NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 9 of 323

a guda biyu suna bayyana duka a waje. Taci gaba da scrolling har tazo kan wanda sukai gaba ɗayansu,"kai amma wannan ma yay kyau. 1 Family na Baffa kenan". Sanda tazo kan wanda Turaki yake shi kaɗai ta ƙara cewa,"wannan kam shima enlargement ɗinsa zan bada a ƙara min, Hammah yayi kyau sosai kamar wani magidanci". Sameer yace,"Maama wai duk sai kin cika bangon ɗakinki da parlonki da hoton Hammah ne?". "ƙila hakan ce zata kasance, dan sai dai idan bai yi sabon hoto shi ɗaya ba". Sai da suka zo ƙarshe a kallon hotunan sannan ta ƙara cewa,"gaskiya Hammah ya dawo ya fito min da matar aure, dan na ƙagu naga sirikata". Aiko nan dukansu suka haɗa baki wurin faɗin,"aiko dai Maama ya kamata ace Hammah yayi aure, sai tsofewa yake yi". Kallon da tai musu ne yasa babu shiri suka gimtse bakinsu, saboda kalmar tsufa da suka jinginata da Turaki. "Hajjah nyamdu mae henyi". (Hajiya abinci ya kammala). Mai aikin data ƙaraso wurin a yanzu ta faɗa sanda take tsugunawa a gefen hannun kujerar da Hajiya Madina ke zaune. Ba tare da ta juyo ta dubeta tace,"usema be habdugo". (sunnu da ƙoƙari) "aha Hajiya Miyetti". (yauwa Hajiya na gode) Daga haka ta miƙe ta bar wajen cikin azama dan barin musu wajen. Hajiya Madina ta ɗauke tab ɗin daga kan cinyarta tana ajeta kusa da ita, sannan ta kalla ƴaƴan nata tace da su,"my bloved ones dinner is ready". Tare suka miƙa kaf ɗinsu suka nufa dining area, warm coolers na abinci ne zafafa masu kuɗin gaske, an jere akan dining table ɗin wajen kala shida, kowanne cooler da kalan abinci dake ɗauke acikinta, ta yanda kowa idan zaici abincin zai ci favorite nasa ne. Zaytuna ta buɗe flask ɗin dake ɗauke da Mandi rice ta zuba a plate ta miƙa shi gaban Hajiya Madina, sannan kowa ya shiga zuba nasa abincin. Tunda suka fara ci babu babu wanda yay magana sai ƙarar cokula da kake ji har sanda suka kammala, wanda Hajiya Madina ce ta fara gamawa, ta yagi tissue ta goge bakinta. "albishirinku". Ta faɗa sanda take jefa tissue ɗin cikin durstbin. "goro Maama". Suka faɗa bakunansu a haɗe. "this time Baffa yayi suprising namu, mo don dow lawol vartugo". (yana kan hanyarsa ta dawowa). "na jam kam?". (amma dai Lafiya ko?) "jam saliiman, mo vii mo yenwi Muhammad mako tan". (Lafiya lau. Kawai yace yana kewar ganin Muhammad ɗinsa ne) "daɗin biyu kenan, to Baba ma yiidama to Dada ma kam yiidima". (Idan Babanka baya sonka to Mamarka na sonka). Muryar Khalil dake shigowa cikin parlon a yanzu ta amsa lokacin da shima yake jan kujerar dining zai zauna. Idon Hajiya Madina ya maƙale akansa tana cewa,"dume a tammi". (me kake nufi?) Khalil yay murmushi kamin yace,"banda nuna launiyar warin fata kawai Baffa sai ya dawo gida saboda mutum guda, hala mu dama ya manta ya haifemu?". Maganar yake cike da zolaya. Hajiya Madina tai murmushi kaɗan tace,"me yasa baka yi zuciya kazo a na farkon ba?". Shima yana murmushin yace,"to yanzu dai ba sai ya dawo ba ya tarar Hamman baya nan. Dole dai ni zai gani ai". "Jealosy". Ta faɗa tana binsa da wani kallo. A rayuwar Hajiya Madina babu abinda take so irin ta ganta cikin ƴaƴanta, kuma kowanne cikin farin ciki da jin daɗi ba acikin damuwa ba. Suna cikin tattaunawa akan batun gobarar data kama ɗazu wajen ɓangaren Lambun gidan, take basu labarin aima har an sallami me gadin wajen, saboda sakaki da yake akan aikinsa. Inda dukansu suka ce hakan yayi daidai, duba da ko lokacin da akazo wajen bama ya cikin gida gaba ɗaya, baima san da kamawar wutar ba, balle yasan abinda ya haddasa kamawarta. Wata matashiyar budurwa baƙa ta faɗo parlon cikin sauri me kama da sassarfa, kayan jikinta kawai zaka kalla ka shaidi itama ƴar aikin gidan ce. Wayar hannunta na ringing a karo na uku da kiran wayar ya ƙara shigowa. Ta ƙaraso gaban kujerar Hajiya Madina da sauri ta durƙusa tana miƙa mata bakinta na faɗin. "kiyi haƙuri Hajiya, na ɗan matsa ne har kira na farko ya shigo ya yanke". Hajiya Madina ta bita da wani irin kallo, ƙwayar idonta na haskawa da ƙyallin ɓacin rai, ta karɓi wayar tana karawa a kunnenta. Kana iya jiyo sautin maganar dake tashi ta ciki, sai dai baka iya jiyo abinda ake cewa, tsawon wucewar 120second ta miƙe daga kan kujerar da ta ke, Zaytuna taja mata kujerar baya sannan ta fito ta nufi ƙofa. Ba tai magana ba har sai data sanyo ƙafarta waje, kan step na farko da zai shigo da kai cikin parlon, sannan muryarta ta fito da wani irin amon sauti. "Suite Eo5, 6th Floor Plot 1010 1st Avenue, By Shehu Shagari Way, Central Business District, Abuja". Abunda ta faɗa kenan ta kashe wayar, kuma tana kan hanyar kaiwa ga ɓangaren Baffa sai jiyo horn tayi a baya, tana juyowa taga motarsa ce ke shigowa. Hakan yasa ta dawo da baya domin tarbar mijinta, inda wani farin ciki da annuri ya mamayeta. *Dare, 20:45pm.* "wai ha jonta a nyamae nyamdu mae na?". (wai har yanzu baki ci abincin bane?) "mihari Kaka". (na ƙoshi Kaka) "nde nyamuda dume?". (da kika ci me?) "Kaka nafa ƙoshi ne kaw
🏠