ogon abu da aka jera kayan wankan kala² a tsorace ta rinqa zare kayanta harta gama ta kunna ruwan sanyi da taimakon ilimin secondary dinta daya zame mata alkhairi a wannan bangaren har dogon gashinta baqi saida ta kwance Wanda ya cukuikuiye saboda rashin gyara saida ta wanke.
Miqewa tayi ta mayar da kayanta tana yaba ni'imar da ahlin gdan suke ciki wankanta na yau ma na musamman ne fitowa tayi dakin ta dauki wasu kaya akan gdan ta qare musu kallo riga da siket ne na English ta jima tana juya kayan kafin tayi qundumbalar sanyasu a jikinta sunkuwa zauna mata dass yan matsakaitan breast dinta da basu sami arziqin bra ba suka tsaya cirko-cirko a cikin rigar kayanta ta bude ta dauki wani wankakken jemammen hijjab dinta tasa ta zauna sallah takesonyi amma batasan alqiblar ba tananan zaune tana tunanin abinda ya dace tayi taji an bude qofar an shigo wata mata ce dattijuwa dauke da kwanukan abinci ta ajiye a qasa tace “sannu da zuwa Hajiya gashi Alh Marwan yace a kawo miki abinci kici"
Dagowa Marwah tayi da sauri tana kallon matar ga tambayoyi a bakinta amma babu damar yinsu saboda mgnr ma wuya takeyiwa Marwah qasa tayi da kanta a hankali cikin sassanyar muryarta tace “inane alqiblah?” dubanta dattijuwar tayi tace “mirrow dinnan zaki kalla" ta miqe tace “idan kinyi sallar zan dawo yarnan kinji yau gdan cikin yanci muke Hajiya mulkatu batanan an daga zuwa China zaaje aci tsutsa" itadai Marwah batace komai ba ta tayar da sallarta magrib tayi sannan tayi Isha ta zauna tana azkar kafin ta miqe taji an sake bude qofar an shigo ta juya ta kalle me shigowar wannan dattijuwar ce tace “Alh yanason ganinki a parlourn sama" dagowa tayi da sauri tana dubanta tayi murmushi tace “yace nayi sauri bacci yakeji" kamo hanunta tayi tace “meye sunanki yata?" Lumshe manyan idanunta tayi tace “Marwanatuh" tarr dattijuwar ta kalleta tace “na dade ina mafarkin zuwan wannan sunan da surar nan gdan nan Ina tunanin kece zaki zama qarshen mulkin mallakar Hajiya Ra'isah a gdannan mace ta kankane komai ta hana komai gudana ta samu mutum sai juyashi takeyi kamar waina" banda kallon babu abinda Marwah kebin dattijuwar dashi tace “ya sunanki?"
Murmushi tayi tace “sunana Zulai shekarata goma sha biyu ina aiki a qarqashin me gdannan tunda nake tare dashi bamu taba samun sabani ba saboda miskiline mgn ma sai yaga dama yakeyinta ya auri matarsa ta farko Juwairiyyah auren zumunci ne ta rasu kan gabar haihuwa daga ita har jaririn bayan shekara biyu ya dauko mana alaqaqai dinnan da tazo ta gama da komai na gdannan ta gama da zuciyarsa ta hana masa gurbin da zaisa wata mace a ciki yanzun kema nasani tabbas akwai manufa a cikin zuwanki gdannan ta tafi China tace zata iya daukar wata hudu acan ta yarda dakene saboda bakida galihu ta kawoki gdanta a matsayin sirri a yau an daura aurenki da mijinta a gidan marayu zaku zauna matsayin ma'aurata amma cikin sirri batare da kowa ya sani ba nima ba ita ta fadamin ba jinayi suna hirar da aminiyarta Ummah jiya"
Gaban Marwah ya fadi sosai tace “aure kuma Baba Zulai nidin aka daura aurena da wani wannan wanne irin aurene?" Rufe mata baki tayi daidai lkcn da suka fito daga dakin suka fito parlourn tabi parlourn da kallon qurulla gabanta ya fadi sosai cikin tsoro take bin kowacce kusurwa da kallo ta gdan tabbas an shiryawa rayuwar duniya a gdan an kashe kudi har na hauka tunda Marwah take ko a film bata taba ganin tsarin daya dauki hankalinta irin wannan tsarin jitayi baba Zulai ta tabata tayi firgigit ta dawo hayyacinta ta sauke idonta akan mutumin dake zaune saman daya daga cikin kujerun gurfane Baba Zulai tayi hakan yasa itama Marwah ta gurfana saukar muryarsa taji a jikinta yace “meye yasa kuka dade bayan na fada maki bacci nakeji?" qasa tayi da kanta tace “tuba nake ranka ya dade naje na tarar tana sallah ne" bai sake mgn ba ya nuna mata hanya ta miqe sumsum ta nufi wata qofa itakam Marwah tana tugune kanta a qasa tama kasa dagowa ta kalleshi sakejin saukar muryarsa tayi yace “Shi mutum mara asali duk yanda kayi dashi saiya nuna maka bai samu galihun tarbiyya ba banda haka meye a cikin gaisuwa" sosai mgnrsa tayi mata dukan nannauyar guduma tayi watsa watsa da nutsuwarta zuciyarta tayi wani mugun baqi batasan sanda taji wani hawaye ya zubo mata ba batajin haushin duk wanda yayi mata gorin nasaba amma yau saita tsinci kanta dajin ciwon kalamansa bai tsimayi me zatace ba yace “kinci abincin da aka kai miki?"
Shiru tayi batace komai ba sai shassheqar kuka da takeyi tsawa ya daka Mata yace “banason iskanci ni zakisa a gaba kiyiwa kuka dubeki ko fasali babu dallah tashi ki bani guri banza kawai"
Kamar me jiran korar tasa ta miqe da gudu ta shige dakin data fito ta zube a qasa ta sake rushewa da kuka tace “wayyohh Allah me kake nufi dani ne?" Kuka tayi sosai har kamar idonta zai fadi kafin ta miqe ta hau gadon ta kwanta tanaci gaba da rera kukanta batasan sanda bacci ya dauketa ba kiran sallar asuba ne ya farkar da ita ta miqe