NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 46 of 84

lfy kinsan meye sunan babe idan kika haifi mace?" Tayi qasa da kanta cike da kunya yayi murmushi yace “Sakinah shine sunanta sunan qanwar Ummuh ce data rasu shekaru sha uku da suka wucce Marwah asalinmu ba mutanen 9ja bane mu larabawan Lebanon ne Ukteeh shine sunan da Muke kiran Sakinah tare muka taso a gurin kakannin mu nida ita a Lebanon Ukteeh tabani shekara biyar saboda haka ita taci gaba da kula dani bayan Ummuh da Abuh sun dawo 9jah saboda karatuna yasa aka barni acan shekaru sunata tafiya har Ukteeh ta isa aure aka aurar da ita ga wani dan gasar Qatar suka haifi yarsu daya tak me kama da babanta amma ita bata da irin haskenmu tanada dan duhu duhu a cikin fatarta nine na zaba mata suna Fadimatu muna kiranta da Zahrah Everlasting na shaqu da Baby Zahrah sosai tun muna tana qarama na fara nuna mata qauna lkcn idana shekara goma sha bakwai a duniya na gama karatuna, Tun Ina qarami na taso daso da burin zama Sojah hakan yasa mahaifina ya yarjemin naje nayi training yasani a makarantar sojoji ranar dazan tafi yini nayi Ina kuka ba iyayena nakewa kuka ba rabuwa da Baby Zahrah shine nakewa kuka saboda yarinyar shekarunta biyu amma tayi mugun sabo dani, hakadai ranar dazan tafi daqyar aka rabamu tana kuka ina kuka Ukteeh na kukan tausayin mu" Jan fasali yayi ya qara matseta a jikinsa yana shassheqar kuka yace “ashe bansani ba rabuwar qarshe mukayi da Baby Zahrah da mahaifiyarta Marwah rabuwar data zamemin masomin lalacewata Marwah tunda na tafi na kasa samun nutsuwar zuciya kullum saina bata lkcna wajen Kiran wayar Ukteeh kawai dan na zauna nayi hira da Baby Zahrah nayita dariya, ko a makaranta abokai na sun karanceni idan sukaga ina dariya ina walwala to da Baby Zahrah nake waya yarinya qarama me shiga rai duk abokaina sai suka canza min suna kawai suka koma kirana da Baby Zahrah kuma ko hira sukeyi indai ba sunanta suka kiramin ba bana kulasu Marwah munada wata al'ada ta larabawan Lebanon muna iya aurar da yarinya tun tana jaririya ma idan ta samu wanda takeso" Sake share hawaye yayi yaci gaba da cewa “munada wata biyar a training abin ya isheni na kasa jurewa abinda nakeji game da Baby Zahrah saboda haka na shirya nabi jirgi naje 9ja na sanar da Abuh cewa nifa inason Baby Zahrah kuma ita nakeson aure, ba qaramin mamaki da dadi iyayena sukaji ba babu bata lkc Abuh ya shirya muka juyo Lebanon dashi ya sanar da Anwar mahaifin Baby Zahrah yayi murna sosai akace to tunda duka abin na gdane na bari Zahrah ta qara girma sai ayi mana aure, nakuwa qeqashe qasa nace ni saidai a dauramin aure da ita haka aka daura aurena da Baby Zahrah tanada shekara biyu da rabi inada shekara goma sha tara ranar nayi hotuna da yar qaramar matata kamar wata babba haka na rinqa rungume kayata ke ranar a dakina ta kwana na kwana ina kallonta kwanaki uku hankalina ya kwanta Baby na ta zama tawa na koma makaranta. Satina guda da tafiya aka kira aka sanar da Ukteeh Ummuh batada lfy tana asibiti ashe qaddarar mutuwar matata ne da mahaifiyarta qawata, qin fadamin Ukteeh tayi suka shirya suka tafi 9ja..." Muryarsa ce ta qara rauni kuka yacita sosai yaci gaba da cewa “daren ranar kamar nasan wani abu zai faru dani ban iya bacci ba gashi inata kiran wayar su Abuh da wayoyin su Ukteeh harma data kakanni na na kasa samu ashe a wannan daren qaddarar da rabuwata da Baby Zahrah ta fado Marwah jirginsu ne yayi hatsari a cikin 9ja ya dagargaje a duk wani mutum dake cikin jirgin ya mutu ciki harda Ukteeh da Baby Zahrah har garama Ukteeh su Abuh da mijinta sunga gawarta amma Baby Zahrah ta qone qurmus banganta ba Marwah ta mutu ta barni da ciwo a zuciyata. Bansamu lbrn mutuwar ba sai bayan wata biyu kullum naje gdansu Baby Zahrah Abuha cemin yakeyi suna 9ja dana gaji na shirya na tafi 9ja na tarar basanan haka sukayita yimin yawo da hankali hardai na gaji naje nasa kakanmu a gaba nace saiya fitomin da matata ina kuka wannan ya tashe hankalinsu suka fito suka fadamin gsky" Dakatawa yayi yayi kukansa me isarsa tana tayashi tana share masa hawayen idonsa tana girgiza masa kai ya sake rungumeta yace “Tunda aka fadamin banqara sanin inda kaina yake ba sai bayan sati uku ashe wai haukacewa nayi saida aka dorani akan magunguna sannan na dawo hayyacina amma ba fah kullum cikin kuka nake da kiran sunan Baby Zahrah wannan dalilin yasa Abuh ya hanani komawa Lebanon naci gaba da zama a 9ja wlh Marwah ko sigari bantaba shaba iyakar zamana a Lebanon sai bayan dawowata 9ja da azaba tayimin yawa gata zuciya gata jiki wani aboki nayi Mahfuz bayan Abuh ya shigemin gaba ya samamin makarantar yayan manya ta sojoji na fara zuwa Mahfuz ne yaga damuwa tayimin yawa bana tabuka abin arziqi so kinsan kowanne society da irin matsalarsu mu a al'ada irin tamu ta sojoji shaye² ba wani abu bane har gasa akeyi ta wanda yafi kowa iya shan giya Marwah tun ina qin sha haka Mahfuz ya rinqa nunamin idan nasha zatake ragemin damuwa haka kuwa akayi ranar dana fara shan giya har party akayimin aka nemomin zafafan mata aka bani kwalba biy
🏠