NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 69 of 84

cigaban Mata, y'an ci ya d'ara bauta, freedom writters._ ) *( F.W.A)🖌* *WACECE NI?* *(SANADIN KUKANA!)* _typing✍🏻_ *Mrs Dr M.A...* *50-52* Da gudu ya qarasa gaban mutumin ya sanya hanu ya damqi wuyansa ya miqar dashi ya hada kansa da bishiyar da take gurin ya sake jifa dashi a fusace yace “kasamin shi a waccan dakin horon ka hada masa shocking harsai ya fadi abinda ya kawosa gdana har dakin matata waye ya turoshi. Juyawa yayi da koma ciki zuciyarsa na wata irin bugawa kamar zata faso qirjinsa ya sake haurawa saman ya taddata kwance inda ya barta wani irin tuquqi zuciyarsa takeyi masa duk yanda yakeso yasa a ransa ba ita ta kawoshi ba ya kasa dubada abinda Ostin ya fada masa cewa “hajiya tayi baqo" inkuwa hakane to tabbas tasan da zuwanshi ga qarin wata hujjar daga kalaman mutumin da yake cewa ta fada masa mijinta baya kusantar ta, idan ba itan ta fada masa ba waye yasan baya kusantarta? Juyawa yayi ya fice zuciyarsa na tafasa ya shiga dakinsa ya zube a tsakar dakin dafe da qirjinsa shi kadai yasan irin zafin da qirjinsa yakeyi masa kwarto a cikin gdansa dakin matarsa da yafiso a duniya diye da kowacce mace hawaye suka zubo masa yana girgiza kansa yanajin wani qunci yana mamaye kowanne kusurwa na jikinsa da gaske ne wannan qazamin mutumin ya kwanta da Zahransa meyesa tayi masa haka meyasa zata ha'inceshi. Miqewa yayi yana layi kamar zai fadi ya shiga dakin nata baba zulai ya tarar tana shafa mata ruwa a fuskarta tana hawaye saboda wannan sharrin ya girmi tunaninta matuqa tayi mamaki tunda suke da Marwah bata tabayin baqo namiji ba ko a Hira bata taba cewa da ita tanada wani namiji data sani ba bayan Colonel Marwan ba ajiyar zuciya ta sauke me qarfi bakinta yana furta “innanillahi wa innah ilaihirraji'un" hawaye nabin kwarmin idonta, tsallaketa yayi ya shiga cikin dakin ya dauki dansa ya tsaya a kanta yace “kin munafurceni kin ha'inceni bantaba tunanin haka daga gareki ba Zahrah kaico da bamu muka tarbiyyantar dake ba wannan ba tarbiyyarmu bace kina da aurena akanki kike neman wani namijin me kike nema Zahrah meye banayi miki wacce buqata kike da ita da tafi tawa dahar kike neman wani kin cuceni Zahrah Allah ya isa tsakanina dake qato har gidana" Dakatawa yayi yaja fasali kana ya share hawayen idonsa yace “bazan taba yafe miki ba Zahrah kije gakinan ga duniyar nan bazan iyaci gaba da zama da mazinaciya irinki ba sannan abu na qarshe idan kin haihu ki nemawa danki uba bani bane ubansa Mu'azzam nasan danane amma wannan cikin ba nawa bane" yana fadin haka ya juya zai fita saura kadan suyi gware da Ummuh ya kauce yabata hanya ta qarasa gaban Marwah da takasa furta ko kalma daya sai rawa da jikinta yakeyi kalamansa sunayi mata yawo a kwanya, rirriqeta Ummuh tayi tace “ke ki nutsu shiga nutsuwarki sai me meye dan kin rabu da wannan alaqaqai din dama ai ba ajin aurenki bane qaddara ce ta hadaki dashi kaje Bunayyah kaje Allah ya sakawa wanda aka zalumta ka turamin a waya ka saki matarka qanwarka saki daya ka kyauta amma inaso kasan wani abu ni nasan Allah bazai taba hadamin ku duka iri daya ba sama ace Zahrah tana neman maza to da kake mata wannan babatun laifin waye kuma horon waye komai tayi kaine sila kuma a gurinka ta gani wacce irin macece baka nema ba da aurenka sai ita dan anyi mata sharri?" Dagowa yayi ya zuba idonsa akan Marwah da sai yanzu ta samu damar sakin wani kuka me ciwo sai yanzu ta tuna ashe zarginta yakeyi da zina a fili tace “ hasbunallahu wa ni'imal wakil wlh Ummuh ban aikatab...." Rufe mata baki Ummuh tayi tace “kin ma aikata Zahrah kin aikata kuma cikin mu munaso tashi kibar masa gdansa" juyawa yayi wasu hawaye sunabin kuncinsa zai fita ta zabura ta miqe da sauri ta janyo loccar ta dauko qur'ani cikakke tace “wlh tallahi billahillazi La'ilaha illah huwa ban aikata abinda mijina kuma yayana yake zargina dashi ba Allah kaine shaidata Kaine zaka wankeni Allah..." Rufe mata baki Ummuh tayi ta qwace qur'anin tace “bakida hankali wannan dan iskan zakiyiwa rantsuwa dan ya yarda dake kada Allah yasa ya yarda dake koma ya kike ni inasonki Zahrah matsawa tayi tasa hanunta ta sharara masa mari ta fuzge Mu'azzam da yake hannunsa tace “baka isa mubar maka danmu ba kaje ka haifa da matar sonka shima ba naka bane zamu nema masa uba" Tana fadin haka ta fuzgi hannun Marwah suka fice tana waiwayensa tana hawaye shikam ya tsaya kamar mutum mutumi ya kasa motsa ko yatsansa zubewa yayi a gurin yayi zaman yan bori maganganun Ummuh sunayi masa yawo a kwanyarsa rabawa baba zulai tayi ta gefensa ta wucce ta sauka qasa ta fada saman kujerar ta fashe da kuka tana fadin “Allah ka biwa marainiyarka haqqita wannan zalumcin yayi yawa" ta jima a gurin tana kukan tausayin Marwah kafin taji saukowarsa idanunsa sun kada sunyi jawur ya fice daga gdan ya shiga motarsa ya fice. Gdan nasu ya nufa shima sanda yaje ya tarar da Ummuh a parlour tayi tagumi rungume da Mu'azzam a jikinta
🏠