NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 63 of 84

yace “ki shiga ki gyara komai na gdan anjima zata dawo" gdy tayi ya juya ya fice bai bata lkc ba ya dawo da kayan abinci aka jibge a store ya kuma fita yanayima dansa wasa suka sake komawa gdansu Ummuh. A parlour ya tarar dasu dukkansu har Abuh Marwah tayi matashin kai da cinyar Ummuh dawowarsu kenan daga gdan marayun sunje an basu bayanin zuwan Marwah gdan, sunata hirarsu gwanin dadi Marwah tanajin wani sanyi a ranta lkc zuwa lkc tana share hawayen gdy ga Allah daya nuna mata danginta yau har taji muryar mahaifinta a waya duk da bayajin Hausa saida turanci suka gaisa yana kuka yana godewa Allah daya kawoshi wannan lkcn yana cewa dama yanaji a jikinsa Zahransa bata mutu ba. Ummuh ce tayi masa alqawarin bazata koma gdanta ba harsai tazo taga danginta nan ya qara cika da mamaki Abuh ne yake fada masa ai matar MARWAN ce wadda ta haihu kwanaki ya qara jinjina lamarin ubangiji wani abun saidai ubangijin badai mutum ba, shigowarsa ce tasasu dagowa idanunsa ya sarqe cikin ns Marwah yanajin wani irin bugun zuciya gabadaya kunyarta yakeji da haushin kansa akan abubuwa da yawa da suka faru a baya amma maimakon yaga ta nuna masa alamar bacin rai sai yaga tayi murmushi ta miqe ta nufosa ya zubawa qirjinta ido yana hadiyar yawu. Miqa hannunta tayi ta dauki Mu'azzam yanata Bangale mata baki tace “ina kakaimin shi tun rana gashi yanzu har dare yayi" murmushi yayi ya janyota jikinsa da sauri ya rungumeta ita da dansu yace “inasonki everlasting don Allah kiyimin adalci kada ki hukuntani akan abinda ya faru a baya kinji?" Zuciya taja tare da janyewa ta zauna a kujera shima ya zauna Ummuh ta tashi zatabar gurin yayi saurin cewa “Ummuh yau Zahrah zata koma dakinta an gama aikin harma na zuba komai yanzu haka na baro Baba Zulai tana gyara mana gdan" Wani banzan kallo ta watsa masa tace “ai Kaine kake da kanka bamu muke dakai ba amma ka manta cewa munada haqqi akan ita Zahrah saboda haka ban shirya mayar da ita gdanka yanzu ba..." dagowa sukayi daga ita harshi gabanta yayi muguwar faduwa tayi saurin kawar da kanta saboda Allah ya sani ta tayi missing din mijinta mugun buqatarsa takeyi. Dakewa taketa qoqarin yi kuma sai taji Abuh yana cewa “Bunayyah dadai kayi hqr ankaita Lebanon taga danginta Abuha yace jibi zaizo ka bari yazo idan yazo sai su tafi Qatar din tare yaje ya nunata a dangi daganan kuma sai Ummuh ta wucce da ita Lebanon taga danginta mahaifiyarta" wani yawu ya hadiye yace “nidai na roqeku kada kuyimin haka Abuh wlh akwai matsala don Allah kuyi hqr kubani matata duk inda kukeson taje ni zan kaita da kaina..." dakatar dashi Ummuh tayi da cewa “ai munsan dakai din bamuce ka kaita ba so bamu buqatarka ne a cikin lamarinta ka tsaya kawai matsayinka na miji" idanunsa ne ya ciko da qwallah zuciyarsa na raya masa kodai wani abu Marwah tace yanayi mata? Amma a fili sai yace “ok amma ai zaku bani ita naje na gyara bangarena na gdannan mu kwana acan ko?" Murmushi Abuh yayi yace “aa dauki matarka ku tafi kada kayi mana kuka a gaban danka" shafa kansa yayi yana dariya yace “na gde Abuh Ummuh ta daina sona yanzu so take na mutu ta huta" ba Abuh ba ita kanta Ummuh yanda yayi mgnr saida ya bata dariya, yayi murmushi ya kalli Marwah yace “tashi mu tafi dare ya farayi" ajiyar numfashi tayi ya miqe ya shiga dakin nata ya dauko mata mayafinta sanda ya fito Ummuh tajata daki tabata ruwan rubutun da tasa akayi musu na tsari ita da Mu'azzam tasha sannan ta bata wani tace ta dafawa Marwan din tea dashi ya shanye ta sake bata wasu qwayoyin magani tace ta hadiye zasu dade a jikinta, hakanan ta hadiya tayi mata gdy ta bata turaruka da kayan bacci tsadaddu kuma fitinannu harda zaba mata wadda zatasa a daren yau itadai kunya ta cikata suka fito Abuh dake yiwa Marwan nasiha ya hada harda ita ya sake yi musu sanna suka rakasu har gurin motar suka fita daga gdan dayake babu nisa tsakaninsu sosai saida suka biya ta wani gurin saida kayan ciye² ya siya musu ya dawo ya zauna tare da kissing din kuncinta yace “na matsu najini a samanki Baby Zahrah na yau zanyi kwanan farin ciki da bantaba yiba a rayuwata" Qasa tayi da kanta a kunyace yau tasan ta kade har ganyenta dama ya take qwatar kanta a gurinsa bare an dade baa haduba, batasan sun isa gdan ba saida taji yayi horn ta dago tana qarewa gaban gdan kallo har zuwa lkcn da aka bude da gani basai ka tambaya ba an shirya rayuwa a gdan ta sauke numfashi tare da kallonsa suka hada ido ya daganta gira tare da daukar Mu'azzam da yayi bacci ya fita ya bude mata qofar ta fito ya zagaya baya ya dauki kayan daya siyo miqa hanu tayi zata karba ya janye yace “saurin me kikeyi aikinki da ciki" Sunkuyar da kanta tayi ya wucce yana cewa “ita munafukar kunyar data dawo a daidai wannan lkcn zanyi kaca² da ita a daren nan" suna shiga sukayi karo da Baba Zulai a parlourn takuwa rangada guda tace “ina bayanki uwar gijiyata Allah yaja kwana ya qarawa rayuwa albarka" murmushi Marwah tayi tace “Baba kwana biyu kin daina ziyararmu Junior har y
🏠