NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 98 of 323

babu wata matsala, zuwa safiya zamu tafi gida". sai bayan wucewar sakanni goma sha biyar da maganar Maama sannan Fulani tace,"Allah kiyaye gaba. zamu koma". ta faɗa tana miƙewa, su kai sallama da Granny, Hajiya Madina kuma ta tafi yi mata rakiya. Turaki yabi bayansu da kallo, yana ji a ransa Hajiya Madina itace rayuwarsa. hoton wancan lokacin ya shiga haska masa, yana ɗan ƙarami bai san mene mutuwa ba amma yasan me wutar dake ci a cikin ɗakin zata iya haifar musu shi da ƙanwarsa, kasancewarsa yaro me bala'in wayo, kuma tun yana buga ƙofa yana faɗin,"Mum please come and open us". har ya gaji ya daina faɗa. ya shiga toilet da gudunsa ya ɗebo ruwa a ƙaramin cup yazo ya dinga watsawa labulen da ya kama da wuta amma wutar bata mutu ba. ya ɗauko abu ya taka yana leƙa cikin gadon da Zaytuna ke kwance yana so ya kamo hannunta ya ɗaukota su fita a ɗakin amma ya kasa, ƙarfinsa da tsayinsa ba zai kai ba. idan ya juya yaga wutar ta ƙara kama wani wajen sai tsoro ya daɗa kamasa, ya ƙara zuwa ya buga ƙofa in ya kira Mum yaji shiru sai ya dawo ya kuma taka abu a ƙoƙarinsa na ɗauko Zaytuna amma sai ya kasa, sai ya ƙara saka kuka yana ta kiran sunan Mum. daga ƙarshe kawai sai ya zauna a gefen gadon ya kifa kai da gwiwa yanata kuka, kuka mai ban tausayi, yana ta kallon hoton Mum acikin idonsa, yana ji a zuciyarsa babu daɗi, yaro ne shi amma ya san me ake nufi da laifi, dan haka ya dinƙa jin haushin kansa akan laifin da yayiwa Mum ba tare da ya sani ba, laifin da gashi har ya shafi ƙanwarsa da yake tsananin so. lokacin da ya saddaƙar shi da ƙanwarsa sun mutu, saboda hayaƙin da ya gauraye ɗakin da ba a iya ganin komai ta yanda wutar ta ƙara yawa saɓanin da kaɗan take ci tunda gefen labule ta kama, amma zuwa lokacin har ta kama katifa ƙauri yana tashi, ɗakin yayi duhu, shi kuma sai tari yake yi yana ta so yaja gadon Zaytuna amma ba zai iya ba. a lokacin ne kuma hayaƙin ya fallasu acikin gidan, mai gadi yaje ya sanarwa da Hajiya Madina cewa wuta ta kama a ɓangaren Hajiya Ramla, kuma ya ga ta fita tun ɗazu ita kaɗai babu yaran. jin wannan batu yasa Hajiya Madina barin ɓangarenta a rikice ta yo ɓangaren Hajiya Ramla, ta shigo ɓangaren tana taƙwala kiran Your Excellency, sai taci karo da wayarta a kan dining. wannan yasa Hajiya Madina ƙara hargitsewa ta haye sama da sauri, garin hawan ta zame ta faɗi, amma bata kula da faɗuwar ba ta tashi tana ɗingishi ta wuce direct zuwa ɗakin Hajiya Ramla, tana zuwa ta murɗa handle taji ƙofar a rufe, gashi tana gani daga ɗakin wutar ke ci, sai tabi ta rikice ta koma ƙasa ta kira me gadi tana daɗa tambayarsa ya tabbata yaga fitar Her Excellency, yace ya gani tun kusan minti biyar ma kenan, amma ba da yaran ta fita ba, kuma bama da mota ta fita ba. Hajiya Madina ta ɗora hannu aka tana salati, suka dawo saman ita da me gadi, kuma suna zuwa suka jiyo kukan Turaki yana buga ƙofa yana cewa,"Mum please come and open us, please Mum, the fire is coming closer to us". jiyo muryarsa yasa Hajiya Madina yin tangaltangal zata kife a ƙasa, tana duban me gadi tace,"my children are inside Malam Hamisu. innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, taimaka min Malam Hamisu ƙofar a rufe take". ta faɗa tana fashewa da matsanancin kuka tana kama handle tana jijjiga door ɗin. Malam Hamisu ya murɗa handle ya tura ƙofar yana duddukanta amma taƙi buɗewa, sai daga baya tunanin ɗauko spare key ya zowa Hajiya Madina. ta kira me aikinta tace tayi gaggawar zuwa side ɗin Baffa ta ɗauko duka keys ɗin da ta gani acikin bedside drower, kuma cikin mintuna kaɗan sai gata ta kawo. Malam Hamisu ne ya iya buɗe ƙofar don ita ba zata iya ba saboda yanda jikinta ke rawa gaba ɗaya. jin an danno ƙofa da ƙarfi hakan yasa Turaki ya tsorata, ya buɗe bakinsa ya kira sunan Mum da ƙarfi yana ƙara fashewa da kuka, sai yaji muryar Hajiya Madina saɓanin wacce yayi tsammani. ba zai iya tuna abinda ta dinƙa faɗa ba amma ba zai manta yanda ta dinga lalubensu ba acikin hayaƙin har ta gansa, tana zuwa ta janyo shi zasu fita sai ya tirje yana ce mata,"Maama Jaishuna". tsananin firgicewa da rashin sanin inda kanta yake bama tasan me yake faɗa ba har suka fito daga ɗakin, tari ya sarƙe shi maganarsa ta maƙale, Hajiya Madina ta dinƙa jijjigasa har Allah yasa tarin ya tsaya. kuma sai a sannan ta gane me yake cewa, lokacin da ta rungume shi tana kuka sosai, ya tureta a jikinsa yana nuna mata ɗakin yana cewa Baby Jaishuna. ta na fuskantar abinda ya faɗa ta kunce goyon dake bayanta wanda ta manta ma da shi, ta koma ɗakin a sukwane tana kurma ihu tana zabga salati. within a minutes sai gata ta fito tana janye da gadon Babyn, don sai da ta fito ta ɗauko Zaytuna acikin bed ɗinta wacce a lokacin numfashin jaririyar ma ya ɗauke gaba ɗaya saboda uban hayaƙin da ta zuƙa. Malam Hamisu dake tsaye da yara a gabansa cikin ɗimauta yana dubanta ya ƙwala ƙara yana faɗin,"wuta a rigarki Hajiya". taji sanda ya faɗi cewar wuta a rigart
🏠