NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 93 of 323

n wayarsa akan locker, ta isa wajen ta ɗau wayar hannunta sai karkarwa yake. ba security a wayar, dan haka tana buɗewa kai tsaye lambar Maama ta laluba, bata ma san ta yanda akai ta iya wayar ba tunda ba taɓa riƙe waya tayi ba a rayuwarta, ko wayar Yami ma tsakaninta da ita in Amir ya kira Maijidda ta kawo mata tasa mata a kunne, amma ko ɗaga waya bata taɓa yi da kanta ba. scrolling kawai take a ɓangaren miscalls amma ta rasa lambar da ta dace ta kira, bata san wani Bello Ƙaraye ba, haka bata san lambobin biyun da babu suna a jiki na waye ba, fita tai daga ɓangaren call ta shiga contact, take taci karo da sunan My world, cikin sauri ta danna kiran ya tafi. daga can ɓangaren Hajiya Madina da ke zaune akan kujerar dake cikin ɗakinta. ƙafafunta a harɗe tana jin yanda zuciyarta ke matsewa, tana jin yacca zuciyarta ke faɗa mata kamar ba zata iya komai ba, tana jin yanda idanuwanta ke faɗa mata kamar ba ita ta haifi ƴaƴan dake zaune a gabanta ba, tana jin yacca ƙwaƙwalwarta ke faɗa mata rayuwar Turaki ita tafi cancanta da ta ingata sama da ta sauran, cikin kanta na lissafa mata kamar yanda take jin bata da kowa a duniyarta sai Turaki, haka shima Turaki ke jin ba shi da kowa a duniyarsa sai ita, ita ɗaya jallin jal. ƙwayar idonta ta wulƙita ta kalli Zaytuna, sannan ta kalli Nihal, tukunna ta sauka akan Samha, duka Yaran suna daga kan gadonta ne suna hira cike da soyayyar junansu. Samha kawai take iya gani a lokacin, kallon yarinyar take da irin kallon da ita kaɗai tasan ma'anarsa, ta kuma san manufarsa, ta kuma san lissafin da ƙwayar idonta ke yi akan yarinyar, ta kuma san ciwon da kallon nata ke hifarwa da ƙwayar idonta. da ace zata iya, tabbas da tace komai ɗin da take ji take gani ƙarya ne, to amma bata isa ba, bata isa ta kira abubuwan da tasan suna tafiya ba a matsayin ƙarya, ita gaskiya take bi, kuma gaskiyar ta sani, kuma gaskiyar zata bi. sanda ta rufe idonta tana sauke wata nauyayyar ajiyar zuciya, sannan ne wayarta dake kan cinyarta tayi ƙara, ta ɗaga tana kallon screen ɗin da sunan THE BEST ke yawo ajiki. lokaci ɗaya taji duk wani ɗaci da ɓacin ranta ya gushe, tana jin wani ɓari na damuwar da take ciki ya yaye, fuskarta ta bayyana jin daɗin ganin kiran nasa, sai ta ɗaga tana faɗin. "Me Babban suna kana ina?, ina ta kiran wayanka baka ɗauka ba, na kira Bello yace bakwa tare, ina ka tafi?, Khalil yace baka je office ba yau, ina fatan kana cikin ƙoshin lafiya, duk inda kake ka dawo gida yanzu kaji, ina nan na kasa samun nutsuwa tun kiran farko da nayi maka ban samu ba, yau na kiraka yafi sau goma kiran baka picking, tukunna dai kayi lunch?". maganar take muryarta na bayyana tsananin damuwar dake ƙunshe a cikin ranta, ba don komai sai dan rashin sanin halin da yake ciki tun safe da ya bar gida. haka take ita, indai ya fita a gida basa 1hour basu yi waya ba taji ya lafiyarsa, idan kuma yana gida to jiddan walahairan yana part ɗinta, suna tare ko a parlo ko kuma a bedroom ɗinta, sai dai idan ranar yana jin miskilancinsa har da ita to sai dai ita ta bisa part ɗinsu. ta kan tsokane shi da cewa,"Hamman'su kana juya ni kamar waina a tanda". Fillo da ke tsaye tana sauraren maganar Hajiya Madina, tausayin matar yay bala'in kamata, sai ta kasa yin ko da motsi, tai shiru ta kasa yin magana, tabi inda Turaki yake yashe kawai tana kallonsa, me yake faruwa da rayuwarsa ne?, me zata faɗawa Hajiya Madina yanzu?, ya zata yi idan taji a halin da ɗanta yake ciki?. sai ta tuno yacca Hajiya Madina ta shiga tsananin tashin hankali a wata rana da ya yanke da wuƙa yana yanka lemu, ta dinga kuka akan ɗan jinin da ya zuba daga jikinsa, ta tuna yanda Hajiya Madina ta koma bata iya nutsuwar minti ɗaya babu Turaki a kusa da ita a lokacin, ta tuna yacca duk bugawar sakan, duk wani motsi nasa sai tace,"menene me Babban suna?, me kake so?, me zan maka?, ciwon yana zafi?, sannu kaji, Allah ya baka lafiya". haka ta dinƙa ririta shi kamar jariri sabuwar haihuwa a lokacin. sai Fillo taji inaa ba zata taɓa iya kasassaɓar sanarwa da Hajiya Madina halin da Turaki yake ciki ba a yanzu, ba zata iya ba har ga Allah, bata son taga uwa ta shiga tashin hankali, balle kuma Uwa irin wannan da lokaci ɗaya take fita daga hayyacinta akan ɗan da ta ƙwallafa rai akansa duk kuwa da tana da wasu Ƴaƴan da Allah ya bata. Hajiya Madina ta rufe ido ta buɗe tana kallon agogo, ƙarfe biyar na yamma, yau watarana ce da ta kafa tarihi a tsakaninta da Turaki, rana ta farko da Turaki ya saɓa umarninta a iyaka tsayin rayuwarsa, to amma me yasa?. sai kawai ta rufe ido ta ƙara buɗewa tana sauke ganinta a daidai lokacin da agogo ya nuna biyar harda minti ɗaya, sai taji ranta ya ɓaci. kuma cikin nuna ɓacin ran tace,"baka taso a stubborn ba, kuma duk cikin ku shida kai nafi karewa daga duk abinda zai sa ka zama stubborn, amma me yasa sai daka girma?, kana so ka zama Stubborn kamar Khalil ko?. saboda nace duk sanda ka fita ya zama kuna tare da shi ko ina zaka je, ba wai ina
🏠