NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 88 of 323

i ya bar office ɗin, ya tafi airport ɗauko Bello Ƙaraye wanda ya dawo daga sudan yaje wani course. akan tinin barin Gombe international airport, cikin motar ƙirar Bugatti, motar da Mai Martaba ya bawa Turaki ita a ranar buɗe company ɗinsu, Bello ya kai hannu yay reducing volume na karatun qur'anin da suke saurare tun barowansu airport, can kuma sai ya kashe gaba ɗaya. yace,"Kana ciwon baki ne?". Turaki yayi masa shiru bai tanka masa ba, idonsa na manne akan titi. Bello yay tsaki,"duk inda ɗan rainin hankali yake daga kanka an rufe ƙofa. banda iskanci tun tahowarmu nake magana but you refuse to answer me, kuma tsabar miskilancinka ya kai intaha ina kallon bakinka yana motsi amma ba zaka faɗi abinda ke cikinka ba...i don't know what is exactly wrong with you, i saw some changes in you tun before na tafi, to ni ba ɗan iska bane da zan ta tambayarka kana min banza". Turaki yace,"ka bani damar magana ne balle na faɗa maka abinda ke cikin nawa?, tun fa da na ɗaukoka ka isheni da Bima Restaurant, sai kace baka taɓa cin abinci ba a duniyarka. tun saukar ka you din't ask about my health, abinci abinci kawai shi ka sani, kai idan kana jin yunwa you see nothing balle ma ka lura da ramewar da mutum yay". yanda yay maganar a ƙufule Bello Ƙaraye ya bushe da dariyar ƙeta, shi dai tunda ya fito a jirgi ya kalla kamar idanun Turaki sun faɗa loko, to amma bai lura da muguwar ramewar da yay ba sai yanzu, yanwa yake ji sosai shi yasa idonsa ya rufe da ganin komai. yace,"to ka bani damar ganin ramar da kayi ne balle nace Muhammad Turaki baka da lafiya ne?, tunda fa da ka ɗaukoni fuskarka take a ɗaure, sannu wannan bata haɗani da kai ba, to ta ina zanga wata rama?, motsin bakinka kawai na lura da shi...anyway what is wrong with you?, did you go to the hospital?". Turaki yay masa wani kallo yace,"ciwon uban me nace maka ina yi da zanje asibiti?, ni lafiyata ƙalau". Bello yace,"ikon Allah, to naji lafiyarka lau. what is the problem?". Turaki yay masa shiru yana kallon titin gabansa, cikin ransa yana tunanin ta inda zai fara yi masa maganar, sarai ya san rainin hankalin Bello, yanzu sai ya faɗa masa kuma ya ɗauki maganar a gantale. ba zai nutsu ya fahimci naganar ba balle ya basa damar fayyace masa komai. Bello dai na gefe yana kallonsa, ganin baida niyyar cewa komai ya ɗaga kafaɗa ya maida hankalinsa kan wayarsa, ko mene idan tayi tsami zaiji, ba zai iya da wannan miskilancin ba, yunwar dake rarakar cikinsa ma ta ishe shi. shirunsu ya ratsa cikin motar, sai can Turaki yace,"just give me your full attention let's talk". yay maganar a hankali. Bello ya kallesa yaga Seriousness ɗin dake kan fuskarsa, sai ya kifa wayarsa a kan cinyarsa yace,"na baka duka attention ɗina, idan ma so kake na cirosa na miƙo maka gaba ɗaya sai nayi hakan". Turaki ya waigo yay masa kallo ɗaya ya ɗauke kai, ya dinga motsa bakinsa kamar bebe, shi yasan hali na rainin hankalin Bello shi yasa yake ta shakkar faɗa masa, he never take things seriously a lokacin da ya kamata. Bello ya katse tunaninsa,"mu tafi Restaurant ɗin kawai, ba zan iya isa gida banci komai ba". sai a sannan Turaki ya buɗe baki yayi maganar da tasa Bello ya zabura, har yana ƙoƙarin miƙewa akan kujera. da wani mugun shock Bello ke kallonsa yana ganin kamar ba Turakin da ya sani ba ne, wannan wani Turaki ne na daban da zai iya aikata abunda yake faɗa, amma nasa Turakin ko da ace giyar wake yasha ba zai iya aikata abinda wannan ya faɗa ba. "what! kace mene?, na kasa fahimtar me kake son cewa". Bello ya tambaya har sannan idanuwansa a waje. Turaki yace,"abunda kaji na faɗa". Bello Ƙaraye ya cire hular kansa yana goge wani uban gumi da ya fara keto masa, ya koma kamar wanda yaywa sarki ƙarya. "wait Turaki! wait!, abar zancen wasa dan wannan maganan naka ba magana bane da za'a ɗauka matsayin wasa...". bai ƙarasa abinda zai ce ba Turaki ya katse shi,"ni dama na taɓa faɗi maka abu a wasa ne? balle ka ɗau maganar nawa a shashance". Bello yace,"to idan ba wasa kake ba Hauka ka yi?, dan maganar da kayi bata masu hankali bace kuma ba magana bace da hankalina zai ɗauka...kasan kuwa me ka faɗa?, Turaki are you in your sense? yaushe lissafinka ya fara kwancewa?". danger ta tsayar da motarsu, fuskar Turaki a ɗaure ya juyo ya kalli Bello yace,"kaga Malam, ban faɗa maka personal issue na ba dan ka dinga min ihu aka ba, idan ka gane fine, idan ba gane ba just keep quite". Bello yace,"ba zanyi shirun ba". yay ɗan jim yana maimaita furucin Turankin acikin kansa, anya kuwa bai sha wani abu ba kafin ya ɗauko sa?. ya ɗaga kai ya ƙara kallon Turakin da tsananin mamakin da yaƙi barinsa, da ƙyar ya iya buɗe baki yace masa,"da sanin wa kuma da izinin wa akai hakan Muhammad?". Turaki yace,"da sanin kaina da izinin kaina ni ɗaya, sai kuma me?, sai akayi ya ya?". da wani mugun jin haushinsa Bello yace,"sai ka yi ba dai-dai ba, kuma tun wuri kaje ka warware kwaɓar da ka aikata kai ɗaya, karma akai gaba na
🏠