NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 97 of 323

atsa shi, taci gaba da rayuwa tare da su ko da ace ba zata so su ba, shi dai kawai ya dinga ganinta yana jin daɗi, yake yi mata duk wata kalar biyayya, ya kuma nuna mata zallar soyayyarsa, irin wannan soyayyar da ta ke only between child and his mother. alƙawarinsa ne daga zarar da ya sami job ba zai dinga barinta tana zuwa office ba, ta gama yiwa gwamnati aiki, shi zai dinƙa biyanta da kuɗin da yafi wanda take samu ba tare da tayi aikin ko da rubutu a takarda ba, alƙawarinsa ne zai nema mata wacce zata dinga kasancewa tare da ita idan baya kusa da ita, zai nema mata yarinya kamilalliya kuma kimtsatstsiya, irin yarinyar da ta san darajar uwa, irin wacce tasan kalar soyayya da kulawar da ya dace a nunawa uwa, irin wacca yasan ko da a bayan idonsa ba shi da haufin ba zata bari ko da ƙuda ya taɓa mahaifiyarsa ba. ya ƙara ɗago kai yana kallon Hajiya Madina, wacca a yanzu tayi ƙasa da kanta tana goge hawaye. sai ya rumtse ido sosai yana jin wani ɗaci a zuciyarsa. a hankali yace,"dan Allah Maama ki daina kuka a gabana, bana so, yana ɗaga min hankali...kiyi haƙuri ji nayi kamar idan na shiga room ɗin Mum zan ganta, naji ne kamar tana kirana a lokacin, dalilin da yasa na buɗe kenan...kuma dana shiga sai ban ganta ba, ban ganta ba ko da inuwarta sai hotonta". ta ɗago tana daɗa goge hawayenta da cewar,"me Babban suna bana so naga wani abu ya sameka, bana so ko kaɗan. amma wannan hawayen ba naka bane, na Ramla ne, ina ji inama na san inda take naje na dawo da ita, ta dawo muci gaba da rayuwa tare. ta zauna tare da ƴaƴanta ko sa sami kwanciyar hankali, babban damuwata shine rashin sanin halin da take ciki". Granny tace,"shekarun aka faɗa muku kwana 25 kacal, idan zaku yarda da ni ku yarda kawai, ko da ace zaku samu labarin Ramla, ina jin sai dai ku sami labarin mutuwarta". Maama tayi shiru tasa handky tana ƙara goge hawayenta tace,"in Allah ya yarda tana raye, me Babban suna yace yana ji a jikinsa tana raye kuma in a safe place". Granny tace,"ke komai aka faɗa sai dai ki faɗi view ɗin wani me Babban suna, to ai sai kuyi ta zaman jiran ganin dawowarta, haka zaku zauna har zuwa busa ƙaho, zai fi muku ku haƙura da ita kawai". Turaki yace,"insha'Allahu zata dawo". ya faɗa da sautin murya mai matuƙar ban tausayi. Hajiya Madina ta kallesa tace,"da ma da kanka ka buɗe ɗakin?". sai ya ɗaga mata kai alamar ehh. lokaci ɗaya zuciyarta taji rashin daɗi, taji tana dana sanin abinda ta yiwa Fillo, taji tausayin yarinyar ya kamata, taji ta ƙara son yariyar a ranta, taji ta ƙara ƙwaɗayin auren yarinyar wa Turaki, her only beloved son Muhammad Turaki. "Me Babban suna nayi zaton Fillo ce ta buɗe zata yi aiki a ɗakin, da ta kirani nazo naga condition da kake ciki sai na yanke mata hukunci me tsauri, tana ta faɗa min bata da laifi ashe gaskiyarta take faɗa min ni kuma naƙi sauraronta. Allah na gode maka da ban yanke hukuncin da zanzo ina da na sani ba, niyyata muna komawa gida zan sallamesu ita da Kakarta, a zatona duk itace silar halin da ka shiga, ashe dai ƙoƙarin taimakon naka take da gaske". Maganar takeyi yana sauroronta, idanuwansa kuma na gane masa Fillo a lokacin, yana tuno yanda ta dinga roƙonsa akan ya daina jiwa kansa ciwo, da kuma yanda ya ƙanƙameta yana neman taimako daga gareta, da sanin cewar in ya faɗa mata abunda yake buƙata zata taimaka masa kamar yanda ta saba, kamar yanda ta saba taimakonsa ba tare da ta san cewar ya sani ba, wannan tight hug ɗin da ya mata ji yayi kamar idan ya faɗa mata Mum ɗinsa yake so ta dawo masa da ita, to zata ce masa ya buɗe idonsa gata ta kawo masa ita, amma sai lamarin ya kasance ba haka ba. sai ya lumshe idonsa yana daɗa hasko Fuskar Fillo, ta ya zata dawo masa da Mum idan ya faɗa mata?, ta ina zata fara kamar yanda bai san ta yanda ta fara wancan taimakon akansa ba?, sai ya matse idonsa yana jin wani abu da bai san menene ba yana tsarga masa. tsawon lokaci Granny da Maama suna jimanta rashin Ramla tare da su, Turaki duk yana jinsu har lokacin idonsa na a rufe, amma tunaninsa na can wani wuri na daban. akayi sallama a room ɗin, Hajiya Madina ta miƙe da sauri daga kan kujerarta tana yiwa Fulani matar me martaba barka da zuwa. cikin takun ƙasaita da girman izza ta ƙarasa shigowa ta nemi kujerar da aka nuna mata ta zauna. hular alkyabbar dake kanta ta ɗage tana duban Turaki kafin tace,"Allah ya ƙara lafiya". tai maganar kamar tana jin nauyin bakinta, kuma kamar bata so ba. ya ɗan rissina kansa cike da girmamawa ya amsa mata,"amin ya Allah, na gode Mami". Hajiya Madina ma tana rissinawa ta ƙara ce mata,"sannu da zuwa". sai da ta ɗauki minti ɗaya kan tace,"yauwa. ashe Muhammad bai ji daɗi ba, to Allah ya inganta lafiya, ina ganawa da baƙi Mai Martaba yake cewa mu shirya mu taho hospital... accident ya ƙara yi?". Hajiya Madina tace,"aa ba accident ba ne, rauni ne ya samu acikin gida, amma yazo da sauƙi ma tunda glass ɗin da ya fashe ne ya soke shi a goshi, but Drs ɗin ma sunce
🏠