NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 91 of 323

ce komai ba, ya juya zai tafi muryata na ɗan rawa cike da tsoro tace,"na tafi?". yace,"a'a kiyi ta zama". daga haka ya wuce ya barta a wurin. ta bar ɗakin da kewar film ɗin da bata ƙarasa gani ba, kuma da ta koma ranar raba dare suka yi tana bawa Maijidda labarin film ɗin, bata ma san ya akai Zaytuna tasan ta kalli film ɗin ba. kanta a ƙasa tana wasa da yatsunta tace da Zaytuna,"Adda ban iya kunna laptop ɗin ba". Zaytuna tace,"kina buɗewa zata kama, Turaki is the password". tace,"tom". sai ta ƙara ce mata,"zaki iya ɗin ko na kunna miki?". tace,"zan iya Adda, Adda Nihal ta taɓa gwada min". Zaytuna tayi murmushi tace,"ranar da kika sa ta dinƙa mana mitar ƙauyancin da kika mata?". kunya tasa Fillo rufe fuska. bayan fitar Zaytuna babu jimawa ta kammala gyaran wadrobe ɗin, ta ɗauki ƙaramar trolly ɗin ta buɗe taga sabbin kaya ne kamar wancan time ɗin da ta bata. abaya guda huɗu sai riga da skirt na material guda biyu da na atamfa guda ɗaya. duka kayan kamar sai da akayi measurement ɗinta, dan babu alamar ma kayan ragesu akayi. cike da farin ciki ta mayar ta zuge zip ɗin, wannan ma rabawa zasu yi ita da Maijidda kamar yanda suka raba wancan. maimakon taja trolly ɗin sai ta ɗauka ta ɗora akanta, ta fito ta rufe ɗakin farin ciki duk yaƙi barinta. zata sauka a stairs sai taji kamar mutum na sauke wahaltaccen numfashi a cikin ɗakin da yake gaba dana Zaytuna. sai taji ta kasa tafiya, ta tsinci kanta da komawa da baya har ta iso ƙofar ɗakin, ta tsaya tana ƙara tabbatar da abunda kunnuwanta ke jiyowa. bata manta da wani lokaci ba da suka zo gyara ita da Ɗausiyya, Nihal ta ke ce musu su gyara kowanne room dake upstairs banda wannan da yake da coffee door, shi ba'a buɗe shi totally. for sure daga room ɗin take jiyo sautin, to anya kuwa daidai ta ke ji acikin kunnuwanta?, ai ranar har suka gama zaryarsu anan basu ji wani abu makamancin haka ba, ta tsaya tana Contemplating ta buɗe ko ta tafi, abunda kunnenta ke jiyowa dai ba na wasa ba ne, ba irin abunda mutum zaiji bane ya ƙyale ya tafi. sai kawai zuciyarta ta tsaya akan ta buɗe ɗin, ta sauke trolly daga kanta. tasa hannu ta murɗa handle na ƙofar room ɗin, door ɗin ya buɗe yana bada wani sautin ƙara. tsabar mamaki da tsorata Fillo sai taji kamar ƙafafunta ba zasu ƙara ɗagawa ba, tabi wurin da Turaki yake a yashe a ƙasan tiles dafe da ƙirjinsa, numfashinsa na fita da ƙyar. ruwan hawaye na sauka ta gefen idonsa, kawai sai taji kanta yayi wani irin nauyi, hawayen nasa ya ɗimautata, kamar wannan ace yana hawaye?, me ke damunsa?. bata san lokacin da ƙafafunta suka kaita gabansa ba gwiwoyinta suka durƙushe a saitin da kansa yake, ta kallesa taga kamar ma a sume yake, gabanta ya faɗi saboda yacca idonsa ya tsaya a wuri ɗaya cak baya ko motsi. ta kai hannu ƙasan hancinsa taji yana numfashi, sannan ta sauke wata nauyyar ajiyar zuciya. tausayinsa yay bala'in kamata, taya zata iya barinsa taje ta sanar da halin da yake ciki?, idan ta tafi me zai iya faruwa before ta dawo?, me zata yi don taimaka masa a wannan lokacin?, a yanzu kamin wani yazo?, sai taji cikin kanta kamar babu komai, dukkan wata dabara tata ta yanke mata, bata san me zata yi ba. acikin wani yanayin dake da wuyar fassaruwa tasa tafin hannunta me taushi ta shafa fuskarsa, sannan ta duƙo da kanta saitin kunnensa muryarta da rauni tace masa,"baka da lafiya? sannu, ka daina hawayen, bari naje na kirawo Maama". ta faɗi hakan tana ƙoƙarin miƙewa, ta yunƙura zata miƙe sai taji ya ruƙo hannunta ya dawo da ita. ƙwayar idonta ta faɗa cikin nasa a sanda hawayen ciki suka sami nasarar gangarowa kan kumatunta. a sanyaye tace,"zanje na kira maka Maama ne". sai taga ya girgiza kansa a hankali cikin ƙarfin hali. ta sake cewa,"to kana da magani a kusa na ɗauko maka?, aina zan ɗauko?". nan ma kansa ya girgiza mata a hankali. cikin dauriyar abinda yake ji acikin zuciyarsa. sai ta samu kanta da ce masa,"to me zanyi maka? me kake so?". sai taji ya ƙara damƙe hannunta sosai, ya sauke kallonsa daga kanta ya tsayar ajikin bangon dake facing nasu. ta tsaya kawai tana kallon gefen fuskarsa, tana jin yanda ruwan hawayensa ke ɗiga a saman skirt ɗin jikinta, tana jin yana ɗauke kansa daga ƙasa yana ɗorawa a saman cinyarta, tana ji yana ƙara damƙe hannunta, tana jin yanda wani abu ke fita daga tafin hannunsa yana shiga cikin nata, tana jin wannan zafin da ta tabbatar yana ji a zuciyarsa yana taɓa tata zuciyar. ta rumtse ido for few seconds sannan ta buɗe, ta buɗe tana bin inda yake kallo har sanda ta sauke kallonta gaba ɗaya akan ƙaton enlargement ɗin dake manne a bango. tayi mugun zabura da hoton da ta gani, ta tsayar da ƙwayar idanuwanta cak akan hoton tana ƙarewa dattijuwar matar dake jikin hoton kallo, ba sai an faɗa ba matar balarabiya ce, kallon matar take tana hango tsananin kamanni na Turaki dana Zaytuna a tare da ita, tun daga murmushinta har dimple ɗinta daya lotsa ciki sosai babu abinda ya banbanta daga na
🏠