yi tana qoqarin hadiye kukanta tace “kullum yana zuwa bai jima da fitaba yanzun ma Dana kirasa cemin yayi yaje wani aiki sai ya dawo da dare zaizo" murmushin takaici Ummuh tayi saboda tanada masaniyar kwanakin da yayi rabonsa da gdan ta samu lbr a gurin baba Zulai amma batason cika bincike tunda mace da mijinta ta boye laifin abinta kai idan ka zaqe sai kayi laifi.
Kama hanunta tayi tace “ok muje kuyi sallama zasu tafi jini yakeson tafiya kiyi qoqari gobe kizo ki yini ku danyi hira kinji Allah yayi miki albarka"amsawa tayi da amin suka dawo parlourn ta zauna kusada mahaifin nata kaunarsa tana ratsata tanajin wani sanyi a zuciyarta ashe dama haka yaya sukeji game da iyayensu ashe shima I sunyi kewarta hawaye ne suka qara zubo mata maganganun Colonel Marwan suna dawo mata “ubanki kikace ba ubana ba..." Hawayen da take hadiyewa ya zubo mata tayi saurin qasa da kanta daga Ummuh har Abuh sun fahimci akwai damuwa a tattare da ita miqewa sukayi sukayi mata sallama tare da alqawarin zatazo goben.
Tayi tunanin zai shigo da daddaren amma ga mamakinta sai tajishi shiru bai shigoba har suka rufe qofarsu suka kwanta ranar tayi kukan da ta dade batayi ba ga jiri da yake damunta data miqe hakadai ta rinqa daurewa, cikin daren ya kirata agogo ta duba taga 12:30am ta daga ta kara a kunnenta tayi masa sallama bai amsa ba sai cewa yayi da ita “kin hadani da iyayena kinji dadi to bari kiji na fada miki bawai iyayena suke aurenki ba nine nake aurenki sanda ma naje na daukoki a wannan gdan da kika rayu na taimaka miki na aureki iyayena ma basu san dake ba saboda haka ki nutsu ki gane kanki wlh bazan dauki iskancin kai qarata gurin iyayena ba ki dawo cikin nutsuwarki aurenki din banza da wofi uwarme nake qaruwa da ita a aurenki"
Kashe wayar yayi ta ajiye wayar cikin sanyin jiki tace “waini meye yake faruwa dani ne me nayi masa waye ya fada masa ni wanne mutum na fadawa?" A wannan daren dai bata iya rintsawa ba.
Da safe data tashi ma da ciwon kai ta tashi saboda haka batako sauko daga saman bata sake jan bargo ta rufa wajen goma yazo gdan dansa ya dauka a parlour yanata wasansa ya cillashi sama ya cafe yana dariya shima yana dariya suka haura saman ya murda dakin nata ya shiga ya tsaya akanta tana kwance qudundune saman gadon bacci ya fara daukarta saboda zazzabin data kwana dashi zama yayi akan stool din mirrow din ya sauke yaron yaje ya haura samanta ya bude fuskarta ta bude idonta a hankali ta kamoshi jikinta da zafi zau tace “ka kyaleni junior kaji kwanta kayi bacci" saukar muryata yaji har tsakiyar kwanyarsa yace “ki tashi kisa kayanki muje kuyi sallama da Abuha gobe zai tafi"
More comments😍
More typing😍
*Mrs Dr M.A...✍🏻*
[3/13, 10:03 AM] MRS M.K.D: https://www.facebook.com/Freedom-Writers-Association-110039363936693/
https://www.facebook.com/Freedom-Writers-Association-110039363936693/
*FREEDOM WRITTER'S ASSOCIATION.* 📕🖊️
( _Y'anci don cigaban Mata, y'an ci ya d'ara bauta, freedom writters._ )
*( F.W.A)🖌*
*WACECE NI?*
*(SANADIN KUKANA!)*
_typing✍🏻_
*Mrs Dr M.A...*
*48-49*
Dagowa tayi da sauri ta dubeshi shima ita yake kallo ta sauke ajiyar zuciya tare da cewa “ina kwana" bai amsaba sai miqewa da yayi ya fita yace “kada ki batamin lkc inada abinyi zankai matata airport zata tafi Rasha" jikinta a sanyaye ta miqe ta shiga bathroom tayi brush ta fito ta dauki doguwar rigarta ta zura ta dauke mayafinta ta yafa ta fito yana tsaye har ya quta saboda takaicin jiran da yayi mata.
Tana fitowa ya zafga mata hararar da saida yayan cikinta suka juya ya fuzgi dansa dake hanunta ya fice ya shiga motar itama ta fito ta bude ta shiga yaja a guje suka fita ya nufi gdansu Ummuh duk bacin ran da take ciki tana shiga gdan sai taji ya goge.
A parlour suka iskesu tana zuwa ta shige jikin Abuha tana dariya shima murmushi yayi yace “Bintun kina lfy ya jikana?" Shigowar Colonel Marwan ne yasasu dagowa suka kalleshi ya qaqalo murmushin da baikai zucci ba yace “jiya bata barni nayi bacci ba har mafarki ta rinqayi da ku shiyasa nace yau asubanci zamuyi muku" kallonsa takeyi da tsananin mamakin yanda ya karkace yake sharara qarya a gabanta itama Ummuh shi take kallo tace “aikuwa kayi qoqari sosai Bintun ya jikinki"
Murmushi tayi tace “wlh Ummuh zazzabin dare yasani a gaba yau kinga harda ma na safen yanzun ma a kwance nake yace na taso muzo" taba jikinta Ummuh tayi taji zafi zau tace “jiya ta hanaka bacci amma hakan baisa ka fahimci batada lfy ba ko?" qasa yayi da kansa cike da kunya yace “dama idan muka gama danan zamu wucce asibiti" qwafa tayi sukaci gaba da hirarsu shi hankalinsa yafi karkata wajen yiwa dansa wasa inda ita kuma take kwance jikin Abuha tanata zuba masa shagwaba. Miqewa yayi da Mu'azzam a jikinsa ya fice.
Basu dawoba sai dare sosai lkcn Mu'azzam yayi bacci sukayi sallama da Abuha ta tafi akan cewa zasuzo da Ummuh, suna zuwa gda