NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 94 of 323

nufin ka zama mara ji ba kamarsa, na sani da takurawa ace lallai duk inda zaka je sai da ƙaninka alhalin ka mallaki hankalin kanka, amma ka sani ni uwa ce da ba zan so wani abu ya cutar da ɗana ba, ya kamata ka tuna da akwai masu faraurar rayuwarka a kullum, dalilin da yasa nace duk sanda ka fita ya zam kana tare da Khalil ko Bello duk da nasan dabarata bata isa ta hana faruwar abunda Allah ya shirya ba. amma dai atleast kasancewarka tare da wani zai sa suke tsoron tunkararka. kuma sai da kayi min alƙawarin ba zaka saɓa umarnina ba akan hakan ba, Me Babban suna me yasa yau rana ta farko ka saɓa umarnina?, Khalil yace ko minti 2 baka yi a office ba ka fita, Bello yace kana ɗaukosa a airport kuka rabu. ina ka tafi tun bayan rabuwarku?, me yasa baka dawo gida kaci abincin rana ba?, me yasa kaƙi ɗaga wayata?, me yasa kake son haddasa ciwona ya tashi?, me yasa tun ɗazu ina maka magana kayi min shiru?, rashin maganar na menene?, lafiya?". tunani da lissafi dake a cikin kan Fillo ya tarwatse, gabanta yay dukan tara-tara, kallon Turaki take yi tana tuna irin tarin tasa soyayyar wa mahaifiyarsa, zuciyarta na faɗa mata taje ta same shi ta faɗa masa Maama ce, Maama na son yin magana da shi, zai farka idan yaji hakan, tabbas zai farka. ta isa gabansa tana jijjigasa a hankali daidai kunnensa tana faɗin,"ka tashi ga Maama". a zatonta ko jin hakan zai sa ya farka daga dogon suman da yayi, amma inaa kamar ma da gawa take magana. sai kawai wani kuka ya kubce mata. cikin kiɗima Hajiya Madina tace,"innalillaihi wa'inna ilaihi raji'un...". ko salatin bata ƙarasa ba Fillo tace,"Maama ki zo". ta faɗa tana kuka sosai. daga ɓangaren Hajiya Madina ta zabura ta miƙe daga kan kujera, cikin gigita da tsananin tashin hankali na farat ɗaya, me kunnenta yake ji ne?, kamar kukan wani take ji kuma kamar ana so ace mata tazo ga Turaki babu lafiya. "waye ke magana?, ina Muhammad ɗin?, ke wacece?". kukan Fillo ya ƙaru tace,"Maama ni ce, Hammah ɗin ya faɗi ya suma Maama kizo da sauri". wayar dake hannun Hajiya Madina ta nemi ta faɗi a ƙasa, Samha da idonta ya kai wurin tai saurin taro wayar sanda ta sauka daga saman gadon. ta taro wayar a lokacin da itama Hajiya Madina ke neman faɗuwa, Nihal tai saurin riƙota. Samha tace,"Lafiya Maama, menene?". Hajiya Madina ta kalleta ido a waje, a hankali ta kalli Nihal, sannan ta kai idonta ga Zaytuna wacce tayi tsaye ƙeƙam. sai kuma ta dawo da idonta ta sauke akan wayar tana kallon call ɗin dake tafiya, Hammah aka ce mata alhalin ga ƙannensa anan tare da ita. cikin neman fitar hayyaci tace,"to wace me magana a wayar?, wai Hammanku ya suma, to aina?, garin ya?". ta wurga tambayoyin ga Samha. duk su ukun suka maimaita,"Hammah ya suma?". Hajiya Madina ta ɗaga musu kai kawai hawaye na sintiri a saman fuskarta. "hello, dan Allah wake magana, ina me wayar yake dan Allah?". Nihal ta faɗa acikin wayar bayan ta amshi wayar daga hannun Samha. babu amsa sai kuka dake tashi kawai, Zaytuna ta silale a wajen, Nihal tayi kanta da sauri. Samha ta ɗau wayar ta kai kunne, dan tuni Hajiya Madina tayi mutuwar zaune, ta koma kamar me paralize idonta a wuri ɗaya kawai yake, jinta take kamar rayuwarta ta ƙare, kamar shikenan ta gama aiki. daga ɓangaren Fillo tace,"Hammah ne ya suma". Samha ta waiga taga sauran sisters ɗinta suna nan, ɗaya ta suma ɗaya na ƙoƙarin ganin ta sumen ta farfaɗo. to wace ke faɗin Hammah ya suma?. sai ta dakewa faɗuwar gaban da take ji tace,"to waye yake magana, kuma wanne Hammah ɗin?". Fillo na ƙara jijjiga Turaki tace,"ni ce Fillo, Hammah Turaki ne ya suma Maama, tun ɗazu yaƙi yay motsi kamar ya mutu". a matuƙar razane Samha ta miƙe tsaye tana faɗin,"what! mutuwa?, dan uwarki ke kina ina?, ta ya kika san abinda ya faru da Hamman'mu?". jin furucin Samha yasa jikin Fillo yin rawa a lokacin zuciyarta na faɗa mata shikenan tata kuma ta ƙare, ita dama ta sani ita za'a ɗorawa alhakin faruwar komai. "Fillo aina?, aina ya suma?". Hajiya Madina da ta amsa wayar take tambaya kuka na ƙwace mata. "Maama ɓangaren su Adda Zay...". bata ƙarasa ba taji alamun faɗuwar waya a ƙasa. kuma zata iya cewa rabin second ne ya kawosu, dan ganin su kawai tayi tsaye akanta. Hajiya Madina ta fizgo Fillo ta miƙe tsaye, ta zabga mata mari a fuska, marin da yasa jinta da ganinta suka ɗauke na wucin gadi. kamin ta dawo dai-dai ta ƙara ɗauketa da wasu marikan har uku. "uban wa ya buɗe room ɗin nan?". babu abinda Fillo ke ji a lokacin balle ta iya bada amsa. "ba magana nake miki ba, ban yi muku iyaka da wannan room ɗin ba?, bance duk sanda zaku yi aiki babu ruwanku da taɓa wannan ɗakin ba?, wa ya baki key ɗinsa?, me yasa baki hanasa shigowa ba?, kin buɗe baki kin yi min magana ko sai nasa ƴan sanda sun kamaki kin ƙare rayuwarki a bayan kanta?". Fillo na kuka tace,"wallahi Maama bani na buɗe ba, nazo wucewa ne...". bata barta ta ƙarasa maganar ba tasa bayan hannunta ta kifar da ita a ƙasa, Fillo ta zube a ƙasan tiles k
🏠