NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 72 of 84

gaban Mata, y'an ci ya d'ara bauta, freedom writters._ ) *( F.W.A)🖌* *WACECE NI?* *(SANADIN KUKANA!)* _typing✍🏻_ *Mrs Dr M.A...* *56-58* Cike da tsananin farin ciki yakeyiwa Allah gdy ya miqe da sauri zai fita yaji muryar Ra'isah tana cewa “Sweet Zahrah ta haihu ko?" Juyowa yayi ya kalleta sheqeqe yaja wani uban tsaki ya fice daga dakin ya dauki motarsa ya nufi gdansa, ayau dinnan bazai kwana a 9ja ba sai a Lebanon. Yana zuwa kayansa ya rinqa hadawa bayan ya gama ya shiga yayi wanka ya sake fitowa yayima Emmah mgnyazo yajashi sai airport, babu bata lkc yayi duk wani abu daya dace Allah ya taimakeshi akwai me tashi lkcn aka bashi set, kasancewar yammace suka tashi shigar dare yayi kai tsaye gdan kakanninsu ya nufa yana shiga yaji me gadin yana masa murna hakan ya tabbatar musu da cewa matar tasa tana gdan kutsawa yayi parlourn ya tadda Grandma a zaune itada autansu Ummuh sai Mu'azzam da yaketa qiriniya da tafiyarsa da bata gama qwari ba. Baiyiwa kowa mgn ba ya qarasa inda dansa yake ya daukeshi ya rungume yana dariya yace “Babana shine ka tafi ka barni cikin mawuyacin hali ina mamanka da qanwarka?" Dariya yaron yakeyi harda rufe fuska irin nasu na yara dukka parlourn sukayi dariya, Ummuh dake fitowa daga dakin da Marwah take ta zuba masa ido cike da mamakin inda yaji lbrn haihuwar fuskar jaririyar dake hannuta ta kalla ta kalli fuskar uban nata yarinyar kamar hotonsa kamar har tayi yawa hatta yatsunta da komai nata irin na ubanta ne, ajiyar zuciya Ummuh tayi ta rabashi zata wucce yayi saurin ajiye Mu'azzam ya matsa yace “sannu da qoqari Ummuh ashe nasamu qaruwa Everlasting ta haihu amma shine baki fadamin ba yanzu da Abuha bai fadamin ba shikenan bazan sani ba saikace ba yata ba" Murmushin takaici tayi ta zauna akan kujera batare da tace mashi komi ba ya matsa yasa hannu zai dauki Babyn ta ture hannusa tace “ubanta bai yarda ka taba masa yaba" dagowa yayi a firgice ya dubeta zaiyi mgn ta nuna masa hanya tace “kada ka fadamin komai Bunayyah jeka banson ganinka fah" miqewa yayi zuciyarsa na mugun radadi ya nufi dakin da yaga Ummuh ta fito ta daka masa tsawa tace “kada ka kuskura ka shiga dakinnan ba hurumin ka bane kaje ka dameta da rawar kanka tana fama da kanta" baiko tsaya yaji abinda zata qarasa fada ba ya tura dakin ya shiga ya mayar da qofar ya rufe. Tana kwance a saman gadon ta zubawa silin idonta da yake cike taf da hawaye cikinta nade da bandeji, matsawa yayi da sauri gabanta ya tsuguna a qasa daidai fuskarta ya dora hanunsa saman cikinta ajiyar zuciya taja me qarfi lkcn data shaqi qamshin turarensa ta juyo da kanta idanunta ya fada cikin nasa ya lumshe idonsa tare da sauke numfashi me qarfi yace “ashe aiki akayi miki everlasting meyasa kika boyemin abinda ya kamata na sani yanzun da Abuha bai fadamin ba da shikenan kema bazaki fadamin ba kin biyewa su Ummuh kina fushi dani akan wannan dan qaramin dalilin ba laifina bane kiyimin adalci Zahrah bakeba duniya ma ta shaida inasonki wlh bacin raine yasa na furta miki abinda na furta please everlasting don Allah ki taimakeni kinji" More comments😍 More typing😍 *Mrs Dr M.A...✍🏻* [3/17, 9:18 AM] MRS M.K.D: https://www.facebook.com/Freedom-Writers-Association-110039363936693/ https://www.facebook.com/Freedom-Writers-Association-110039363936693/ *FREEDOM WRITTER'S ASSOCIATION.* 📕🖊️ ( _Y'anci don cigaban Mata, y'an ci ya d'ara bauta, freedom writters._ ) *( F.W.A)🖌* *WACECE NI?* *(SANADIN KUKANA!)* _typing✍🏻_ *Mrs Dr M.A...* *59-60* Numfashi ta sauke tare da qoqarin miqewa yayi saurin kai hanunsa zai dagota ta daga masa hannu da sauri tace “kada ka tabani Marwan bana buqatar kowanne irin taimako daga gareka na roqeka don Allah ka ficemin anan wlh banason ganinka" yanda take mgnr ne cikin zafin rai yayi mugun razana shi bai taba kawowa a ransa itama tana fushi dashi haka ba abinda ya dauka kawai su Ummuh ne suka hanata nemansa. Bai gama wannan tunanin ba ta kuma cewa “na dade da cireka a cikin rayuwata na dade da mantawa da wata halitta irinka da take rayuwa a doron qasa kuma na dade da fara nadamar rayuwa da mutum mara uzuri mara imani meson kansa irinka kuma kullum cikin fadawa Allah yabimin haqqina ya sakamin qazafin da kayimin na zina bazan taba yafe wannan mugun tabon da kasamin a zuciyata ba don Allah ka fita Marwan ka ficemin daganan banason ganinka bakada wata alaqa da yata yadai tawace kuma na yarda zan nema mata uba bada dadewa ba ubanda bazata taba tuhumata akan kasancewarsa uba a gareta ba" Kalamanta iyakar lugude haka sukeyiwa zuciyarsa miqewa yayi ya haura gadon ya kamota ta fusge ta miqe da sauri ya biyota yana cewa “tsaya kiji Zahrah..." Bude qofar tayi ta fice daga dakin da sauri ta fada dakin granny ya tsaya sororo yana kallonta harta rufo qofar yayi murmushi tare da cewa “zaki shi
🏠