NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 95 of 323

anta na dukan bango, lokaci ɗaya taga giftawar wasu taurari acikin idanuwanta. abunda kawai zata ce ta ƙara ji shine Hajiya Madina ta mata gargaɗin cewa,"duk abunda ya sami ɗana, duk abunda ya sami lafiyar ɗana sai naga bayanki Fillo, tabbas sai kin ƙwammace ina ma baki zo duniyar nan ba". daga nan bata ƙara jin komai ba kamar yanda bata ƙara ganin komai ba na tsawon wucewar minti goma sha biyar. kuma sanda ta dawo hayyacinta daga buguwar kan da tayi, sai taga babu kowa a ɗakin sai ita ɗaya. tsawon minti biyar tana kuka, a hankali ta dinƙa kewaye ɗakin da kallo, babu komai acikinsa face shirgin takardu dake cikin locker, sai kuma gadon jarirai irin wanda ta taɓa gani a ɗakin Fulani, sanda Kaka ta zauna yiwa Gimbiya Zahra wankan jego. wanne abu ne acikin ɗakin da ya haddasa shigar Turaki situation ɗin da ta zo ta same shi aciki?, ina abunda yasa ba'a so a buɗe ɗakin?. ta kalli komai kuma bata ga komai ɗin da zai zama dalili ba. taimakonsa tayi, kuma taimakon take da niyyar yi masa, amma ga da abinda aka saka mata da shi, ya za'ai ta manta?, waye zai taushi zuciyarta akan abinda ta ƙudurce na ramuwa?, Amir ne kawai, kuma yanzu babu Amir a cikin rayuwarta, tsawon watanni huɗu sai taji tana kewar Amir a yau. sai ta runtse ido tana jin zafi a zuciyarta, ta miƙe tsaye da ƙyar tana dafa bango saboda hajijiyar da take ji, ko'ina na ɗakin take bi da kallo, so take taga illarsa, ba zata taɓa barin ɗakin nan ba sai taga illarsa da kuma dalili, wannan dalilin da ya haifar da komai. ta miƙe da ƙyar ta tafi tana jan ƙafarta dake yi mata zugi har ta ƙarasa gaban enlargement. kallon matar take yi da kyau cike da nazari da son gano wani abu amma ta kasa, abu ɗaya ta fahimta matar nan na da alaƙa me ƙarfi da Turaki, saboda tsananin kama, kamannin da suka zama kamar an tsaga kara, sai dai irin alaƙar da take tunani zuciyarta na faɗa mata cewa ba ita bace, wannan matar bata yi kama da wacce ta ajiye ɗa kamar Turaki ba, shekarunta kaɗanne, kuma ko da auren ƙauye aka mata baici ace ta haifi ɗa kamarsa ba balle har ta haife shi, ta haifi Zaytuna. ba ma wannan ba, idan ma tayi tunanin ita mahaifiyarsu ce to Hajiya Madina fa?. ta dafe kanta da take jin kamar zai fashe tana saurin dafa gadon jariran, bata buɗe idonta ba har sai da ta daina jin juwar, idonta ya sauka acikin gadon jariran, kan award frame dake kan bargon jariri, tasa hannu ta ɗauko tana kallon award frame ɗin, tayi concentrating akan hoton jiki da sunan jiki. *her Excellency RAMLA MUHAMMAD TURAKI*, sunan da yake rubuce a jiki kenan. wai wace wannan matar?, mene alaƙarta kuma da sunan Turaki?, *MATARSA!*, haka zuciyarta ta faɗa mata, kuma tabbas hakan yake, amma ina take?, mutuwa tayi?, rabuwa suka yi?, take anan zuciyarta ta warware mata dalilin da yasa ba'a son buɗe ɗakin, da kuma dalilin da yasa Turaki shiga critical condition. saboda wannan ɗakin na da alaƙa da ita shiyasa ba'a so a buɗesa, sannan ganin hotonta na fama ciwon da ta jiwa Turaki a zuciyarsa, wannan ciwon da tabonsa ya kasa goguwa daga garesa. wanne irin ciwo ne?, me tayi masa wanda ya kasa mantawa?. ta ƙara ƙulle idonta for 1minutes sannan ta buɗe tana ƙarewa gadon jariran kallon, ta tabbata wannan room ɗin shine silar komai, kamar yanda gadon jariran nan ke da alaƙar komai, kenan idan tunaninta ya bata dai-dai *ƊA* ne silar komai, jaririnsu!, to ina jaririn?, kuma itama uwar tana ina?, ta mutu ne?, ita ɗan da suka mutu?, kenan wannan shine ciwon dake manne a zuciyar Turaki?. sai kawai Fillo ta sauke numfashi tana hurar da iska a bakinta, ta koma ta isa gaban englargement din ta cirosa, sannan ta dawo ta ɗauko award frame ɗin ta fice da su daga ɗakin. *6hours pass, Miyyetti Hospital, Room 05.* cikin vip room ɗin, Turaki ne jingine a jikin pillow ɗin da aka saka masa a bayansa, goshinsa ɗaure da bandage, an naɗe wurin da ya ji ciwo da shi sanda yake dukan kansa ajikin glass. gefensa kuma wata farar tsohuwa ce kamar balarabiya a kan kujera, da siririn farin medical glass a idonta, tayi jugum tana ta kallon jikan nata. lokacin da aka kawo Turaki da Zaytuna asibiti, lokacin ta kira wayar Baffa take sanar masa tana ta kiran wayoyin yaran bata samu, har ta babarsu Hajiya Madina ma ta kira bata samu ba, shine Baffan ke faɗa mata halin da suke ciki na cewar suna asibiti, Zaytuna da Muhammad duk sun suma, kuma for morethan 15minutes ba wanda ya farfaɗo acikinsu. a lokacin Granny ta kira ɗanta tace a yanzu ba da ɓata lokaci ba tana son zuwa nigeria, kuma a awa biyar da minti hamsin da biyar sai gata ta a asibitin cikin tashin hankali tana ta kuka, sai dai ko lokacin da tazo ɗin duk sun farka, Zaytuna ma har ta miƙe, shine dai ke kwance saboda ciwon dake jikinsa. Granny ta numfasa tace,"Ramla dai ta cuci kanta, dan ba zance ta cucemu ba...so do you know what i want from you Muhammad?". Turaki ya haɗiye abu ya kalleta yana jiran cewarta. "Muhammad ka manta da Ramla, ka manta da ita da abinda ya
🏠