NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 90 of 323

du Allah ki ƙara min bayanin wannan, ni ɗazu duk ban gane ba, ya saka turanci da yawa a maganar tasa". Fillo ta aje littafin, ta falli takarda ta shiga yiwa Ɗausiyya bayani turyan turyan kamar itace teacher ɗin. suna cikin yin karatun ne suka ji wayar ɗakinsu na ringing, Ɗausiyya ta miƙe tana ƙorafin ba za'a barsu su dinƙa hutawa ba, yanzu sai ace suzo suyi aiki yen yen yen. Fillo ta bita da kallo tana faɗin,"ke kuma da samun wuri, dama me kika zo yi idan ba aikin ba". Ɗausiyya ta ɗaga wayar, daga ɓangaren Zaytuna tace da ita,"ina Fillo?". tace,"tana waje tana karatu". tace mata,"kice tazo ta sameni". "tom Anty". ta faɗa tana ajiye wayar ta fito daga ɗakin. inda suke ta koma ta zauna ta ɗauki nata littafin tana sanarwa da Fillo saƙon. Fillo tace,"wacce Antyn?". tace mata,"Anty Zaytuna mana". Fillo ta miƙe tana faɗin,"au nai zaton Anty me dogon baki ce, wallah har gabana ya faɗi". Ɗausiyya tayi dariya tace,"idan itace ai ba zaki ga na dawo yanzu ba, da tuni tana nan tana surfa min zagi ni da iyayena kafin tace min kiranki take". Fillo ma tai dariya tace,"ba kya nan ai ɗazu aka ce mana shegu masu warin baki". Ɗausiyya tace,"sai kika mata shiru baki yi mata rashin kunya ba?". Fillo ta harareta tace,"ai tunda na faɗa miki sai kije ki mata tunda you are the boss". su kai dariya gaba ɗayansu Ɗausiyya na faɗin,"Anty Samha ta mu ta bala'i". kafin nan Fillo ta wuce kiran da ake mata. a ɗaki ta sami Zaytuna tana waya, ta tsaya daga bakin ƙofa tana jiran ta kammala, Zaytuna tayi mata alama da hannu cewar ta shigo ciki ta zauna. ta bar ƙofar a buɗe ta shigo daga ciki ta zauna akan carpet. Turaki yazo shiga ɗakin ganin Fillo sai ya fasa, ya tsaya yana kallon duk su biyun, babu wanda ya gansa kamar yanda basu ji alamar zuwansa wurin ba. yasa hannu ya janyo ƙofar a hankali yanda ba za tayi ƙara ba sannan ya wuce, duk dan kar suga giftawarsa. sanda Zaytuna ta kammala wayar ta dubi Fillo tace,"me kike yi yanzu?". Fillo tace,"babu komai, mun gama aiki, ina karatu ne dama kamin na tafi". Zaytuna tace,"to kinga dama kayan wadrobe ɗin nan zaki gyara min, Hammah na min yankan farce ya yanke ni, na kasa taɓa komai". Fillo tace,"sannu Addah". tace,"yauwa, na gode...idan kika gama ki ɗauki wancan ƙaraman trolly ɗin ki tafi da ita". Fillo ta kalli trolly ɗin da take nuna mata, small size ce kamar waccan da ta bata, tace,"tom Adda, na gode Allah ya saka da alkhairi, Allah ya ƙarawa Baffa da Maama lafiya". Zaytuna tace,"amin...na dai faɗa miki tun ranar nan, duk wasu tsaffin kaya da kika san kina da su ki bayar". Fillo tace,"na bayar Adda, wanda muke iri ɗaya da Maijidda kawai na bari". Zaytuna tai shiru for few seconds kamin tace,"tom shikenan, goben kuzo ke da Maijiddan, ina son ganinta". ta amsa,"insha'Allah Addah". Zaytuna ta shiga toilet, ita kuma Fillo ta fara gyaran da ta sakata. lokacin da Zaytuna ta kammala shiryawa zata fita wayarta tayi ringing, ganin sunan Happiness a jiki tayi saurin picking tana faɗin,"Hammah nah". daga inda yake ya amsa da,"na'am Zaytun". sai kuma tai shiru tana jin cewarsa. ta waigo ta kalli inda Fillo take kafin ta amsa masa da cewa,"to Hammah". ta ƙara yin shiru na few seconds sannan ta ƙara cewa,"to Hammah, nima zan fita ne yanzu sai na dawo". da haka wayar tasu ta katse. tana sa wayar a jaka tace da Fillo,"idan kin gama kar ki tafi kinji, ki kunna system sai ki ƙarasa kallon da kike yi ran nan". wani daɗi ya mamaye Fillo, tana masifar son film ɗin, tun wancan ranar da ta kawowa Zaytuna assignmnt ta tarar bata nan sai Turaki ne a ɗakin, ta juya da sauri zata koma taji ya kirata yace ta dawo, ta shigo ɗakin ta zauna tayi tsilli-tsilli kamar ɓeran da aka girgiza acikin ruwan buta. tun zaman da tai a wurin gaba ɗaya sai ya manta da ita, kallonsa kawai yake acikin system. time to time sai yayi dariya ko kuma yay tsaki, Fillo dai na durƙushe a wurin kamar me neman gafara, kuma tun tana jin tsoro har tsoron ya barta, sai dai taita kallonsa ta wutsiyar ido, tana ƙara jin sabon haushinsa, idan taji yay dariya sai ta tambayi kanta dama yana dariya?. tafi ƙarfin minti goma sha biyar duƙe a wajen, tun tana a takure har ta saki jiki itama ta shiga kallon da yake yi a system ɗin, sai da aka kirasa a waya sannan ya tashi ya fita, ya fita ya barta da ci gaba da kallon, daɗin kallo ya mantar da ita yammar da tai, ta miƙe ƙafafu har sai da cajin laptop ɗin ya ƙare, lokacin ana sallar magriba. kuma sanda ta miƙe zata fita daga ɗakin sai ga shi ya dawo, ya kalleta ya kalla room ɗin, ta dabarbarce tana sarƙe yatsunta, ƙirjinta yana ta bugawa. daga sama taji muryarsa yana tambayarta,"ina Zaytun?". kanta a ƙasa tace,"bata dawo ba". sai yay mata kallon tsab yace,"ke kuma me kike yi anan?". ta ɗago kai tai masa duban mamaki tana saurin ɗauke ido daga cikin nasa da ya kafeta da su, bata bar jan yatsunta ba tace,"kaine ai ka tsayar da ni, kace nazo kuma aka kiraka ka tafi". yay shiru bai
🏠