NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 89 of 323

ji kana ambatar sunana". murya a sanyaye Turaki yace,"abinda nake ganin ya dace nayi shi nayi Bello, sakayyar da ya kamata nayi kenan Bello, kai kanka ka sani komai da lissafi nake yinsa, bana abunda bai dace ba ka sani. and na san babu wanda zaiyi suppprting nawa shi yasa nayi komai ni ɗaya, even if its you na tabbata hakan zaka aikata...ba zaka gane komai ba sai na maka cikakken bayani Bello, wannan hargagin naka duk ba shi bane, ka fara ɗaukar maganar da nai maka da mutunci sannan sai nai maka bayani dalla-dalla". "bayanin banza Turaki, wane bayani zaka min dalla-dalla da zan fahimce ka?, wait! tunaninka ma kaina zai ɗauki maganar daka zo min da ita ne?, to ba ni kaɗai ba, babu me ɗaukar wannan zancen banzan naka, so tun wuri ma kwaɓar da kaje ka aikata kai ɗaya kaje ka warwareta kawai Malam". a fusace yayi maganar, shima kuma Turaki cikin fusata yace,"Bello Tukur Ƙaraye karka ƙara min ihu acikin mota, karka ƙara ɗaga min murya". shima Bello ya ƙara fusata yace,"Muhammad Turaki Habib ba zanyi ƙasa da muryata ba, kayi duk abinda kake ganin za kayi, ya za'ai ka aikata ba dai-dai ba kuma kace ba zanyi magana ba. tunda dama kasan ba zan goyi bayanka ba ai dole kaƙi yin shawara da ni kaje ka aikata abinda kake ganin ba zai zame maka matsala ba...ni har yanzu na kasa gane menene acikin kanka balle na fahimci kan zancen naka, anya baka sha wani abun ba?". Turaki yay masa banza, Bello ya dinga kallonsa da bala'in mamaki, ko a mafarki bai taɓa zaton Turaki zai iya aikata abinda ya faɗa ba balle kuma a zahiri. shi ya san waye Turaki, tun suna yara suke tare, ya san sarai abinda zai aikata da wanda ba zai aikata ba, and ya san ba zai taɓa aikata abu ba tare da ya nemi shawararsa ba ko kuma ya faɗa masa ba. Turaki baya gaban gansa sai da sanin mutum huɗu, dole Maama ce mutum ta farko da Turaki zai sanarwa abunda zai aikata, sannan shi ya biyo bayanta, sannan Baffa, sannan Zaytuna, dole mutum huɗun nan sai san abu kafin ya aiwatar da yinsa. amma this time around baya zaton cikin su huɗun akwai wanda yasan da wannan batun, sai a yanzu da shi ɗin ya sani, ya san abinda ba zai iya ƙaryatawa ba tunda yaga gaskiyar lamarin akan Fuskarsa da kuma furucinsa. wai har yana faɗa masa abunda ya dace shi nayi Bello?, tukunna ma! Bello ya sauke numfashi yace,"Maama ta sani?, ni ne daka mayar da ni banza yanzu kaje kai gaban kanka baka faɗa min ba?". har yanzu murayar Turaki da sanyi yace,"itama bata sani ba". Bello ya zaro ido,"what!". yace masa,"yes, bata san komai ba akai. kai ɗin ma na faɗa maka ne saboda na kasa riƙe abin ni kaɗai, ban san wane kalar asiri kayi min ba da bana iya riƙe sirrina sai na sanar maka". fuskarsa a tamke yayi maganar kamar yanda muryarsa ma take a tamke. Bello yay ƴar dariya yace,"Allah ka hauka ce ko kuma ka fara shaye-shaye, faɗa min waye ya baka gurguwan shawarar nan na fara shaye-shaye?". Turaki ya kallesa ta gefen ido yace,"Bello ni nake shaye-shaye?, ni kake cewa ina hauka? just saboda na fita hakkinka tunda na san bama ɓoyewa juna komai". Bello yace,"ai mahaukaci ma ba zai yi abinda kayi ba, sai me shaye-shayen dai, dan abinda ka aikata na ƴan ƙwaya ne, wanda yake cikin hankalinsa ba zai taɓa aikata haka ba wallahi...and imagine, ko kunya baka ji ba kake faɗa min wai Maama bata sani ba. so ko me zaka yi a haukace kake sai dai kaƙi yarda, kana buƙatar ganin likitan ƙwaƙwalwa dole". Turaki yay parking motarsa, without looking at Bello yace,"fitar min a mota". yace,"inje ina?". Turaki yace,"kaje inda masu hankali suke". Bello yay dariya sosai, dariyar dake ƙara ƙular da Turaki, ya dinƙa jin wani tuƙwiƙwi a zuciyarsa. Bello yace,"dan Allah dan Annabi ka juyo ka fuskance ni muyi maganar gaskiya, ka faɗa min cewa ƙarya kake yi, becouse the only Turaki i know ba zai yi wannan haukar ba". Turaki ya kallesa yana jin kamar ya bubbuge shi, wani takaicin Bello ya ƙara cunkushe masa a heart. yaja tsaki kawai ya fice daga motar, Bello na kallonsa ya tsayar da me napep ya hau suka bar wajen. ya tafi ya barsa da tunani kala-kala acikin ransa, abunda Turaki yayi sam ba na mutane ba ne. sai kuma yay shiru yana dogon nazari, to ma...sai kuma ya sauke numfashi, da ya sani ya basa damar yi masa bayani dalla-dalla, ƙila ya fahimce shi ɗin, amma duk da haka idan shi ya fahimta ta ya iyaye zasu fahimce shi?, da wanne idon ma zai jewa Hakimi?. fitowa yayi daga motar ya koma driver seat yaja motar, yana ta kiran wayar Turaki amma bai picking ba, kuma yasan yana sane, kuma ko da ace ya bisa gida yanzu ba zai taɓa sauraronsa ba, so gwara ma ya bari sai gobe sa haɗu, saboda haka kawai sai ya wuce gida da motar tasa. **** Fillo na zaune cikin inuwa a filin ƙofar ɗakinsu na ƴan aiki, littafi ne a gabanta da biro a hannunta. bitar karatunsu take yi dan gobe lesson teacher ɗin nasu zai yi musu exams. Ɗausiyya ta ƙaraso wajen itama, ta zauna akan tabarmar kusa da Fillo, ta leƙa abinda take karantawar sannan tace,"yauwa
🏠