NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 45 of 84

ayi hawaye suka biyo kuncinta ya hada bakinsa da nata yace “My Everlasting dama ashe na baki baby ashe baby nane yake wahalar min dake oh God Allah na gde maka Everlasting don Allah ki haifemin baby girl me kama dake kinji" Lumshe idonta tayi hawayen yanaci gaba da zuba a idonta ta yunqura zata miqe yayi saurin riqeta yace “kula kada ki wahalarmin da baby komai ma kin dainayi sai baby na yazo duniya" kukane ya qwace mata me ciwo tayi saurin rufe bakinta saboda tasan halinsa bayason kuka mara dalili, ruqo hanunta yayi yace “ki daina kinsan banason kukannan ko?" Dagowa tayi ta kalleshi tace “ina tausayin kaina da yayan dazan haifa Colonel me zance musu idan suka tambayeni iyayena?" Rintse idonsa yayi qirjinsa na dokawa ya daga mata hanu yace “ya isa Everlasting kada ki rudamin farin cikina da wannan banzan tunanin naki ki kyaleni na rayu da farin cikina a yau kedai da baki farin cikin kije kiyita baqin cikin ki nidai inason kayana" Tsaki yaja ya fice a fusace ya nufi cikin barreck din gdansa na barreck din ya shiga ya fada kan gado ya dafe kansa yace “oh God everlasting damuwa ce ke gabadayanki" wayarsa ce ta fara ruri ya dauka yaga number Ummuh ya daga da sauri yace “Ummuh ina cikin farin ciki everlasting ciki gareta Ummuh nima nakusa naga dana ki tayani murna Ummuh na kasa boye farin cikina yanzu zan kira Ra'isah na fada mata..." da sauri ta katseshi da cewa “kul Bunayyah banason shirme cikin da baikai ya kawo ba zaka fara yamadidi dashi bakasan cewa wasu daga cikin makusantanka basa burin ganin yayanka ba kai meyasa kullum baka hankali ne?" Murmushi yayi yace “Ummuh kenan ai kinsan ko duniya zataqi zuri'a ta Sweet bazataqi ba saboda haka bazan iya boye mata ba" murmushin takaici tayi cikin tausayin dan nata ta kashe wayar batare da tunanin komai ba ya kira wayar Ra'isah tana dagawa tace “wata guda kenan rabon da ka nemeni sai yau" murmushi yayi yace “yau dinma albishir na kira nayi miki mun kusa samu qaruwa Everlasting ciki gareta wata biyu da sati uku yau Ina cikin farin cikin da bantaba yiba" gabanta taji yayi wata muguwar faduwa bawai lbrn cikin ne ya girgiza ta ba aa sunan daya ambaci yarinyar dashi wai everlasting “Everlasting?" Ta tambayeshi batare da tunanin komai ba yace “eh wlh Sweet amma fah cikin yana wahalar da ita tafi wata biyu tana amai Allah sarki na tausaya mata cikin ya cire mata sha'awata bata iya daukeni kamar dai har dukanta nasha yi ashe nine nayi laifin matsalar daga gareni ne wlh inajin tausayin yarinyar bakiji yanda nake sonta ba bazan iya rayuwa babu itaba..." “dakata Marwan banason shirme me kakeso kacemin? Kanasonta? Ya akayi ka fara sonta ina alqawarin da kayimin na bazaka taba hada matsayina da wata mace ba a zuciyarka me kake nufi da sunan da kake kiranta nifa har yanzu matsayina na alewa ne kawai a suna a bakinka amma wannan qazamar yarinyar mara asali har ta samu matsayin ka kirata da everlasting me kake nufi...." Daka mata tsawa yayi yace “ya isheki haka Sweet na fada everlasting kin isa ki hanani fadin abinda ke rainane ko cewa nayi dake zan karya alqawarinki dane idan ta haifa zan karba in baki nikuma naci gaba da hutawa da matata" Kit ya kashe wayar ya miqe ya fita ransa a mugun bace ya nufi clinic din mutane sai barka sukeyi masa take yaji duk wani quncinsa ya yaye ya shiga ya tarar da ita a kwance lkcn ta gama waya da Helin take fada mata halin da ake ciki tayi mata fada sosai akan sakacinta na daukar ciki yanzu daga qarshe tace “babu damuwa tunda kici gaba da kula da kanki mijinki na tabbatar a yanzu yana sonki so na gaske kiyi hqrn jure masa kada ki sanya aranki kina da ciki bazaki iya da mijinki ba wlh aikine ja a gabanki kiyi yaqi da karuwan mijinki sannan kiyi yaqi da shadiyar matarsa da take rura wutar komai ki dawo da hankalinki jikinki ki saki jiki dashi tunda har zuri'a tashiga tsakanin ku ki barmin sauran aikin" Wannan dalilin yasa ta kwantar da hankalinta yanda yaganta yasashi farin ciki ya matsa jikinta da sauri ya riqota ya miqar da ita ya hadata da jikinsa ya dora hanunsa a cikinta yace “inasonki Everlasting kinga dai ikon Allah ko da tuni kishi yasa kin kashe uban yayanki" qasa tayi da kanta tana qoqarin janyewa ya sake riqota yace “kice kinasona kinji don Allah zanji dadi wlh" sake janyewa tayi idanunta ya ciko da qwallah tace “ni...ni banason..." Saurin rufe mata baki yayi idanunsa ya ciko da qwallah jikinsa na rawar data bata tsori tace “bafa kaine banaso ba turarenka ne banaso amai yake sani" Ajiyar zuciya ya sauke me qarfi yace “na daina sawa amma kice kinasona" lumshe idonta tayi kalmar tanayi mata nauyi kafin tayi mgn taji yayi qasa ta bude idonta da sauri ganin yayi knilling yasata itama tayi qasa tace “ in...Ina...son...ka..." Wata uwar runguma yayi mata yana dariyar da bata taba sanin ya iyaba yace “wayyoh dadi Everlasting da gaske kina Sona?" Daga masa kai tayi yayi murmushi yace “na gde Allah yayi miki albarka ya rabaku da babyna
🏠