kirani duk sanda kike buqata idan harkin amince zan rinqa kawo miki ziyara"
Juyawa tayi ta fice ta barsu da sakakken baki hawaye nabin kuncin Marwah a fili tace “wannan wanne irin masifa ne zina manemin mata nashiga ukuna nikuma haka Allah yayi dani...." Kuka tasaki me sauti tare dayin jifa da takardar tana cewa “ Innanillahi wa innah ilaihirraji'un Allahummah ajjirni fi musibati wa'akalifni khairin minha Allah na tuba Allah ka yafeni Allah me nayi maka ne daka hadani da mazinaci wlh bantaba zina ba meyasa qaddara ta kuma hadani da mazinaci" kuka takeyi sosai Baba Zulai tana rarrashinta tana hawaye tace “kiyi hqr yarnan kiyiwa Allah gdy da yasa kikasani ita wacce maciya tsutsar ai batama san yanayi ba ke kota sani wlh bazata damu ba tunda batada kishin kanta ta yarda ta kishiyar waje akan ta gda ni dama na dade Ina zargin hakan saboda nasha ganin comdom a a bola kodai a wani guri amma tunda ba hurumina bane shiyasa ban zurfafa bincike ba kada kisa abin aranki ya dameki kiyi qoqarin gyarawa kawai" haka ta rinqa rarrashinta tana nuna mata cewa kada ta nuna masa tasan me yake aikatawa jinta kawai takeyi amma maganganun nata kwata² basa shigarta saboda wata tsanar Marwan takeju tana taso mata tanajin kamar ta tashi ta fice tabar masa gdansa amma bata da iko.
Haka ta zauna a gurin kamar mara amfani tanata share hawaye lkc zuwa lkc duk yanda Baba Zulai taso data rabata da damuwar ta kasa kawai kallonta takeyi tabbas Marwan ba mutumin da zaayi sha'awar hada zuri'a dashi bane to amma duk gurbatarsa ai baikaita gurbata ba tuno hakan yasa taji wasu sabbin hawaye sun keto mata ta miqe kawai ta shige dakinta ta kulle ta fada gadon ta kwanta taci gaba da kukanta sallah kawai ke tashinta daga gurin da take kwance tayi ta dawo qarfe hudu da rabi ya shigo gdan da tarkacen kayansa ya hado mata shopping na kayan kwalliya da kayan sawa dana ciye² Baba Zulai ya tarar kawai a parlourn tana gyarashi tana ganinsa tayi masa sannu da zuwa ta karbi kayan hanunsa yace “ina Marwah?"
Gabanta ne ya fadi tace “am...im tana dakinta bama tajin dadine" da sauri ya nufi dakin yace “biyoni da kayan" bai jira cewarta ba ya shiga dakin ya bude ya shiga itama Baba Zulai ta shiga ta ajiye kayan ta ja qofar ta rufe ya zuba mata ido yana kallonta gabansa na faduwa a hankali yaja qafarsa ya qarasa ya haura gadon ya yaye bargon data rufa ya dagota saida yaji kamar kansa zaiyi bindiga ganin yanda fuskarta take sharkaf da hawaye yace “nikam na shiga ukuna yanzun kuma mene ya kawo kukan?" Lumshe idonta tayi saboda ganinsa ma batason yi ta janye jikinta daga nasa ta koma ta kwanta gyara zamansa yayi ya sake kamota jikinsa yace “kiyi hqr aikine ya tareni yau Marwah nayi qoqarin na samuna fito nazo naga lfyrki so kuma sai wani abu ya tasomin na gaggawa zan tafi Germany cikin satinnan ko zakije?"
Dagowa tayi da sauri ta kalleshi yayi mata murmushi wani qunci ta kumaji ya mamaye zuciyarta tayi saurin dauke idonta daga kansa hawayen yana qara kwaranyo mata ta miqe zata fice yayi saurin riqeta jikinsa na rawa yace “wai meye hakanne My special iyakar sanina qlau muka rabu yau me kuma ya faru bayan bananan?" Kiciyar qwacewa takeyi tana kuka me tsuma zuciya tace “ka sakeni Marwan banaso ka sake tabani don Allah na roqeka please...." Dagota yayi yace “menayi miki Marwah me ya faru?" Kukanta yana qara sauti ta qwace daqyar daga hanunsa ta fice daga dakin a quje binta yayi yana kiranta amma tama fice daga parlourn kafin ya fito tayi bayan gdan ta buya a cikin flowers iyakar zagayensa be ganta ba saboda haka yayi gurin kuratan sojojin dake gadin gidan yana tambayarsu ko ta fita sukace aa basuga kowa ta wucce ba umarni ya basu kada subar kowa ya shigo kuma kada subar kowa ya fita ya sake zagayawa bayan gdan cikin tashin hankalin da tunda yake a rayuwarsa baitaba shiga ba ya zagaye gerding din yafi so goma amma yakasa ganinta sai a zagayensa na qarshe ya tsaya a kusa da ita saboda kiran da akayiwa wayarsa kawai saiya taka qafarta taji zafi sosai ta cije lebanta shikuma ya fara dube dube ajiyar zuciya yayi ya sanya hanu ya dagota ya hadata da jikinsa.
Kuka ta kuma saki me tsuma zuciya tace “don...don Allah ka kyaleni na mutu ma na huta bazan iya rayuwa dakai ba na tsaneka Marwan don girman Allah kasa wadancan mala'ikun su budemin qofa na fice daga wannan baqin gdan da datti da qazanta tayi masa yawa...." Wani gigitaccen mari ya sauke mata cikin hasala irin tasa yace “zanc...." Sai kuma yayi shiru ya fizgi hanunta ya nufi cikin gdan da ita tana kuka tana turjewa yana shiga ya watsata a saman kujera ya daga qafarsa ya taka qirjinta da qarfi zuciyarsa na tafasa yace “bana daukar raini kuma bazan dauka ba wlh karyaki zanyi a banza kuma tunda abin naki iskanci ne ma dole ki shirya kibini Germany sakarya kawai" qara fincikar ta yayi ya dagata cak ya nufi dakinta da ita ya cillata kan gadon yabita ta zame da sauri zata fice ya sake cafkarta ya hadata da qirjinsa ya kulle qofar ya fara rage kayan jiki