Dariya yayi sosai yace “ashe dai yana kama dani din dai ni bansan ya akayi ma yarinyar nan kika fini qarfin jini har haka" hakadai sukaci gaba da hirarsu har suka gama shirinsu tsaf suka fito ya bawa wani yaronsa motar yakaisu airport suka shiga jirgi sai qasa 9ja.
Suna fitowa daga jirgin suka hangi Abuh da Ummuh da sauri suka nufosu abin mamaki daga Abuh har Ummuh rungume Marwah sukayi Abuh ya karbi takwaransa ita kuma Ummuh ta qara rungume Marwah a jikinta tanata zuba mata sannu tana dubata sosai gabanta na faduwa ta rasa meyasa ko muryar yarinyar taji sai qirjinta ya buga haka dai suka rankaya suka shiga motar Abuh ne yakeja Marwan na gefensa Ummuh da Marwah suna baya tanata satar kallon Marwah hanunta dauke da Mu'azzam tayi ajiyar zuciya ta kasa hadiye mgnr dake bakinta tace “Bunayyah kullum na kalli fuskar matarka sai naji gabana yana faduwa bansan meye yasa ba inajin qaunar yarinyar a cikin jinina"
Murmushi yayi yace “hakan yafi komai yimin dadi da Allah ya nufeni da kawo wacce kikeso amma Ummuh wani musu mukeyi da everlasting tace “Junior da ita yake kama nikuma nace da Baby Zahrah yake kama taqi yarda tace wai da ita yake kama lkcn tana qarama" Ummuh tayi murmushi tace “tunda na dauki yaron nan nake ganin hoton fuskar Bintu Zahrah haskene kawai ba irin nata ba ita ba fara bace tas"
Wani ihu yayi da yasa Abuh saurin cin birki yayi dariya yace “Allah Abuh tunda aka haifeshi nace da Baby Zahrah yake kama taqi yarda to dai yanzu gashi kinji ko?" Ya juyo yayi mata gwalo takai masa duka ya goce ta turo baki kawai sai hawaye ya zubo mata, da sauri Ummuh tace “Subhanallahi meye kuma na kukan?"
Qara turo baki gaba tayi tace “ba kune kukace baya kama dani ba" dariya sukayi dukkansu ya juyo yace “yarinyar nan kishine zai kasheki ke kishin naki harda wadda bata raye ma yi kikeyi kinga fa Ummuh yar mitsitiyar yarinyar nan saida ta mayar dani kamar wani danta ko waya ban isa nayi da Ra'isah a gabanta ba yanzu saita barni na kwana gwauro"
Tsuke fuska Ummuh tayi saboda sako Ra'isah da yayi a mgnr, da sauri ya saita nutsuwarsa Abuh yace ai muna murna da zuwanta cikin rayuwarka" sake kwanciya tayi a jikin Ummuh hakanan takejin qaunar surukar tata tana ratsa jininta tace “Allah Ummuh dani yaron nan yake kama idan na nutsu zan nuna miki wani hotona da wani mutum da bansan waye ba ance wai a aljihun wandon jikina aka ganshi lkcn da aka tsinceni ina tunanin shine babana"
Ajiyar numfashi Ummuh tayi tace “karki takurawa kanki ki bari a hankali idan kin samu lfyrki kya nunamin ai muna tare Marwah kinji takwarar mijinta" zaro ido yayi ya sake juyowa ya mintsineta yace “Au hakane fa saboda gasa sunan ma irin nawa aka saka miki" murmushi tayi hawaye ya cika idonta tace “Nanny indo tace lkcn da aka kawoni gdan banida baki abu daya na riqe kawai sunan Malwal da aka tambayeni sunana sai nace Malwal komai aka tambayeni sai nace Malwal shiyasa kawai su sanyamin Marwanatuh"
Daga Ummuh har Colonel Marwan babu wanda qirjinsa be buga ba a fili yace “Malwal everlasting shi kadai kika iya kema? Itama Baby Zahrah ta harta mutu bata iya cewa Marwan ba saidai tace Malwal"...........
More comments😍
More typing😍
*Mrs Dr M.A...✍🏻*
[3/7, 8:57 AM] MRS M.K.D: https://www.facebook.com/Freedom-Writers-Association-110039363936693/
https://www.facebook.com/Freedom-Writers-Association-110039363936693/
*FREEDOM WRITTER'S ASSOCIATION.* 📕🖊️
( _Y'anci don cigaban Mata, y'an ci ya d'ara bauta, freedom writters._ )
*( F.W.A)🖌*
*WACECE NI?*
*(SANADIN KUKANA!)*
_typing✍🏻_
*Mrs Dr M.A...*
*30-31*
Ajiyar zuciya tayi daidai lkcn da Abuh yayi parking cikin gdan nashi kallonsa Marwan yayi yace “Abuh na dauka gda zaka saukemu" murmushi yayi yace “kada ka damu Bunayyah haihuwar fari mace tana buqatar kulawa ta musamman saboda jikinta danye ne tana buqatar hutu sosai, idan tayi qwari zamu baka matarka"
Bai iya cewa da mahaifin nasa komai ba amma har cikin ransa wannan hukunci baiyi masa dadi ba, Ummuh ce ke riqe da dan suna tafe tana riqe da Marwah har suka shiga ciki shima yana riqe da ita.
Wani daki suka shiga an qawatashi da komai na buqatun rayuwa, zaunar da ita sukayi ya zauna a kusa da ita yanata zuba masa sannu fita Ummuh tayi ta shiga dakinta.
Riqota yayi ya sauke numfashi yace “meyasa su Ummuh zasuyimin haka me suke nufi da daukoki su kawoki nan nifa banason irin haka everlasting yanzu nikadai sukeso na rayu kenan" kallonsa tayi cike da mamaki ya daga mata gira yace “ko kadan banason nesa dake wlh dumin jikinki ya ratsa nawa babu abinda nakeso kamar kasancewa dake" qasa tayi da kanta ya sake dora hannunsa saman kanta yace “dare yayi yanzu..."
Shigowar Ummuh ne yasashi hadiye mgnrsa ta harareshi tace “ka tashi kaje kaci abinci ka tafi gdanka yanzu nayiwa Zulai mgn tace “matarka ta dawo tun biyu na rana" lumshe idonsa yayi ya marai