ah tafi qarfin ka ka rubuta ka ajiye Marwan a diary dinka watarana wlh muddin ina raye saikayi kuka da hawayenka saikayi nadamar kalamanka kuma sai kasani kuma ka yarda marayu ma yayane kuma zaka gane bambamcin shege da batacce zaka gane cewa rayuwa tafiya take akan hurumin da buwayar ubangijin Yessu al'masihu wannan damar takace amma next tamuce baa fara wasan ba Colonel Marwan"
Juyawa tayi ta fice daga gdan da sauri ta fada motarta taja ta fice daga estate din ta nufi gurin aikinta tabarshi tsaye da sakakken baki daqyar yaja qafarsa ya koma motarsa ya jima a ciki kafin ya iya tada motar ya shiga ya fita daga estate din shima kai tsaye gdan Shukurah ya nufa yana zuwa ya tarar da ita tana sharholiyarta da wani bai kulata ba ya shige ciki ta jima sannan ta shigo ya dauketa da mari yace “banace ki daina kawomin garada gidana ba?" Murmushi tayi tace “au nidin hhhhhh Colonel kenan to ai bari kaji banma fara ba wani ma yayi tusa bare me ciki kaima kakai karuwa dakinka na sunnah gadon da kake kwanciya da matarka ta sunnah balle ni daba auren kowane akaina ba, kabani mamaki Marwan dama ashe matarka tananan kacemin batanan dama ashe bansani ba iskancinka ya shahara haka Allah ya isanta MARWAN ka cuceta da kasa idanunta yayi wannan mugun ganin yarinya qarama yar cikinka Marwan kaga kwalliyar datayi duk saboda kai amma saboda kai bunsuru ne tazo ta tarar dakai kwance da karuwa haba Colonel ai halal ma ana barinta don kunya balle haram Allah ya isarwa yarinyar nan Marwan Allah ya isar mata wlh nasan ba asalin matarka bace da kakejin tsoronta kamar uwar data haifeka wlh da bazaka kirani gdanka ba amma kasani aure duka sunansa aure wannan yarinyar da kakecin mata kake kiran sunanta kuma kake tata mata iskanci saita baka mamaki Allah dai ya ara mata dama"
Shigewa tayi bathroom ta sakewa kanta ruwa shikam zama yayi saboda juyawar da kansa yakeyi waishi meye yake faruwa dashi ne kowa Marwah kowa Marwah meye ne da yarinyar nan wacce baiwa ke gareta da duk wanda yaganta saiya sota?
Ficewa yayi daga gdan ya nufi gdansu yana zuwa yayi saa Abu yananan suka gaisa ya tambayeshi ya gdan sosai ya fara yi masa nasiha akan girman amana baidai fito ya fada masa wacce amana ba amma ya kashe masa jiki sai bayan Abu ya ga yi masa nasihar sannan yace “dama nazo yimuku sallama ne zantafi Germany yau"
Kallonsa Ummuh tayi tace “ita kuma yarinyar nan ina zaka barta Bunayyah jiya da ita na kwana a Raina" yatsina fuska yayi yace “zan tafi da ita zatayimin amfani" bai jira amsarta ba ya miqe ya fice suka bishi da kallo Abu yace “Allah ya shiryaka Bunayyah kayi nisa giyar kudi na dibanka" hawaye Ummuh ta share tace “idan kaga yarinyar zakasha mamaki yarinya ce qarama amma Bunayyah baya tausayinta baya rangwanta mata ta wajen mu'amalar aure wlh Bunayyah bashida imani Abu ya gama sissike yar mutane sannan kuma Wai yace Idan burinsa ya cika sakinta zaiyi wannan wacce irin rayuwa Bunayyah ya zabawa kansa ta rashin adalci tausayin na qasa da kuma imani Abu bana mamakin wasu miyagun halayen na Bunayyah saboda ya mayar da zina ba komai ba a rayuwarsa ina kuka Idan na tuna ni Sukhaina a cikina na haifi mazinaci mai gaggawa wajen sabon Allah shiyasa tun farko nace bazaiyi aikin sojan nan ba kace tunda yanaso abarshi yanzu gashinan yafi qarfin mu"
Rungume Abu yayi a jikinsa yana lallashinta har tayi shiru da kukan yace “ki rabu dashi kar nake kallonsa kada ki qara nuna masa damuwarki akan lamarin yarinyar" saida ya tabbatar tayi shiru sannan ya miqe ya fita.
Ita kuwa Marwah yana fita ta fito ta kwanta taci gaba da kukanta ranar ko ruwa tasa a bakinta dacinsa takeji saboda zuciyarta daci takeyi sosai hakadai a daddafe sukayi azahar Baba Zulai ta matsa mata tasha tea tayi wanka tasa wata doguwar rigar atamfa tayi kyau sosai tayi daurin dankwalinta simple amma iya yau kadai ta rame sosai abinka da mara jikin dama.
Tana zaune ta zuba uban tagumi ya shigo Baba Zulai ta miqe zata shiga kitchen yace “aa kiyi zamanki kawai dama yau zamu tafi ne a kula da gdannan sosai zaro kudi yayi masu yawan gaske yan dubu dubu guda uku ya bata yace da albashinta na wata biyar da abinda zaa kula da gda kafin su dawo.
Kamo hanun Marwah yayi ya dagota ya dagata cak batayi wani motsi na qwatar kanta ba saida suka shiga cikin dakin nata ta zame ta sauka qasa ya sake riqota yace “banason iskancin kin nan fah kiyi ki hada abinda kikasan zaki buqata biyar zamu tashi" kawar da kanta tayi ta haye gadon ta kwanta yabita da kallo yace “ina miki mgn kinayin abinda kikaga dama ko?" Shiru ta kumayi batare da tace komai ba ya juya a fusace ya haura samansa ya fara hada takardunsa.
Baba Zulai ce ta shigo ta sameta a kwance tana sharce hawaye tace “yarinya dama kin hqr namiji da kike ganinsa gunzugun barkono ne wlh gara kiyi kwalli da garwashin wuta da ki kalli wani namijin Marwah idan kikayi hqr komai zai wucce watarana sai labari ki tashi ki shirya idan ya fito ya taddaki a haka rankine zai qara baci a banza kuma tunda ya