NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 96 of 323

shafeta, ka samawa kanka lafiya, ka samawa kanka kwanciyar hankalin daka rasa tun ranar da tasa ƙafa ta tafi ta barku...". Turaki ya katseta da faɗin,"Granny do you know what you are saying?". ta jijjiga masa kai,"i know Muhammad, i mean you should forget Ramla in your life, just like she forget you". sai ya kwantar da kansa yace,"Granny hannunka baya ruɓewa kace zaka yanke ka jefar". tace,"idan ta kama a yanke sai a datse shi a huta, komai ai kamawa take". kansa ƙasa yace,"but karki manta duk lalacewar uwa uwa ce, how can i forget her?, na fa manta da ita da abinda ya shafeta kike cewa?, how?, ki daina faɗar abinda ba zai yiwu ba Granny". yanayin yanda yayi maganar sai yay mugun bata tausayi. sai kuma ya rumtse idonsa zuciyarsa na tafarfasa,"even though I was six years old at the time. Granny har yanzu ina ganin hoton komai tar acikin kaina, ina kallon lokacin da tasa ƙafa tayi tafiyarta ta barmu ba tare da ta ko waiwayi kukan da nake ba, bata dubi kukan Zaytuna dake naɗe aciki showel ba, tayi tafiyarta ta barmu, as if ba daga jikinta muka fito ba, as if ba ita ta tsuguna ta haifemu ba, kamar ba da auren sunnah ta samar da mu ba, inda ace wutar ta cinyemu fa?, da ace mun mutu fa?, da Allah bai kawo Maama a lokacin ba fa?". lokaci ɗaya sai hawaye ya shiga sakko masa akan kuncinsa, cikin kunnensa yana jin sautin kukan Zaytuna da ta dinga tsalawa a lokacin, yana jiyo nasa sautin kukan dake fita da harufan sunan Mum. yana jin komai kamar yanzu yake faruwa, tana fa kallon yanda wuta ke ci a ɗakin, amma ta tankaɗasa ya koma ciki ta rufe ƙofar ta barsa daga shi sai jaririyar dake cikin gado kusa da inda wutar ke daɗa kamawa, tayi tafiyarta ko tausayinsu bata ji ba, me suka mata?, har yanzu tambayar da yake ta so yayi mata kenan, ya ganta ya tsuguna agabanta ya tambayeta zunubin da suka aikata mata, sannan sai ya roƙar musu yafiyarta, idan ta yafe musu sai ya bata labarin abinda yake ɓoyewa kowa, kowa banda Bello da Zaytuna. to aina zai ganta?, yaushe zata dawo?. _a dai ci gaba da haƙuri, da zarar mun kammala biki shikenan....ina godiya da kulawarku._ *Please Comment and Share and Vote.* *LULLUƁIN BIRI* *©️Halima h.z* _Please avoid any mistake._ *24* "nima da nake mahaifiyarta na manta da ita, na manta na taɓa haihuwar ƴa me kamarta ko sunanta, na jima da cireta a sahun ƴaƴana. saboda haka kaima ka manta cewar ita mahaifiyarka ce tunda har ta iya manta da cewar tana da ƴaƴa, ka riƙe wadda ubangiji ya dubeku ya tausaya muku ya baku ita ta maye gurbinta...Allah ne kaɗai yasan hikimarsa akan hakan, wataƙila ba zaku sami tarbiyya da soyayya daga wurin Ramla ba shiyasa ya ƙaddara faruwar wannan lamarin". jin maganan Granny ɗin yasa Turaki buɗe idanuwansa, ya buɗe su a daidai lokacin da Hajiya Madina ke shigowa ɗakin. kallo ɗaya yayi mata yaji tsananin tausayinta ya kamasa, ya ƙara jin ƙaunar matar a ransa, haka ne, basu sami soyayyar mahaifiyarsu ba, kuma basu samu tarbiyya daga wurinta ba, amma Allah ya basu wacce tayi musu dukkan waɗannan gatan, wanda iyakacin abinda wadda ta haifesu zata musu kenan. hijab ɗin dake jikinta fuskarsa ma a karkace ta saka, ya bita da kallo har sanda ya sauke ƙwayar idonsa kan bayan hannunta. tabon ƙonuwar da tayi tsawon shekaru 25 har yanzu yanan bai ɓace gaba ɗaya ba, sai kawai yasa hannu ya goge hawayen da ya sakko masa a lokacin da bai sani ba, idan bai so Maama ba wa zai so?, idan bai ƙauna ce ta ba wa zai nunawa ƙauna?, idan bai kula da ita wa zai bawa kulawarsa?, wataran har yana jin yafi sonta fiye da wadda ta kawosa duniya, har yana jin tausayinta fiye da yanda yake tausayin Mum ɗinsa. Hajiya Madina ta ƙaraso bakin gadon, Granny na amsa sallamarta, jikinta duk a sanyaye taja kujera ta zauna, ta dubi Turaki da muryanta da yay ƙasa tace,"sannu me Babban suna". ya amsa da,"yauwa Maama, thank you so much for your care". ganin yanda ta ƙura masa ido sai ya sauke idonsa ƙasa, yana jin nauyinta na shigarsa, ya sani yayi mata laifi. laifi har guda biyu a rana ɗaya, ya saɓa umarninta na cewa duk inda zai ke tafiya yanzu suke tafiya tare da Khalil, sannan yazo yasa kansa a situation ɗin da ya shiga, saboda wannan condition ɗin da yake shiga ne a duk sanda ya shiga ɗakin mahaifiyarsa shi yasa ba'a so ya shige shi, yasa ma aka rufe ɗakin gaba ɗaya Baffa ya ɓoye key ɗin, ya gargaɗe shi da ko da wasa kar ya ƙara tunkarar ɗakin, tunda duk sanda ya shiga yana tunawa da komai da ya faru a ranar da Mum ta tafi ta barsu, sai ya dinƙa jin komai tamkar a lokacin yake faruwa, sai ya dinƙa ganin yacca wuta ta ke tashi da yanda ya dinga kuka Zaytuna ma tana yi, sai yake jin kukan a cikin kansa. hakan sai yasa yake jin wani irin raɗaɗi, ya dinƙa jin wani irin abu a tare da shi da ba zai iya kwatantasa ba a yayin da yaga hotonta. idan yana ganin hotonta sai yaji kamar ya cirota daga cikin hoton ta zama a zahirance, yay mata kallo na zahiri sai ya rungumeta ta yanda ɗumin jikinta zai r
🏠