NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 61 of 84

ar dan ba ta lura da barakar dake tsakaninsu amma kullum ta tambayi marwa cewa takeyi da ita babu komai tsakaninsu suna waya dashi. Babu yanda zatayi da ita hakanan ta qyaleta kullum sai rama Marwah takeyi Ummuh ta rasa dalilin ramar tata har Helin Ummuh ta kira waiko Marwah ta fada mata abinda yake sata rama haka itama amsa dayace ta tambayeta tace mata babu komai. Wata ranar laraba suna zaune a parlourn Ummuh ta dauko wani tsohon hoto tace da Marwah “kinga hotonnan qanwa tace mahaifiyar Baby Zahrah mu biyu tak Grandma ta haifa wannan yarinyar kuma me shekara biyu da rabi itace baby Zahrah sunyi hoton nan ne a ranar da zasu baro Lebanon zuwa 9ja, idan mutum ya mutu zuciyar makusantansa takan samu sukuni Marwah amma mu tamu ta kasa hutawa bamusan dalili ba" Karbar hoton Marwah tayi ta zuba masa ido jikinta ya dauki rawa ta zubawa fuskar yarinyar ido qirjinta ya buga da sauri fuskar hoton da yake gurinta wanda ta dauko a gidan marayu tana yi mata yawo akan wannan hoton katin da sauri ta qara bude idonta tare da qanqame hoton ta miqe da sauri ta nufi dakinta da mugun gudu Ummuh ta miqe ta bita daidai lkcn da Colonel Marwan ya shigo parlourn shima ya rufawa Ummuh baya hoton katin da akace an tsinta a aljihun wandon jikinta lkcn da aka tsinceta wanda suke tare da wani saurayin balarabe da take hasashen babanta ne shi ta dauko da kuma wanda akayi mata ranar da aka kaita gdan marayun ta zube akan gadon tana dubawa tana kuka me tsuma zuciya da sauri dukkansu suka matso dan ganin abinda take kallon ta hada hotunan uku tasa wanda Ummuh ta bata a tsakiya, da sauri Marwan ya matsa ya fara kallon hotunan bakinsa na rawa ya dauki wanda take tare da wannan saurayin yace. “Mar...Marwah ina kika samu hoton nan waye ya bakishi Ummuh duba ki gani hotonane da Baby Zahrah ranar daurin aurena da ita wlh shine Ummuh kigani kingani lkcn tanayi min dariya tana wasa da gashin kaina rugota yayi jikinsa sosai yace “sai... Wlh saikin fadamin ina kika samu hotonnan waye ya baki?" Ummuh ce ta matso ta dauki dayan wanda akayi mata ranar da aka kaita gdan marayu kayan dake jikinta ranar da zasu baro Lebanon sune a jikinta saidai baqi da sukayi suka kukkuje jikinta duk ya kukkuje. Wata muguwar rungume Ummuh tayi mata tace “kadiran ala mayyasha'u wlh tun ranar dana fara ganinki kike rikidemin kamar mahaifiyarki Ukteeh ashe kece Zahrah ashe kece a tare damu tabbas kece wlh kece da gaske kece Zahrah kece da gaske kece Bintun kece Bintu Ukteeh na...." Kuma rushewa tayi da kuka me tsuma zuciya tace “Allah kaine kake zartar da komai kaine kake qaddara komai Allah na gde maka daka qaddaramin ganin yata a cikin gdana matsayin matar dana Allah na gde maka Allah Bunayyah naji dadi yau Ina cikin farin ciki wanda bantaba yiba a rayuwata" Shikam Marwan ya zama kamar mutum mutumi ya kasa motsa komai sai bakinsa da hannunsa da suketa rawa yana nuna Marwah daqyar ya iya cewa “Ba...Baby Zahra...." Baya yayi luuuuuu ya fadi kamar matacce da mugun gudu tayo kansa ta haye jikinsa tana kuka tana girgizashi tana cewa “kada ka mutu Abuh Mu'azzam bani bace banice Baby Zahranka ba nima bansan ya akayi na samu hotunan nan ba ni banida kowa bansan kowa ba ba kowace ni ba face qasqantacciya wadda qaddara ta saka hada jiki da ita har kayi mata ciki ta haifa maka dan da kakejin dama kasani ka zubar dashi kafin yazo duniya, don Allah ka tashi ka cikamin alqawarin da kayimin na zaka nemomin dangina" Shigowar Abuh ne yasa Ummuh dagowa rungume da Mu'azzam tace “dama ka fadamin Abuh nabi a sannu akwai wani boyayyen abu tsakanin yarinyar nan da Bunayyah yaudai gaskiya ta bayyana Marwah itace Fatima Zahrah itace Baby Zahransa ashe bata mutu ba Abuh duba ka gani duba hotunan nan ka gani wlh bana ko tantama Zahranmu ce wannan tabonta yananan wanda Bunayyah ya qonata da ruwan tea yananan a cinyarta lkcn data haihu inayi mata wanka naganshi har saida na tsorata matsawa tayi jikin Marwah ta janye gashinta daya zubo ya rufe qirjinta ta dora hanunta a saitin nononta tace kalli Abuh wannan digon baqin duk wata ya mace da aka haifa a family dinmu tanada shi shima yasamin kokwanto da wasu wasi akan yarinyar nan abinda yasa nayi shiru saboda nasan mahaliccin dayane komai zai iya faruwa Abuh ashe har gori Bunayyah yakeyi mata Innanillahi wa Innah ilaihirraji'un" Numfashi Abuh yaja me qarfi yace “Alhmdllh Sukhaina bai kuka ya kamata kiyi ba kina ganin halin da yake ciki shima fah" jan hanun Marwah tayi tana masifa tace “yaje daganan ma ya mutu na samu yata ta dawo zai gane wlh sai yasan yayi mata gorin nasaba bandama qaddara da rashin gata me zatayi dashi mazinaci dan giya...." Saurin rufe mata baki Marwah tayi ta fuzge hanunta tace “ki daina banaso Ummuh koma ya yake inasonsa don Allah ki daina bayin kansa bane uban danane kuma yayimin alqawarin zai tayani neman dangina niba nice Zahranku ba bani bace ni yar 9ja ce ni baqace ni kukuwa farare ne ku larabawa ne ku" Mamaki ne ya cika Ummuh ta saki hanunta a sanyaye
🏠