NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 92 of 323

Turaki dana Zaytuna. _but who is she?_, tambayar da taiwa kanta kenan, kuma kafin zuciyarta ta raya mata wata amsa sai ganin Turaki tai ya miƙe tsaye yana toshe duka kunnuwansa biyu yana doka goshinsa a jikin glass da ƙarfi. tayi azamar miƙewa tana ruƙo shi tana faɗin,"ka daina, zaka ji ma kanka ciwo". ta faɗa cikin tashin hankalin da ta rasa na menene, kuma rufe bakinta kenan jinin dake fita a goshinsa ya zuba akan ƙirjinta. ta kalla jinin dake ƙirjinta, ta kalla jinin dake fitowa a goshinsa, idonta a waje tace,"ka bari". ta faɗa da wani mugun ƙarfi tana sa hannu da iya ɗan ƙarfin da take da shi ta fizgo shi daga bakin glass ɗin da yake tsaye, sai gasa a gabanta, taja hannunsa ta zauna da shi a ƙasa tana kunce ɗankwalinta ta ɗaure masa goshin. "menene? ka daina kukan to dan Allah, ka faɗa min me kake so?, me zanyi maka?, ka jira anan karka ƙara tashi zanje na kira Maama". ta faɗa kukan dake bakinta na fitowa. kuma sanda ta yunƙura zata miƙe lokacin ya janyota jikinsa ya rungume tsam yana kama hannunta ya toshe kunnensa da su. muryarsa na fitowa cikin muryar namiji mai rauni da faɗin,"don Allahhhhh, ki taimaka min". _Ayi Haƙuri dan Allah, mun shiga rububin biki, from this week har next week, babu zama kullum tafe ake, idan an zauna kuma hayaniyar ƴan taro ta hanaka sakat balle ka sami natsuwar typing, kuma kun san jiki da jini, mutum naso ya huta idan yay struggling. dalilin da yasa kuka jini ɗiff kenan, kuci gaba da haƙuri tare da min uzuri._ *Comment naku shi ne ƙwarin gwiwata.* *LULLUƁIN BIRI* *©️Halima h.z* *23* ya ƙara maimaitawa,"help me pleaseeee". ya faɗa yana ƙara ƙanƙameta. Fillo ta haɗiye yawun bakinta da ƙyar, ita bata taɓa jinta a jikin ɗa namiji ba ko da Yayanta Hamid. amma yau itace gaɓa ɗaya cikin jikin wani ƙaton ya ƙanƙameta, ƙanƙamar da tasa ta jin kasala, kuma tana ta ƙoƙarin ta fita a jikin nasa ta kasa. sai tayi shiru kawai tana sauraren yanda zuciyarsa ke bugawa, beat ɗin na fita da ƙarfin gaske, sai taji tana jin tsoro. muryarta a hankali tace,"taimakon me zanyi maka?". ta faɗa tana so ta raba jikin nata da nasa, lokaci ɗaya sai tsoronta ya ƙaru jin yacca jikinsa ya saki gaba ɗaya. ta fita daga jikin nasa a sanda ya tafi luu ya faɗi ƙasa, bata san lokacin da ta kurma uban ihu tana tallafo kansa da sauri. ta shiga girgiza shi tana cewa,"ka faɗa min taimakon me zan maka?, me kake so na maka?, Turaki ka tashi dan Allah". kuka take sosai tana cewa ya tashi, da dai ta tabbatar cewa ya suma sai ta miƙe a ruɗe ta fice daga ɗakin, har ta kai step na ƙarshe zata sauka daga stairs sai kuma ta fara tunanin idan ta tafi ta barsa shi ɗaya cikin wannan halin me zai iya faruwa da shi?. dan haka da sauri ta ƙara komawa har tana kusa zamewa, Allah ya taƙaita tsautsayi bata faɗo daga benen ba. yana nan a sumen har yanzu, tai kansa cikin kiɗima tana ƙara jijjigasa tana cewa,"ka tashi don Allah, ka tashi ka faɗa min duk abinda kake so zanyi, zan taimaka da ko menene ko da ace zan rasa raina ta sanadin hakan". duk wata dabara nata da tunaninta ya gushe a brain ɗinta, tayi dirshen a wajen tana ta kuka abinta, tsoronta Allah tsoronta ace mutuwa yayi, wa ya kashe shi?. sai kawai ta ƙara fashewa da kuka tana tallafo kansa zuwa kan cinyarta, tasa hannu ta share hawayenta tana ta maganganu ita ɗaya. "kar ka yi min haka dan Allah, kar ka mutu a sanda yake daga ni sai kai a wajen, za'a ce ni na kashe ka, wallahi haka zasu ce. kuma ni ban san komai ba, ban san me ya sameka ba, dan Allah dan Annabi ka farka karka mutu yanzu, ka farka ka faɗa min duk abinda kake so, ka faɗan duk kalan taimakon da zanyi maka, ni kuma nayi alƙawarin zan maka shi". ta ƙarasa maganar tana kifa goshinta akan nasa, sam sam bata san me ya kamata tayi a yanzu ba, abu ɗaya ta sani, shine ba zata taɓa fita ta barsa shi ɗaya a cikin wannan halin ba. can kawai sai taji zuciyarta na faɗa mata cewar ta kira waya, ta kira Maama ta sanar mata komai, to amma da wacce wayar?. ɗago da kanta tayi ta fara laluben aljihunsa dan ɗauko wayarsa, ta gama lalubenta bata ji komai ba sai wallet ɗinsa. tunaninta wayar ko tana cikin wallet ɗin ne, hakan yasa ta buɗe wallet ɗin da niyyar ɗaukowa, amma da mamakinta tana buɗewa taci karo da hoton mutum biyu, na Zaytuna da kuma Dattijuwar matar da ta gani a jikin wancan hoton. kanta ya ƙara ƙullewa ta rasa wanne irin tunani za tai akan lamarin dake yawo cikin ranta, yanzu ba lokacin buƙatar lallai sai ta san komai ba ne, yanzu lokaci ne na kuɓutar da Turaki da take ganin kamar rayuwarsa tana jingine da ita ne, warwarewar abunda bata sani ba shi yafi komai sauƙi a wajenta, idan ya farka zata zauna ta zana komai dake ƙulle cikin kanta a tsakiyar tafin hannunta, tukunna ta karance shi da zurfin tunaninta, idan lissafin nata yayi dai-dai, to ta tabbata daga nan zata warware komai a cikin sauƙi. cikin azama ta miƙe ta nufi hanyar fita sai Allah ya nufeta da gani
🏠