NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 70 of 84

tana kuka, durqushewa yayi a gabanta ya riqo hanunta zaiyi mgn ta katseshi tace “tashi ka bani guri Marwan wlh zan iya illataka na tsani ganinka Marwan ka ficemin daga gdannan" dagowa yayi idanunsa kamar garwashi yace “don girman Allah Ummuh kada kiga laifina adalcin da zan iya yiwa Zahrah kenan..." Miqewa tayi tace “nasani ai banga laifinka ba dama" wuccewa tayi ta shige dakinta ta datso ta qyaleshi miqewa yayi ya nufi dakin Marwah a kwance ya tarar da ita ta qudundune da blanket tanata ajiyar zuciya wani tausayinta yaji ya ratsa zuciyarsa ya matsa a hankali ya zauna a gefen gadon ya dagota tayi saurin janyewa ta miqe a fusace ta nufi bathroom yayi saurin janyota yace “ki tsaya kiji abinda zan fada mik..." Angajeshi tayi ta fice daga dakin da gudu ta shige kitchen ta datse qofar binta yayi da kallo tare da cije lebansa ya juya ya fice daga gdan Saida Ummuh taji tafiyarsa sannan ta fito ta nufi kitchen din ta kamota tace “kinyimin daidai don Allah ki cire damuwa a ranki ba kanki aka fara ba uwar muminai ma Nana Aisha (R.A) anyi mata irin wannan qazafin qarshe munafukai sune sukaji kunya kema insha Allahu duk wanda yakeda hanu a rabaki da mijinki shine zaiji kunya jibi insha Allahu zan kaiki Lebanon kiyi zamanki acan ki huta da wannan banzar rayuwar" Itadai batace komai ba haka suka yini har zuwa dare da Abuh ya dawo Ummuh ta sanar dashi abinda yake faruwa shima ransa ya baci matuqa musamman da yaji furucin da Marwan yayi wai cikin jikinta ba nashi bane bai iya cewa komai ba saboda baqin ciki kuma bai nemi Marwan din ba. Washegari da wuri yazo gdan saboda kwana yayi bai rintsaba abubuwa uku suke damunsa takaicin kama matarsa da yayi da wani qato da takaicin sakita da yayi da takaicin qin saurararsa da iyayensa sukayi da kuma takaicin Kiran da Ra'isah tayi masa wai lallai saidai ya cikewa Marwah saki uku kuma yaje a gwada jininsa idan bata liqa masa wani ciwon ba, yana zuwa ya tarar da Abuh a parlourn yana duba jarida ya zauna suka gaisa shiru ta ratsa kafin daga baya ya dago yace “Ummuh fah Abuh?" Kallonsa yayi yayi murmushi yace “tayi tafiya" dagowa yayi da sauri cikin faduwar gaba da baisan dalilinta ba yace “matata da dana fah?" Kallonsa Abuh yayi yace “matarka kafini sanin inda take da kuwa bansan kanada shi ba Mu'azzam da wanda zaa haifa nan gaba duk ba naka bane munyi musu uba" Kallon Abuh yakeyi amma ya kasa furta komai miqewa Abuh yayi yace “zan hau sama inason hutawa idan zaka fita ka rufe mana qofar" binsa yayi da ido har ya haye saman ya miqe a kasalance ya fice gda ya koma ya shiga dakin dayasa wannan mutumin yana shiga mutumin ya fara kuka yana durqushewa yace “wlh Alh biyana akayi akace nazo na shiga dakin matarka Ostin shine ya nunamin dakinta Hajiya bata taba ganina ba" matsawa yayi gabansa ya damqi wuyansa yace “waye ya turoka kuma nawa aka baka saboda ka tarwatsamin farin cikina?" Shaqa yayi masa bata wasa ba Saida yaga ya galabaita sannan ya sakeshi ya zaro bindiga ya sanya masa a maqogaro mutumin yayi saurin cewa “Haj...Hajiya Ummah ce ta sanyani tace wannan din kishiyar qawarta ce wlh dubu ashirin suka bani"............. More comments😍 More typing😍 *Mrs Dr M.A...✍🏻* [3/14, 8:12 PM] MRS M.K.D: https://www.facebook.com/Freedom-Writers-Association-110039363936693/ https://www.facebook.com/Freedom-Writers-Association-110039363936693/ *FREEDOM WRITTER'S ASSOCIATION.* 📕🖊️ ( _Y'anci don cigaban Mata, y'an ci ya d'ara bauta, freedom writters._ ) *( F.W.A)🖌* *WACECE NI?* *(SANADIN KUKANA!)* _typing✍🏻_ *Mrs Dr M.A...* *53-55* Wani mugun mari ya zuba masa jikinsa na rawa ya fice daga dakin da sauri ya koma cikin gdan ya zube akan gado yana dafe da kansa yace “ya Salam wannan wacce irin masifa ce me Ra'isah take nufi da rabashi da matarsa wannan wacce irin qaddara ce" dare yayi sosai saboda haka ya kwanta amma fa bai iya rintsawa ba da asuba ya fice daga gdan ya nufi gdansu wannan ma Abuh ne kadai a gdan suka gaisa yace “don Allah Abuh kayi hqr wlh bacin raine nayi kuskure dana yanke hukunci cikin fushi..." Daga masa hanu Abuh yayi yace “babu wata damuwa a cikin lamarinka da Zahrah face abinda Allah ya hukunta Allah bai qadarta zama na har abada tsakaninku ba ka godewa Allah ka rabu da mazinaciya wacce tayo ciki a waje ta kawo maka gda" toshe kunnensa yayi saboda kalaman na Abuh sunyi masa nauyi zuciyarsa na tafasa. Miqewa Abuh yayi ya fice daga parlourn zuwa gurin da yake training duk safiya, haka ya qari zamansa a gurin har ya gaji ya miqe a gajiye ya koma gdansa ya shige dakinsa ya kulle ya kwanta yanata kiran wayar Marwah da Ummuh amma taqi shiga zuciyarsa tana qara daukar zafi ji yake kamar yayi tsuntsu yaje ya ishesu a duk inda yake, yananan kwance kiran Ra'isah ya shigo wayarsa yana gani har tayi ring dinta ta katse bai dagaba duk yanda yake tunanin bacin ransa ya wucce haka zuciyarsa har bugawa
🏠