NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 99 of 323

a, amma ba zata iya cewa ga yacca akayi ta cire rigar tayi wurgi da ita ba, domin hankalinta gaba ɗaya baya jikinta, yayi kan jaririyar yarinyar da ta gama saddaqarwa ta rasu, ta saddaqar da sun rasata, kuma banda Malam Hamisu ya lura da wutar ya ankarar da ita da sai dai wutar ta babbake su, duk da cewar wutar ɗan kama jikin rigar tata yayi, to sai Allah dai ya taƙaita komai yazo da sauƙi. ganin Hajiya Madina ta rage daga ita sai rigar nono sai zanen jikinta, Malam Hamisu yaja yaran suka sauka zuwa ƙasa. itama ta sauko daga benen a ruɗe cikin tsananin tashin hankali tana salati tana kuka tana jijjiga Zaytuna. bayan mintuna biyar sai ga fire service sunzo, motar su tayi parking a compound tare da motar Baffa, ya fito shima a matuƙar razane yana kallon yanda hayaqi ke fitowa ta window. ya nufa me gadi da mugun tashin hankali yana tambayarsa ina iyalinsa, ganin Baffan yasa Turaki kamo hannun Khalil suka fito daga ɗakin me gadin da ya saka su aciki, a lokacin Khalil shekararsa biyu dan ko yayesa ma ba'ayi ba kasancewar baida cikakkiyar lafiya an haife shi a bakwaini. ganin yaran Baffa yayi kansu da gudu ya ɗauke su, idanuwansa a warwarje yake tambayarsu ina Madina da Ramla, Turaki na kuka ya girgiza masa kai alaman bai sani ba shima. sai Malam Hamisu ne yake sanar masa ai babu jimawa Hajiya Madina ta fita a mota tayi asibiti da Zaytuna. kuma ya kamata abi bayanta gudun kar a sami mummunan haɗari dan hankalinta ba'a jikinta yake ba. "Her Excellency fa?". Baffan ya tambaya da tsananin ruɗu bayan jin abinda Malam Hamisu ya faɗa masa. "ranka ya daɗe ita bata gidan, fitarta babu jimawa wutar ta tashi". Baffa yaja yaransa yana cewa da Malam Hamisu,"ka ji da fire service ɗin nan, zan bi bayan Madina". da faɗar haka ya shiga mota yaja suka bar gidan yabi bayan Hajiya Madina, yana driving ɗin yana bin hanya da kallo har ya iso asibiti, shima motarta ya gani a wajen asibitin sanda zai wuce, bai tunanin wannan asibitin tazo ba tunda ba shi suke zuwa ba. Samun Hajiya Madina yayi a ward ɗin tayi dirshen a ƙasa sai kuka take yi, tana ganinsa ta miƙe tayi kansa tana nuna masa emergency room ɗin da jaririyar ke ciki, gaba ɗaya ma ta kasa magana sai jan nunfashi take yi tana masa nuni da hannu. Jikin Baffa sai ya mutu zatonsa ko sun rasa yarinyar ne, ya nufi ƙofar emergency room ɗin yana leƙawa ta glass, likitoci ne kusan biyar akan yarinyar ana ƙoƙarin ganin an ceto ranta, duk da suna ganin da kamar wuya yarinyar ta rayu, wannan furucin nasu ne yasa tunda Hajiya Madina ta zube a ƙasa bata motsa ba tai dirshen tana ta kuka tana roƙon Allah. kuma cikin hukuncin ubangiji sai gashi numfashin yarinyar ya dawo bayan an shafe rabin awa akanta ana ta saka mata wasu machines, duk da likitan ya faɗa musu the Baby is now alive amma hankalin Hajiya Madina bai kwanta ba, har sai da suka shiga room ɗin da akai admitting Babyn taga idonta biyu an saka mata robat oxygen a hancinta sai wutsil wutsil take sannan ta dawo cikin nutsuwarta. tukunna hankalinta ya kwanta ta daina kukan da Baffa ya shafe rabin awa yana lallashinta bata ji ba, a sannan ne kuma zafin ciwon jikinta ya ratsata, tana dubawa taga ashe ta ƙone ne a bayan hannunta da kafaɗarta, sai kuma targaɗan da tayi a ƙafa garin hawa bene. Hajiya Madina tasha wuya sosai da ƙonewar da tayi, ba za'a kira ƙonewar da ƙarama ba dan round tayi babba, dan bayan sunyi 1week a asibiti na kwanciyar da akai da Zaytuna sai da suka ƙara 1week saboda caɓewar da ƙunuwar tata tayi, ashe ƙarfin hali take tayi. saboda tashin hankalin da suka ƙara shiga na ɓatan Hajiya Ramla, babu inda ba'a duba ba babu Hajiya Ramla, haka babu cigiyar da ba'ayi ba within that 2weeks amma babu amo babu labarinta, wannan ne ya ƙara firgitar da Hajiya Madina ta ƙara fita hayyacinta gaba ɗaya, ta mance ma da wani abu ciwo dake jikinta balle xafinsa, dan idan ma tace zata bi ta kan ciwon tausayin Zaytuna da Turaki ba zai barta ba. cikin wannan hali da suke ne na jimamin ɓatan Ramla kowa ya ƙara tabbatarwa da Alƙali Dikko yayi sa'ar mata a duniya, situation ɗin da Hajiya Madina ta shiga a silar ɓatan Hajiya Ramla ba zai faɗu ba, yanda kasan wacce uwarta ta mutu, abinci wannan bata ci sai an mata da gaske, kuka kuwa da ace ruwan hawaye na ƙarewa tuni nata ya jima da ƙarewa. Hajiya Madina macece ta gari, me kyawun zuciya, wacce babu algus a tare da halinta, wacce take zaune da kowa lafiya take kuma nuna kowa nata ne, bata ƙyamar kowa kuma bata munafurta kowa, dan sau tari akan cewa da Hajiya Ramla matsalar kishiyarki ɗaya ne, bata iya munafurci ba. ita kanta Hajiya Ramla tasan tayi sa'ar abokiyar zama, abunda kowa ke faɗa mata kenan tunda aka auro Madina, shi yasa suke zaune lafiya babu fitina, babu faɗa balle tashin hankali, kansu a haɗe kamar waɗanda suka fito ciki guda. tunda aka haifi Turaki Hajiya Madina ta mayar da shi kamar ɗan cikinta, idan ba sani kayi ba ba zaka taɓa cewa ba ita ta haife shi ba, an aurota dalilin ra
🏠