Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
7 / 7
qur'anin tana karantawa,suratul mulk take karantawa cikin siririyar murya a hankali,wanda sai kayi dagaske kafin kaji harrufan suna fita akan labbanta. Yarone ya banko ƙofar langa langar wanda saida yasa salaha razana ta ɗago da sauri,ɗan gidan Zulai ne wanda yakebin Iliya. "Salaha wai kizo inji wani a waje" "Wani a waje kuma ni,waye?" To waye zai nemeni kuma ma da daddarennan,a ranta tayi wannan tambayar kafin yaron yabata amsar tambayar da tayi masa a zahiri. "Bansanshi ba kawai dai yace dan Allah kizo" Har ta buɗe qur'anin zata cigaba da karantawa saikuma maganar da sukayi da addah shekaranjiya ta faɗo mata,kan cewar tunda a cikin abinda ta manta na rayuwarta banda ilimin ta,shine ta bata shawara kan ta nemi koyarwa a islamiyya da boko idan har ta samu ko dubu biyar biyar suke bata zata rage wani abun,idan ta dawo kuma sai tana saqar kwandonta a gida ko ɗakinta. Bayan ta amincene Addah tayiwa wani malamin islamiyyar bayansu malam baqeer maganar salahan,kuma yace idan yadawo daga karatu zai biyo suyi magana tunda suna hutu ballantana ta sameshi a makaranta. To duk a tunaninta wataƙila bazai wuce shi ba,to amma da daddarennan? Share tantamarta tayi ta saka hijabi kana ta nufi ƙofar addan. A zaune tasameta itada wata baƙuwa ta zomata hira,suna kuwa tayin hirar cacai cacai kamar tsuntsaye. "Assalamu Alaikum adda dama a wajene wai ana sallama dani inji yaro,shine zanje na dubo ko malam baqeer ne dayace zai zo" "Ehhh bazai wuce shiɗinba inaga sun tashi a karatun darene ya biyo ganin yanada lokaci,to kije kuyi maganar Allah yabada sa'a" Ameen ta amsa dashi a taƙaice kafin ta nufi ƙofar gidan cikin nutsuwa. A cike ƙofar gidan yake da yara sunata wasa,maza suna guje guje mata kuma sai shewar gaɗa ce take tashi. A can gefe ta hango mutum yana jingine da wani kututturen bishiya,ganin fitowarta ya tashi daga jinginen ya tsaya,hakan yabata alamar shine ke nemanta. Saidai daga inda take tsaye tana hango ƙananan kayane a jikinsa riga da wando. Wanda aka ce ustazine mai ya haɗashi kuma da saka ƙananun ƙaya. Daurewa dai tayi ta isa saboda baka shedar mutum tun bakayi ido huɗu dashi ba. Da sallama a bakinta da ƙarisa wajen,saidai maimakon sallama ta dawo gareta da mutum mai addini sai kuma wata shakyakykyiyar murya data doki dodon kunnenta. "Barka dai sarauniyar matan duk duniya,nayi zaton bazaki fitoba,sai kuma gashi ga mamakina kin amsa ƙirana kin zo gareni" Razana salaha tayi tareda ɗora hannunwanta a ƙirji tana kallonsa da idonta kaman zasu fito waje. "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Sune kalaman da bakinta yafara maimaita da sauri,ganin hakanne yasa Jazuli matsowa a hankali kusada ita domin ya kwantar mata da hankali. Maimakon hakan ya taimaka saima ƙara ta'azzara abin dayayi,domin ganin ya matso inda take da sauri salaha ta juya ta koma gidan a tsorace. Shima cikeda rashin sanin yakamata yabi bayan yana ƙiranta har ta shige gidan shima yabi bayanta suke shige tare. Waigawar da salaha tayi taga yabiyota shine yasake razana ta tasaki wani kuka bata nufi ɗakinta ba saboda tasan binta zayyi,saita nufi sashen adda. Suna zaune sai ganin mutum sukayi ta tsallaka su ta wuce ɗaki.shima daidai lokacin ya ƙariso yana ƙiranta. A tare adda da kuma baƙuwartata suka kalleshi. Baƙuwar ce tafara magana tareda cewa. "Dama ai nasan bazaka iya tsayawa a waje ka jira wannan doguwar hirar tamu ba nida adda....." "ahah ya naga ina magana kana kallon ɗaki kodai kaine ka aika a ƙirata kuma ka biyota" Adda ta faɗa tana ƙaremasa kallo. Sosa ƙeya yayi wacce babu komai a wajen an katseshi an bar iya saman kan irinna na nigogi. "Alhamdulillah alhamdulillah ubana yau kaine kebin mace hadda kunya ashe zanga wanga rana" Matar ta faɗa cikeda murna......tohhh fah Amin magana ta wannan layin 09035784150 Sadi-sakhna ce. An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 7 of 7