Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 3
hakan na nufin zanmutu ne, zan canja halina zanbar duk abinda nakeyi, saboda taraiya dakai yafi komi muhimmanci agareni, yakalleni yajuya yatafi, tun daga ranar ni Ambar na nutsu, nadaina xuwa duk wani party, hatta shigana na canja, naje kasuwa nasiyo yadin hijabai nadinka nafara sawa, nadaina kula kowa, saidai har lokacin fuad yaki bani fuska, narame ina shirin fita hayyacina domin soyayya, ibada na dawoyi sosai ina rokon gafaran Allah sannan ina neman hankalin fuad, nazauna a barhaq ina cin abinci watarana, wani yazo yanata murmushi ambar, na kalleshi na kauda kai, yayi yayi naki kulashi. Kaina a sunkuye, can naji mutum yazauna kusa dani yakira mai bada abinci yayi ordern abinda nayi order, inajinshi anma tunanina baya gun, hankalina bai nutsu ba, can yace ambar, gabana yayi mummunan fadi, muryan fahad dayadda yake kiran sunana na dago naga shine for the first time naga yanamun murmushi. Sai yace kishirya karfe 5 zanxo anjima yaci abincinss harya gama bance komiba, kodan murna ne,? Ina xuwa hostel nayi wanka nayi sallah dama hafsat taje abuja gun wani saurayinta, nashirya tsaf cikin abaya karfe biyar yazo yakiran nafita muka zauna a motarsa yace nalura kin canja sosai ambar, hakan dakikayi shine mutunci kinga kinjawa kanki mutunci, ko ina kikaje, anma macen dabata da kamun kai ba mace bace, nan yace ambar tun randa nafara sonki naji ina sonki saidai da aka gayamun halinki naji na tsaneki, nayi niyyan bazantaba alaka dake ba anma ganin kincanja saboda ni yasa nabaki chance, ambar i love u, kuka nayi sosai, bance komaiba, har muka rabu, tundaga ranan nida fuad kaman tom nd jerry, soyyanmu tayi karfi soyayya mai tsabta, hannuna fuad baitaba rikewa ba, duk shaawata haka nake dannewa yazo yakawo nafara azumi hakan ya mugun taimakona, dlfuad ya taimakamin ina kara ilmin addini, duk wanda yasanni yasan fuad har gun momy nakaishi taji dadi saboda tayaba da hankalinshi, nanfa ma hassada akasamu abunyi yau akai wa fuad wannan gulman jibi akai masa, most abunda ya fi burgeni shine baitaba sauraransu ba, saidai yayi ignoring , tuni nasawa raina nasamu mijin aure, a satin hafsat tadawo nan namata bayani fuad atake nace oya bani dubu dari na. Tace zata samun, hankalina a kwance, bansaniba ashe hafsat ma son fuad take tadade tana harinnsa bata sameshiba gashi tashi daya nasameshi abinda ya bata mata rai kenan, haka muka gama wannan semestern nida fuad kullum tare cin abinci tare. Karatu tare komi tare, munason junanmu sosai, saidai duk lokacin da fuad yaga hafsat baya sakewa yasha cemun narabu da ita ba kawa bace karnazo ina dana sani, nakancemasa itakadai natashi da ita anma zanyi kokari naga ta. Canja 10anma duk dahaka fuad bayaso, ahaka muka shiga aji biyu alokacin fuad yagama yafita da second class upper munyi murna sosai, nan yafara shirin tafiya service, mukuma munshiga aji biyu watarana ina assighnment naga kiranshi nadauka tareda cewa my dear, yace fito inason ganinki yadda yayi maganan muryanshi narawa nace toh, inafita kofan hostel nace dear na meya faru, yace karki kuskura ki yaudaren, macuciya azzaluma, marar imani ashe haka kike nayi danasanin saninki, nayi danasanin haduwa dake. Hankalina yatashi sosai nace fuad menayi yaja tsaki yace ashe soyayyanmu akan bet kikeyi? Akan dubu dari ambar kika karbi soyayyata? Allah ya isa tsakanina dake, nace fuad bahaka bane wlh tlh fuad bahaka bane, yace ki amsamin yes or no, na sunkuyar da kai sannan nace yes, ya buga motan dakarfi how could u ambar? Y? Ya shiga cikin motansa sannan yace kisa aranki baki taba sanin waye fuad ba, tsakanina dake yakare, yaja motansa yatafi kuka nafarayi nadauki wayata nakira hafsat tace tana daki dasauri naje raina abace nace akanme zaki fada wa fuad? Tace luk hafsat rayuwace, kowacce mace da basirarta, kinmanta kema duk macen dakika ga saurayinta kwacewa kikeyi? Yes naga fuad i love him, kuma naga yanasonki so i have to separate the two of u before na iya shiga ransa, na rikota nahadata da bango hafsat i hate u, nayi regretn saninki , saninki baijawomin komi ba sai bakin ciki, nan fa muka fara fada dakyar aka rabamu na tattara kayana nadawo gyda, nan momy hankalinta yatashi dana gayamata meya faru momy shiru tayi tace kiyi hkr, kicireshi kema, nace mony fuad nacikin bacin raine anma inya huce zanbashi hkr tace tohm, anma me???, sati daya nagagara cin abinci fuad baya picking calls dina z nima nadaina zuwa lectures koyaushe ina nemanshi ranan muka hadu akofan barhaq ina bashi hkr haka fuad yakallen gashi akwai mutane haka nasauke girman kai, yadauki ruwan gora ya watsamin tareda cewa ambar in mafarki kikeyi kifarka nace bansanki ba i hate u, ko ke mayyace? Nayi kuka sosai har cikin raina, bantashi shiga tashin hankali ba saidanaga hafsat da fuad a mota suna dariya cikin kwanciyan hankali, innalilahi wainna ilaihi rajiun sanda ne agefena na karfe nadauka ina xuwa jikin motan nabude najawo hafsat na kwala mata ko ta ina ajikinta fuad dakarfi ya fizgeni for the first time arayuwata da fuad yarikeni, ya wankamin mari tareda cewa ambar bana sonki bana sonki bana kaunar ganinki kifita acikin rayuwata dolene? Kuka nakeyi sosai ga mutane suncikaa ina kuka sosai, har suka tafi, yakai hafsat clinic, nayi ciwon SO, maza mayaudara ne, maci amana, basuda alkawari, duk sacrifice dazaki musu idan halinsu ya motsa saisunyi abunda ransu yabasu, idan zaki bawa namiji hakorinki na karshe anma namiji zaiyi using wannan hakorin yayi dariya wa wata, zaki iya mutuwa akan namiji anma namiji zai je dawata janaizarki, tuni nafita hayyacina, nafara sumbatu domin kuwa son fuad yamin kololuwan illa, of all girls inrasa meyaudarata sai hafsat? Sumbatu nake, bana hayyacina, tuni nakoma ruuwa tsundum, wannan karon harda shaye shaye nafara rayuwata ta kara shiga garari, randa naga bazan iyaba kawai na wuce club daredare anan nahadu dawani banma san sunanshi ba don alokacin nafara ganinshi yalura ina cikin damuwa tuni yabani kwalban giya yace nasha kadan, aikuwa dana kafa kai saida nasha yafi rabi, yayi dariya yace daga yanzu bazaki kara jin damuwa ba, tuni na fita hayyacina nan nafara surutai ba buge buge. Yadaukeni yakaini hotel, dama sanadin fuad nashiryu nadena kula maza donhaka atake nazubar da randan shaawan dake damuna, mun mori juna duk abuge, washegari dasafe ganina nayi nikadai a hotel tuni nasa kayata nadauki wayata nayi gida, momy hankalinta yatashi anan na mata karyan ai na kwana a makaranta saboda wani assighnmemt nan tamin fadan aidana fada mata sannan duk lokacin da zankwana nagayamata, nan nacigaba da xuwa party na aboye, ina shaye shaye na, idan nayi high sai dai na tsinceni a hotel, gaba daya kwanyata ta toshe nadena karatu hatta exams banyi cikakke ba, muna hutu wata rana natashi da amai, sosai hakan yasamin zazzabi nanfa hsnkalin momy yatashi tace ko malaria ne, anan mukaje asibiti test din farko likitan yace inada ciki, tunda momy ta haifen bantaba shiga tashin hankali irin wannan ba, momy atake tazubar da wayoyin hannunta, tace likita zamu dawo , tasani agaba mukaje gyda, momy tana kuka amina na kuka, momy nacewa yanzu ambar tarbiyan dana baki kenan? Haba ambar! Yaza ki samin zargin cewa ban baki tarbiya mai kyau ba, innalilah. Tadauki waya takira daddy tace kayi kazo gyda duk garin dakake, tarufeni adaki nikuwa sai kuka, danasani fal a fuskata, nan na fara tunanin wacce irin rayuwa nadauka ma kaina, washegari daddy yadawo har lokacin bawanda yaci abinci acikinmu, tamishi bayani a harzuke daddy yacire belt yashigo dakina yarinka naushina, duka kam nasha har takeni daddy yayi tsantsan duka, yanacewa shiba irin tarbiyan dayabanba kenan, infita inbarmoshi gida karna spoiling masa image a matsayinsa na babban mutum sannan dan siyasa, nan momy takafe cewa laifin dady ne inba kana zaune agyda ba tayaya zaka dauramin tarbiyan yara mata ahannuna nikadai, inbanda aikinka baka da lokacin kowa, gashi yarka ta kwaso maka rabonka, nanfa fada yakoma kan momy, daddy yace ya gwammaci ace masa na mutu akan acemasa na yi ciki, habawa sai duka yarufeni yace kasheni zaiyi, tabbas nasan zai iya daddy nada mummunan zuciya donhaka tuni naroki momy ta taimakamin tadauko atm da purse kudine aciki tace gashi ambar kibar garinnan ki tafi gombe akwai kudi aciki kiyi settling zanzo nasameki , tabudemin kofa ina kuka nafice motan gombe nashiga tunani nakeyi sosai don Allah yagani nayi dana sanin abunda na aikata Abinda Aka Gasa Shi Yaga Wuta 15 3 days ago Abinda Aka Gasa Shi Yaga Wuta 14 6 days ago Abinda Aka Gasa Shi Yaga Wuta 13 1 week ago Abinda Aka Gasa Shi Yaga Wuta 15 3 days ago Abinda Aka Gasa Shi Yaga Wuta 14 6 days ago Abinda Aka Gasa Shi Yaga Wuta 13 1 week ago Share this on WhatsApp Share this on WhatsApp muna isa gombe bansaniba saida ta gefena ta tabani sannan ta sanar mun , nafito jiki a kasale, na hau kekenapep nace malam kataimaka kakaini inda zansamu hotel, aikuwa yakaini wata hotel yar daidai nakama daki na sati nashiga ciki da falo, kwantawa adakin nayi nafara kuka sosai, nayi nadama sosai, tunanin momy da daddy nake, bayan gydan nashiga domin na yi wanka, nashiga bathtub din fad na sulale nafadi, na bugu sosai sannan namuke nafito jini ke zuba ajikina nan nakira hostel service din tuni suka kaini asibiti bansan adadin kwana nawa nayiba nidai nabude naga momy agefena, zanyi magana tahanani, nan take cemun ai cikin ya zube, a hotel din sunrasa wazasu nema nawa, saisuka dauki wayata suka kirata, tace alhmdlh da cikin yafita yanzu kinga daddynki zai hakura kizauna, Allah yagani haushin dadyna nakeji duk shiyajawomin bayada lokacinmu, harda laifina nabin kawayen banza dasunan wayewa akarshe wa wa gari ya waya? Nagama asara , ba budurci ga ciki ga shaye shaye ga hulda da maza. Subhannalah, kuka nayi sosai koda aka sallamen nadawo gyda dakyar daddy yabarni nazauna, nanfa naciga da rayuwa a takure, anan nakejin lbrn ai hafsat sunrabu da fuad,anma bawanda yasan dalili, gashi anma result gp na ya balain saukowa har 1point ga courses danake carryn, naji haushi tuni nasiya sabon littafin canja rayuwa, nadawo mumina, ba ruwana azubi mon nd thurs, ga hijabi da liqab, ga zuwa islamiya rayuwata nadawo ina takurata ahaka nasamu nacigaba da karatuna, wasa wasa bana da saurati tsayayye guda daya na arziki wanda zanfitar a matsayin miji, duk samarin danake ganin sunmin over yanzu lokaci yakai da bana ganinsu , magidantan ma insunxo jikina sukeso daga baya nadawo nukadai kaman mayya dox moments are the worst moment of life, momy tace i should learn a simple lesson from dat duk wacce batayi usn ooppotunitynta ba tym will come da zaiwucemiki nd u shall regret it, aikuwa nagani don wasa wasa gashu har nayi grads babu mijin aure. Gashi inason auren, anma me,?? samarin duk sun gudu, bana ganin kewar kowa, tunda na kama kaina, harnake cewa tph kowani namiji dan iska ne, wasa wasa harnagama atbu nayi 6yrs dakyar nafita da second class lower, nan nazo inajiran inyi service duk dahaka shiru, watarana nafito daga sallooon zanyi gyda kawai abun mamaki naga taslim a makwabta yaje hira, na kare masa kallo tabbas yakara girma gashi yayi kyau , ga kwarjini yayi fresh na kalleshi saina tunafa ashe shine yafaramin illa a rayuwata, gashi yazauna da wata a mota hankalinsa kwance sai hirarsa yake nazo na wucesu, anma ranan ban iya bacci ba, taslim is my first love dole sonshi tadawo min danye araina, nanfa nalura yarinyan dayake xuwa gunta fauxa ss2 take lalle namiji dan iska ne, yagama lalata yanmata anma sai kuga yanabin kananun yara dasunan aure, aikuwa tuni haukata ta motsa nace idan ban aureshiba toh kuwa bawacce zata aureshi, nasa aka nemomin nukbansa nakirasa yayi mamaki kwarai tareda cewa yazata nayi aure nace masa aina zanyi aure munyi alkawari dakai, yayi murmushi yace bakida mantuwa ambar ai lokacin yarinta ne, dakin yi aurenki dont bother abt me, nace but i do, so is beta kasan nayi don naga kwana biyu inda kake xuwa yu bets change plans or yull c a big problem, yayi shiru can yakashe ina zaune naga txt dinshi gashi akofar gydanmu nafita nasameshi yakalleni yace ambar nazo mu fahimci juna, ambar u r my age mate, aurenmu bazaiyi yiwuba kuma ni tuni na manta dake. Nayi darriya nace dole kamanta dani tunda ka kwanta ka ketamin budurcina, yaja tsaki toh ai kinga matsalar ku kenan na hausawa mace don kayi havn sex da ita saitace aurenka zatayi, ke kintsba ganin anyi haka,? Na kwanta dake na aureki? No i need a fresh blood, kinmun tsufa, kuma am quite sure badani kadai kikayi ba, beta find away, before nazama ciwon kai, yaja motarsa yatafi nayi kuka sosai nayi dana sani, duk dadin bakinsa ina yake? Namiji zaimiki dadin bakine idan yanada bukata duk lokacin dakika kuskura kika bayar toh daga ranan dake da slippers darajanku daya, zaki iya zama da namiji yana binki akan kibashi kanki for years kiyi tunanin sonkine, anma inaaa duk randa kika kuskura toh wlh zai rabu dake, idan bai rabu dake alokacinba toh kinzama masa sex machine don zai bukaceki ko yaushe sannan maganan aure na tasowa shikenan zakiga ya ware, toh waini meya kaini tun farko? Na farko bin kawar banza, na biyu rashin rikon addini, don nasan ko salloli nake tsayarwa da kyau bazai barni na aikata zinaba, duk mai zunubi mai aikatawa ya binciki addininsa, ga dai tarbiyan iyaye alhmdulilah sunyi kokari, kuka nake sosai bantashi fuskantan tashin hankali ba sai da aka cemin aminanmu zatayi aure, wayyoni kanwata ta kama kanta gashi miji yazo mata tun tana ss2 yafi mata, nifa ? Yatawa rayuwar take? nanfa mukayi bikin amina muka gama tasha gata kam, nanfa nafara jin surutai danginmu anfara maganan meyasa bazanyi aureba, nanfa momy hankalinta yatashi dady kuwa cewa yayi yaban sati biyu idan ban fito da miji ba toh zai badani, ban damuba gwara ma yayi hakan saboda ayanzu da banda tsayayyen nab gwara hakan, aikuwa daddy yabadani wa dan abokinsa aliyu haidar, ali baitaba aureba anma shekaransa 34 nanfa ba shiri aka fara hidiman biki ko bari baayi munsaba ba, shimadai ba yabo ba fallasa, tun randa daddy yace nafito da miji ko yasamamin nafara dilka da gyran jiki, akalla na kashe sama da dubu dari duk dan na suke kar ali yagane, idan muna waya yakance ina burgesa yaga nagama jamia anma ba ruwana kaina akame, shiru nakeyi don dayasan past dina daba haka ba, nayi gyran jiki sosai na kimtsu, atunanina duk bazai ganeba tunda na suke, abinda bansaniba ko ince mata dayawa basu saniba shine wannan gyran da akeyi its not natural, cusa wancan kimtsa wancan no matter how pure it is, mace tana zuwa da niimanta tun haihuwa, donhaka idan tabari yatafi samunsa bamai wahala bane anma kowa yafison original, nadauka budurci baida wani muhimminci tunda nayi gyran jiki, anma budurci fata ce ajikin mace, idan yafita babu mahaulakin dazai iya sama miki wani, don haka magani ko gyran jiki bazai kwace ya mace ba, saidai yarufe hanya!, ahaka mukayi biki banda wasu kawaye sosai saboda duk sunyi aure nanfa daddy yazubamin kaya na tare agydan mijina aliyu, darenne yakamata ace tazama tafarkona toh anma bahakanba, washegari ali yadda yake ba yabo ba fallasa donhaka saina fara tunanin ko bai ganeba harda adduoina, muna zaune lfy da ali ina service dina yana aiki, saidai abunda ban gane ba shine duk lokacin da ali yakiran yajii inagun service sai yace na bawa kawata daya mugaysa , baidamenba tunda idan suka karbama cewa yske su lura dani, sannan duk lokacin danace zanfita idan kasuwa nace zanje zaikaini yajirani nagama mudawo hatta wani hidiman dangi yana makale nikuma sainaga rashin dacewar hakan, donhaka naxaunar dashi nace karya damu zanna zuwa ko ina, yanuna rashin amincewarsa anma na dage sai yabarni, watarana muna office dinmu yakamata ace naga officerna don yamin sighning wasu papers, anma mutumin baizoba akace sai bayar na yamma, don haka naxauna muka jirashi haryazo alokacin na nemi abun hawa narasa, sai nadauko wayata don nakira ali anma naga ba caji, hankalina yatashi sosai ga magrib tayi, wasu yan batch dinmune zasuyi gyda kasancewar suna girmamani a matsayita ta matar aure sukace bari su saukeni nayi niyyan naki amincewa saidai ganin dare zaimin a gun gashi bakowa yasa nashiga yana ajiyeni a kofar gyda nabude gydan nashiga ali nazaune rike da cup din coke batare da na lura da yanayinsa ba nace dear yau na wahala da kyar nasamu mai kawoni bansamu abun hawa ba, yaja tsaki wacce ta sa najuyo idonsa jajur cikin tashin hankali nace meya faru dear? Ransa abace yace kimin shiru munafuka, azzaluma mayaudariya, iskancin dakikayi awaje bai isheki ba yanzu kin yi aure bazaki dainaba? Aini naji mamaki ashe cutana zaayi aka daukeki akabani, wacce tagama saida mutuncinta wa samari awaje, yanzu wani yakawoki a mota anma zakicemin wai aiki, yanzunnan nadawo agun meyasa ban samekiba, wlh nayi nadaman aurenki , meye amfanin auren karuwa??? idona cike take da hawaye, nace bahaka bane sir, kirifamin baki jahilar banza, kuka nake sosai anma bai kulani ba, tunda ga ranan zaman dadi ta karemin agydan ali, bayacin abincina, baya dawowa gyda sai tsakar dare sannan idan yafara zagina har kakkanina saiyazaga, na zauna zaman hakuri harna gaji daganan na yanke shawaran nanemi takardata, saidai nace barin kira momy naji, ina kuka nake mata bayani tace nanemi izini nazo , dana tambayeshima cewa yayi adawo daga karuwanci lfy, nadai kimtsa da kyar nafita ina xuwa gyda na tarar amina ma tazo, tayi bul abunta ga ciki ajikinta sainaji hawaye nazubomin nace amina hankalinki a kwance ko? Tace adda ambar kinyi kuskure tun farko dakika dau wannan rayuwar, ganinan dai duk kawayena suna cemin ban wayeba, anma meye rashin wayewan dasuke nufi? Rashin harka da maza, zuwa party dasauransu na yadda, saboda a tunanina shine asalin jahilci. Meye wayewa kina harka da maza? Kowani namiji yarainaki? Yasan hawanki yasan saukanki? Ina wayewa aciki kowani namiji yasan bangare najikinki? Ina wayewa aciki namiji yataba jikinki wanima gobe yaxo yataba? Wannan shine jahilci. , ki kama kanki kizama mace on ur own, be d boss of ur own life, karki kuskura wani namiji yaga saukanki, neva b a victim, do not cry for a guy, it would be used against you, karki bari namiji yaga downfall dinki, donkinason namiji bashine zaiza yayi dake kaman akuya ba, yayi ruling dinki kaman bakida yanci. Balle harki biye mishi waidon kiyi ladabi da biyayya, inata kuka amina na bayaninta nayi nadama sosai inata kuka momy ma kuka take, tacemun kiyi hakuri bakomi, yanzu ki koma da ubangijinki kawai anma maganan ali yasakeki adda baitasoba, kizauna kiyi hakuri laifin da kika shuka kike girbawa, ba kedai ba, kowacce mace me irin halinki dole ta fuskanci tashin hankali a rayuwanta, baaayiwa Allah wayo, nayi kuka sosai, momy da amina suka bani shawaran nazauna a gydan ali duk hakurin aure ake, kowani aure dakika gani hakuri akeyi, momy nafada tana kuka tace daddynku duk da baku taba ganin tashin hankalinmuba bakusan me nake cikiba, anma nayi hkr nazauna shiyasa kuka tsinceni haryau, dadynku baya zama siyasansa yafi masa mu, momy na kuka tana bamu tarihinta da daddy yadda tasha wahala sosai, gashi dan siyasa yanmata suka tsaya mata agaba, dasunan partners, nanma amina tadaura dacewa ko hafsat dakike fada kinji lbrnta? Nace a a, tace toh hafsat haryau batayi aureba, last a makwabta nakejin labari tabi mijin makwabciyata kuma kanjamau take dashi, hauka ne yafara damunta domin kuwa shaye shaye yamata yawa, ambar ki gode Allah kin nutsy rayuwanki tacanja so use ur time kiyi hakuri kizauna har Allah yadawo miki da hankalinshi, haka na hakura nakoma nacigaba da zaman gydan ali, abu sai gaba yake har nazo nafara lura ali neman aure yake, tunda nake bantaba shiga tashin hankali da tsanan kaina ba da nadama sosai akan abubuwan danayi abaya sosai, haka inaji ina gani abdul ko fadan kishiya bai kawomin ba, momy ce tazauna tahadamin kaya akwati set hudu, sannan tacanjamin kayan daki, ranan mungama gyra daki nida amina nace amina nifa tunda muka fara rikicinnan baya saurarona gashi zai kara aure nasan gatana takare, amina tsyi dariya tace bai kareba yaruwa auren shine kadai hanya kisa musu ido karki tanka musu. Sannan ki gyra jikinki sosai idan momy zasu tafi london kice tasiyo miki kananun english wears, sannan ga littafin girki na kawomiki. Adda mikewa tsaye zakiyi ba boka ba malam, mijinki nasonki donhaka ki kokarta duk abinda zai jawo zargi a tsakaninku ki kawar, nace amina toh mufara da gyran jikin naji wata a gydan biki kwanaki tana cewa akwai hadin dawo da budurci, amina tayi dariya tace adda babu, duk duniya babu mahaulakin dazaice miki maganan gyran mata zai dawo miki da budurci karyane ko shi wayene, sannan idan mai siyarwa ne toh sunfadane don kawai kisiya kayansu, maganin gyra saidai ya tsukeki, don budurci kam karyane don budurci fata ne ajikinki, saidai maganin gyra yamiki maintainin jikinki, toh idan yana dawowa da budurci nawa kika kashe da amarcinki? Almost 200,000 anma meyasa budurcin baidawo ba har ali yagane? Sannan bakowani maganin gyra zaki dauka ki cusa ajikinki ba, ki tabbatar da asalinsa, donhaka dakanki ma zaki iya gyra jikinki, kisiya miski, gabaruwa, ganyen magarya da lalle, saiki dage da shan fruits musamman kankana, wadannan kadai inkin rike ba ruwanki da asaran kudin gyran jiki, domin specified ne daga matan zamanin annabi, ga girki karki kuskura ki maimaita abinci a sati. Kaya kuwa sai inda karfinki yakare, habawa nan fa muka dukufa, amina ta tafasa ruwan ganyen magarya da gabaruwa tasa nashiga ciki na zauna tace nayi na sati, ga shafa miski idan nafito, saikuma shan kankana, sai inyi blendn dinshi da dabino da mazar kwaila insa madara insha, tamin hadin mayukan jiki tuni nayi bul, nayi shirin amarya, ga dinkuna na agun tela, satin biki sukayi abinsu nima ba yabo ba fallasa, nadan sake, anma abun cin fuskan shine nida ali watanmu sha daya anma harya kara aure, aka kawo amarya tana site dinta, daredare ali yakiran yazaunar damu dukka biyu yayi waazi sannan suka wuce daki, ranan kasa bacci nayi, kwana nayi ina sallah saidai asuba ne bacci yadan kwasheni, karfe bakwai naci kwaliyya taf shaar dani nafito nashirya kumalo, na ajiye musu nakoma daki ali da amaryarshi basu fito ba sai karfe goma, anan suka karya nafito na gaysheshi ya amsa sai wale baki yake, itakuwa saiwani fici fici take da ido, nan nakare mata kallo tas, shikuwa kaman munafiki, ina zuwa daki nazauna lallecin fuska yarasa wacce zai dauko min sai riri? Wacce mukayi secondry da ita? Wannan yar iskan yarinyan? Toh ai angudu baa tsira ba, munafuka jiya tana ganina ashe shiyasa dayake waazi tarufe fuska cikin gyale maima zaiyi da ita? Kyau dai da komi ba abunda banfitaba, naja tsaki na cigaba da goge daki, haka har sukayi sati, ninake girki bai damenba, randa zan karba ba kunya tayi sallama tazo dakina bayan mungaysa wai ambar nazo rokan alfarma ne, don Allah kitaimaka ki sayar min da kwananki, nayi dariya nace kiyi hkr, nima ina bukatar mijina, haka tamike tafice, dayadawo ma yana kwance a falo ina daki, hakadai harya fita dama kwana bibbiyune, , ganin haka yasa nazauna nayi tunani barikinta takeyi a gyda yadda taga dama, idan suka fara wasu surutai tashi nake nabar musu gu donhaka na yanke shawaran nima zasu ga nawa fannin lokacin momy tadawo tasiyomin wasu arnan english wears. Na jerasu a wardrope, nan nayi shirin aiki, da sassafe sainayi wanka naci kananun kaya, wataran mini skirt da top, wataran wando gajere wataran bomshot inci kwaliyya inyi paking gashina infeshe jikina da turaruka, munacin abinci ina daddana wayana ina ci cikin kissa ina lumshe idona, takasan ido ina hankalce dashi sai hadiyan yawu yake, ya kallen yajuya, dazatan nagama innatashi tafiya nanfa zanzage na juya jikina sosai, ga kananun kayannan sunzauna, inje kicin ingama abuna, inje falo, ko yazo yazauna sai insa ear piece a kunneta ina jin radio, anma duk ina hankalce dashi, riri kuwa haushi takeji sosai saboda bayadda ta iya dani jikinta nanan kaman na maza kotasa kayan bazatayi kyauba sannan batada gashin yin yanda nake, kwata kwata bata da kyau da charisman dazata hada kai dani donhaka nayita rayuwata ina sane dasu anma daga ita harshi sasu nake a kwandon shara, musamman shi naga yanzu yafara sake fuska, inyaggani wataran da wani adon sake baki yake , gashi riri ta rasa aina nake siyo kaya haka takarbi kudi agunshi tasiyo enfmglish wears ina kallonta tafara sawa dariya ma taban. Nanfa nacigaba dabasu assighnment, tuni ali yadawo saiti yafara gwadamin maitarsa anma inaaaa ambar jaaa ajikinki, abinda zuciyata kefadamin kenan yadda ya wulakantani gwara nadan jamasa rai duk da cewa nasan m payn for my misteks, kuma inason kasancewa ds mijina anma dole nayi hakuri kullum kwaliyan daban nake, nakoyi kuskurena, nayi nadama kuma kullum ina kara nadama, fatana Allah ya gafarceni abinda na aikata, na lura da son da ali yakemin,hmnn danma ban kaimishi budurcina ba, da ace nakai mutuncina da kimana zaifi haka yawa, bazai taba zargi naba, kullum acikin koyan sabon salon girki nakeyi, zanbashi yaci yakoshi, idan kwanana ne na gyra mishi daki na feshe da turare sannan na wanke mishi toilet bana bari mai aiki tayimin wannan, sai akwanan riri ne mai aiki ke masa hidima, donhaka sainayi usn wannan advantage din, nadawo da tunanin mijina kaina, ran jumaa itace ranar da nayi niyyan mushirya mu daidaita, aikuwa godiya kan godiya da alkawuruka kala kala, nasan adduoi danakeyi ne yasa Allahna yaji tausayina, ahaka nadaidaita da ali komi normal, ina tarairayan kayana kaman jariri, ahaka nasamu ciki riri ma haka , nan muka cigaba da rainon yaran cikinmu duk wani bita da kulli da riri ke hadamun bana kulata, hakan yasa fada baya hadamu, cacar baki ma sai naga dama nake kulata, ahaka wataran naje biki makwabciyata ammata kishiya, nayi mamaki sarai danaga hafsat agun bikin itace kawar amaryar, ta lalace duk jikinta yasake, gashi tana abu kamar marar saiti, ba cikaken hankali kuma haryanzu ba mijin aure ga makarantan tagama anma miji shiru, yanzu ko samarinma zaurawan tadena gani, rokona tayi tayi gafara acewarta ita tayi sanadin rabani da fuad, anma fuad nasona, nayi dariya nace dama can ba mijina bane, kinga mijina muna zaman lfy, taban hkr nan nabata shawara nace tayi nadama ta gyra rayuwanta ko Allah zaijikanta inyaso ko da magidanci ne tasamu, tacemin akwai wani matansa biyu yana sonta anma ita tana tsoron wulakancinsa nayi dariya sosai sannan nace ai rayuwar dakika dauko dolene namiji ya wulakantaki shanyewa zakiyi kiyi hakuri kijure, tace bakomi, bayan natafi satin na haihu nasamu na mace, nasa mata suna amina, riri ma ta haihu na mace, tasa mata bilki,nan muka samu dakyar muke dan hada kai, duk da mukan samu sabani wani lokacin anma ba wannan bane damuwata, babban damuwana shine mijina yasoni kuma ya kula dani, alhamdulilah bayan gyran kuskure na danayi, nasamu hankalin maigida na, fuad ina ganin sanarwan bikinsa wata ustaziyan mace yanemo ance tana da hankali banyi mamaki ba tunda dama shidin haka yake, wanda yafiban mamaki shine taslim yar sarkin malamai ya aura ance yarinyan akwai zubyn hadda, naji mamaki kwarai, namiji ba abun yadda ba, su zasu zauna su bata miki rayuwa anma insungama suje sunemo ustaziya, ya ishi mata ishara duk wacce namiji ke binki don jikinki ya ke yaruwa kisani yana samun abunsa zaiyi gaba bazai aureki ba, zainemo yar mutunci da kamala, shawara ta rage name shiga rijiya, anan nakawo karshen labarin budurcina yancina, (don Allah wannan labarin hadawa ko ince kirkira nayi it has nothing to do da rayuwan wani, but if plx yazo mistakenly daya da rayuwar wata, am sorry, don anfara bina privately ana min wasu illegal tambayoyi,and please masu copy and paste, idan zaku tura kuna cire numbana don Allah, ana yawan adyn dina tahaka) muhadu a labarina na gaba wato A SANADIN HAKURI An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci

Chapter 2 of 3