokaci guda kuma ya turbune fuska ya ce, "Ya kai Yarduza kayi sani cewa tsakanina da kai har abada babu yarda da aminci domin na san cewa inda kana da iko da tuni yanzu ka kasheni domin ka sami damar hawa kan wannan karagar mulki. Ina tabbatar maka da cewa koda na sama Sarki ba zan yarda ka zauna a kusa d ani ba sai dai ka bar cikin garina ka koma daji da zama idan za ka iya. Idan kuma ba za ka iya ba sai dai ka bar kasar gaba daya, saboda idan na zauna tare da kai hankalina ba zai taba kwanciya ba. Da zama tare da kai gwara na kwanta akan gadona tare da bakin maciji a cikin mayafına wanda a ko yaushe zai iya sarata ya sa min dafi a jikina". Lokacin da Kuraisu ya zo nan a zancensa sai yarima Yarduza ya cika da tsananin mamaki da takaici har kwalla ta zubo masa ya ce, "Ya kai dan uwana kayi sani cewa ban taba tsammanin cewa haka matsayina yake a wajenka ba. Ka tsaya kayi tunani tun muna yara, shin na taba cutar da kai ne? Idan baka manta ba, babu irin wahalar da baka bani ba. A kalla ka sumar da ni ya kai sau goma, sannan ka sha sa mini kunama a cikin rigata ya yin da nake barci tana harbina. Sau uku kana jefani a cikin rijiya mai zurfin gaske amma saboda ina da nisan kwana ban mutu ba. Duk wadannan abubuwa kana yi mini su ne saboda kishin cewa ni kadai ne matsalarka a fagen samun sarautar kasar nan. Ko sau daya ban taba kullatarka ba a cikin zuciyata bisa wadannan abubuwa da kayi mini, kuma ban taba tunanin daukar fansa ba. Sai a yanzu da komai ya zo karshe kake tunanin zan iya yi maka hassada ko na cutar da kai. In dai saboda wannan mulki ka ke son ka nisanta da ni ni kam na hakura da mulkin, kuma turakarsa da kuma jinyar rashin lafiyar da yake fama da ita. Yarduza ya ruga da gudu da sauri ya kama kafadun Sarki ya zaunar da shi bisa wani dakalin gini, sannan ya dubeshi cikin tsananin damuwa ya ce, "Ya kai Abbana akan wane dalili za ka fito da kanka har nan a cikin wannan hali da kake ciki na rashin lafiya?" Koda jin wannan tambaya sai Sarki ya kawo gwauron numfashi ya ce, "Ya kai dana ai dole ce ta sa na fito, domin idan ka tafi shi ke nan sarautar garin nan ta bar zuri'armu har abada. Idan har yarima Kuraisu ne ya hau kan karagar mulki ko shekara uku ba zai yi ba akan karagar za a zo a cishi da yaki a kawar da shi. Idan kuwa kaine ka zama Sarki, sai ka shafc sama da shekaru sittin akai. Sannan idan kai ne ka zama Sarki za ka yi adalci kuma talakawa za su ji dadinka, sannan arziki zai yawaita sabanin idan Kuraisu ne sai an sami fatara, talauci da rushewar daukaka. Ya kai dana kayi sani cewa duk wannan labari da na sanar da kai a yanzu gunki Salkar ne ya sanar da ni. Idan na mutu za ku yi gasar yaki kai da dan uwanka Kuraisu wanda duk ya kai wani kas shi ne zai gajeni. Idan har ka tafi baka tsaya kayi wannan gasa ba ka sani cewa kamar ka rushe Birnin nan ne, kuma har abada ba zai sake wanzuwa ba." Sa'adda Sarki yazo nan a zancensa sai yarima Yarduza ya cika da tsananin mamaki kuma hankalinsa ya dugunzuma ainun har kwalla ta ciko idanunsa ya ce, "Ya kai Abbana yanzu ta ya ya kake tsammanin cewa zan iya tarar yarima Kuraisu har na iya fafata yaki da shi na kaishi kas alhalin ya fini girma, karfi, wayo da dabarar iya yaki?' Sarki ya kama hannun yarima Yarduza da kyar ya ce, "Ya kai dana kayi sani cewa sau tari nasaraz ta danganta akan sa'a da kuma dakewar zuciya. Ka sa a ranka cewa ta kowanne hali sai ka sami nasara domin ceton kasarka da jama'arka. Wnanan shi ne kadai abinda za ka yi ka cika mini babban burina na duniya. Kuma irin wannan buri ne nima na cikawa nawa mahaifin bayan mutuwarsa. Idan har ka sami nasara tabbas kaima sai ka haifi wanda zai cika maka irin annan buri komai daren dadewa. Da wannan furuci nake yi maka bankwana na karshe, domin abu ne mawuyaci mu sake ganina Mu hadu a littafi na uku 08137237071 An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 1 of 1