ta koma ta tsuguna gaban mijinta tana kuka tanayi masa magiyar ya tashi ya fada mata yanasonta bai tsaneta ba ya tashi yayi Mata alqawarin ba zai qara yi mata gori ba, cikin hawaye Abuh ya bude fregde ya dauko ruwa me sanyi ya sunkuya yarinqa zuba masa a kansa cikin gashinsa zuwa fuskarsa zuwa qirjinsa, ajiyar zuciya ya fara saukewa a hankali ya bude bakinsa yace “kece Zahrah da gaske kece Marwanatu kece Zahrah ta".............
More comments😍
More typing😍
*Mrs Dr M.A...✍🏻*
[3/10, 3:10 PM] MRS M.K.D: https://www.facebook.com/Freedom-Writers-Association-110039363936693/
https://www.facebook.com/Freedom-Writers-Association-110039363936693/
*FREEDOM WRITTER'S ASSOCIATION.* 📕🖊️
( _Y'anci don cigaban Mata, y'an ci ya d'ara bauta, freedom writters._ )
*( F.W.A)🖌*
*WACECE NI?*
*(SANADIN KUKANA!)*
_typing✍🏻_
*Mrs Dr M.A...*
*38-39*
Kukane ya qara cin zuciyarta ta miqe a sanyaye zatabar gurin ya cafko hanunta ta fado jikinsa ya matseta tare da dora kansa saman sumarta yana jero ajiyar zuciya yace “ko lkcn da bansan matsayinki a gurina ba nasoki kamar rayuwata balle yanzu da nasan wacece ke a gurina Ina sonki everlasting tunaninki da damuwar rashinki shine yasani tahowa nazo naji dumin jikinki ko na samu sauqin abinda yake damuna"
Dago kanta tayi da sauri ta kalleshi kawai sai taji digar hawayensa cikin qwayar idonta ta lumshe idonta tare da sake kwanciya a jikinsa tanajan zuciya tanajin ninki qaunarsa a zuciyarta.
Janyeta Ummuh tayi daga jikinsa ta jata suka fice daga dakin yana me binsu da kallo tare da tsananin jin kunyar Marwatuh a zuciyarsa, ya jima a zaune kafin ya iya miqewa ya matsa inda Mu'azzam yake kwance yaron ya girma sosai kamarsa da mahaifiyarsa ta qara fitowa hasken fatarsa ne kawai na ubansa sai hatsunsa, ajiyar zuciya yayi yasa hanunsa ya dauko yaron ya zuba masa ido yana murmushi hawaye na zubo masa yana tuna rabonsa da dannasa tun ranar sunansa gashi har ya shiga wata na hudu dakansa yake tambayar kansa ya akayi hakan ta faru?
Miqewa yayi dauke da yaron yanajan karan hancin ubannasa ya fita dashi ya dauki key din motar Ummuh ya fice, kai tsaye gdan daya gina saboda Marwah ya nufa an zuba komai na amfanin mace a gdan yayi kyau sosai har saman saida ya haura dakuna biyu ne sai wani dan qarami na Mu'azzam wanda aka sanya masa dan qaramin gado na yara, qasanma da daki biyu da alama na baqi ne dana yar aiki iyakar haduwa gdan yayi, yayi murmushi ya juya suka fita gdan Ra'isah ya nufa dansa yana jikinsa da yar tazara tsakanin Nassarawa Layout da Badawa Layout.
Tunda suka taho gabansa yake faduwa hakanan yakejin bayason zuwa gdan yadai rinqa danne zuciyarsa ya isa gdan da Baba Zulai ya fara haduwa takuwa yi tsalle ta miqe tana murna tace “ga jikana yazo gaisheni ga jikana oyoyo" murmushi yayi shima Mu'azzam dake yasanta ya rinqa bangale baki yana miqa mata hanu ta sanya hanu zata daukeshi dadai lkcn da Ra'isah take saukowa daga saman cikin shirinta na fita ta daka mata tsawa tace “idan kika taba shegen dannan a bakin aikinki wlh shashasha kawai da batasan ciwon me kyautata mata ba wannan dan zinar har abin dauka ne"
Tsayawa sukayi sororo suna kallonta harta qaraso qasan da isarta da gadararta ta qaraso gabansa ta nunashi da yatsa tace “Marwan idan ka qara kawomin dannan me kama da yartsana wlh saina dura masa poison ya mutu ka huta nima na huta...."
Bata rufe bakinta ba taji saukar hannunsa a kuncinta tayi baya ta fada kujera ya bita ta dora qafarsa a qirjinta ya nunata da yatsansa yace “ki shigo hankalinki akan matata da dana idan ba hakaba zakiyiwa kanki asarar aurenki kada ki qara sheganta min dana dan sunnah ne me asalin da baki dashi"
A matuqar tsorace take shiyasa bata iya ce masa qala ba har ya gama sababinsa ya dauki dansa ya nufi saman ya bude dakinsa ya shiga yaja ya tsaya turus saboda tsananin mamaki tunda ya sanya qafa yabar qasar baa gyara dakin ba, qwafa yayi ya bude bathroom din ya dawo yana bude wadroop ya dauki kayansa kala biyu ya juya ya fice daga gdan tana kallonsa ya watsa mata wata uwar harara ya fice a fusace har yaje jikin motarsa ya juya ya koma yace da Baba Zulai tazo su tafi, da murnarta ta dauko kayanta suka rankaya harda juyawarta tace “to Hajiya saduwar alkhairi"........
More comments😍
More typing😍
*Mrs Dr M.A...✍🏻*
[3/11, 9:35 AM] MRS M.K.D: https://www.facebook.com/Freedom-Writers-Association-110039363936693/
https://www.facebook.com/Freedom-Writers-Association-110039363936693/
*FREEDOM WRITTER'S ASSOCIATION.* 📕🖊️
( _Y'anci don cigaban Mata, y'an ci ya d'ara bauta, freedom writters._ )
*( F.W.A)🖌*
*WACECE NI?*
*(SANADIN KUKANA!)*
_typing✍🏻_
*Mrs Dr M.A...*
*40-41*
Suna fita kai tsaye gdan da Marwah zata zauna nan suka nufa yayi parking ya fita ya bude mata