ikin wasu wasi da zulumi tun ranar suna da yazo gdan bai qara zuwa ba sai a gurin Ummuh takejin cewa bayan suna da kwanaki biyu ya tafi Ghanan kasancewar ko wayarta baya kira saidai ta Ummuh ita zai tambaya lfyr dansa da duk wani abu da ake buqata.
Ganin kwanaki sunata tafiya ne zuciyarta ta kasa jure rashin jin mijin nata ta daren yau ta dauki wayarta ta fara gwada layinsa duk kiran da tayi masa kusan busy ake ake cewa da ita dole ta hqr ta ajiye wayarta sai bayan awa daya ta sake gwadawa har ta kusa tsinkewa sannan ya daga da wata kakkausar murya yace “hello" a sanyaye tace “barka da da everlasting" ajiyar zuciya yayi yace “ya akayi?"
Wani irin mugun sanyi jikinta yayi tace “a...am dama..." Sai kuma tayi shiru saboda sosai muryarsa ta girgizata rabon da taji yayi mata mgn da irin wannan muryar tun ranar data fara ganinsa daren daya tura Baba Zulai ta kirata, katseta yayi da cewa “kin kirani ne na rinqa qirga bugawar numfashinki kome?" Cikin sanyin jiki da sassanyan muryarta tace “naji shiru sati guda da tafiyarka zuciyata ta kasa jurewa kadaicin rashinka bansan laifin da nayi maka ba Abuh Mu'azzam wannan hukuncin naka yayimin tsauri don Allah idan laifi nayi maka kayi hqr ka yafemin bazan iya jurewa ba..." Bata gama rufe bakinta ba yaja wani uban tsaki ya kashe wayar.
Hankalinta ya qara tashi ta sake kiransa saida tayi kira biyar sannan ya daga cike da bala'i yace “zaki fuskanci qasqanci daga gareni idan baki fita daga rayuwata ba Marwah wlh na tsaneki haushin kaina nakeji da nayi gangancin hada zuri'a ta da qasqantacciya irinki mara asali tsintacciya wadda batasan makomarta ba bansan masifar data sani hada jiki dake ba har nakai gayi miki ciki wlh ji nake dama na zubar da cikin nan kafin yazo duniya Marwah da ace kece kika haifamin dana gara ace na mutu ban haihu ba, saboda last warning kada ki qara kirana da mijinki Marwah nafi qarfinki kuma na tsaneki ke badan ina tunanin wani abu bama da sawwaqe miki zanyi ki huta nima na huta taintacciyar mage kawai"...........
More comments😍
More typing😍
*Mrs Dr M.A...✍🏻*
[3/7, 12:00 PM] MRS M.K.D: https://www.facebook.com/Freedom-Writers-Association-110039363936693/
https://www.facebook.com/Freedom-Writers-Association-110039363936693/
*FREEDOM WRITTER'S ASSOCIATION.* 📕🖊️
( _Y'anci don cigaban Mata, y'an ci ya d'ara bauta, freedom writters._ )
*( F.W.A)🖌*
*WACECE NI?*
*(SANADIN KUKANA!)*
_typing✍🏻_
*Mrs Dr M.A...*
*36-37*
Katse wayar yayi tare dayin jifa da ita ya koma ya kwanta zuciyarsa na tafasa wani bangare cike da takaici da nadamar kalaman da ya fadawa matar tasa wasu hawaye masu zafi suka zubo masa yarasa meyasa yakejin tsanar yarinyar a kowacce gaba ta jikinsa tare da jin haushin hada zuri'a da ita da yayi.
Hawayene sukebin idonsa ya miqe ya dauro alwala yayi sallah yana roqon Allah ya yaye masa abinda ke damunsa game da Marwah ya rasa laifin da tayi masa da yake nisanta kansa da ita ko waya idan ya daga zai kirata sai yaji ya kasa dole ya ajiye.
Ita kuwa yana katse wayar jikinta ya dauki wata rawa zuciyarta na bugawa da qarfi fat² tayi saurin dafewa tare da furta “Allahummah la sahla wama maja'altahu sahla wa'anta taj'alul hazna iza shi'itah sahla Innanillahi wa Innah ilaihirraji'un Allahummah ajjirni fi musibati wa'akalifni khairin minha...." Wani kuka me ciwo ya qwace mata jikinta yana rawa ta zame daga kan gadon tana jin numfashinta yana qoqarin daukewa tace “Na dade Ina tunano zuwan wannan ranar gata tazo shiyasa naqi sakin jiki dakai tun farko saboda tsoron fadawa wannan tarkon meyasa zaka gujeni a lkcn da nafi kowa buqatarka meyasa zaka karyamin alqawarin da kayimin Colonel me nayi maka haka daka tsaneni meyasa ka tsaneni ka fadamin laifina wlh zan gyara banida kowa saikai bansan kowa ba saikai Allah na roqeka kada ka rabani da mijina Allah kasani inason mijina...."
Kukan da takeyi ne yasa mata wani azabbaben ciwon kai tana zaune a gurin ta kasa tashi tama rasa meye ya kamata tayi hakanan ta miqe daqyar ta shiga bathroom ta wanke fuskarta ta dauro alwala ta dauki hisnul muslum ta fara karanta wasu addu'o'i da tasan zasu sama mata sauqi a zuciyarta ta danji sauqin radadin da zuciyarta takeyi mata amma ta kasa tsayar da hawayen idonta a wannan rana daga ita harshi babu wanda yayi bacci kwana yayi yana tunanin halin da zata shiga sanadin kalaman daya fada mata har kuka yayi sosai shima bude system dinsa yayi ya zubawa hotonta da Mu'azzam da sukayi ranar suna Ummuh ce duk ta turo mishi donshi ko gurin sunan bai iya zuwa ba, kyawun yarinyar na musamman ne yanajin qaunarta a can qasan zuciyarsa saman ta kuwa qiyayyarta yakeji har wani bangare na zuciyar nasa yana fada masa idan yaci gaba da zama da ita zai cutu.
Wata sama da daya har an tafi uku rayuwar daga ita harshi babu wanda takewa dadi kullum zai kira Ummuh su gaisa ya tambayeta lfyr dansa amma baitaba tambayarta lfyr uw