NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 87 of 323

okacin?, a yanzu kamin wani yazo?, sai taji cikin kanta kamar babu komai, dukkan wata dabara tata ta yanke mata, bata san me zata yi ba. acikin wani yanayin dake da wuyar fassaruwa tasa tafin hannunta me taushi ta shafa fuskarsa, sannan ta duƙo da kanta saitin kunnensa muryarta da rauni tace masa,"baka da lafiya? sannu, ka daina hawayen, bari naje na kirawo Maama". ta faɗi hakan tana ƙoƙarin miƙewa, ta yunƙura zata miƙe sai taji ya ruƙo hannunta ya dawo da ita. ƙwayar idonta ta faɗa cikin nasa a sanda hawayen ciki suka sami nasarar gangarowa kan kumatunta. a sanyaye tace,"zanje na kira maka Maama ne". sai taga ya girgiza kansa a hankali cikin ƙarfin hali. ta sake cewa,"to kana da magani a kusa na ɗauko maka?, aina zan ɗauko?". nan ma kansa ya girgiza mata a hankali. cikin dauriyar abinda yake ji acikin zuciyarsa. sai ta samu kanta da ce masa,"to me zanyi maka? me kake so?". sai taji ya ƙara damƙe hannunta sosai, ya sauke kallonsa daga kanta ya tsayar ajikin bangon dake facing nasu. ta tsaya kawai tana kallon gefen fuskarsa, tana jin yanda ruwan hawayensa ke ɗiga a saman skirt ɗin jikinta, tana jin yana ɗauke kansa daga ƙasa yana ɗorawa a saman cinyarta, tana ji yana ƙara damƙe hannunta, tana jin yanda wani abu ke fita daga tafin hannunsa yana shiga cikin nata, tana jin wannan zafin da ta tabbatar yana ji a zuciyarsa yana taɓa tata zuciyar. ta rumtse ido for few seconds sannan ta buɗe, ta buɗe tana bin inda yake kallo har sanda ta sauke kallonta gaba ɗaya akan ƙaton enlargement ɗin dake manne a bango. tayi mugun zabura da hoton da ta gani, ta tsayar da ƙwayar idanuwanta cak akan hoton tana ƙarewa dattijuwar matar dake jikin hoton kallo, ba sai an faɗa ba matar balarabiya ce, kallon matar take tana hango tsananin kamanni na Turaki dana Zaytuna a tare da ita, tun daga murmushinta har dimple ɗinta daya lotsa ciki sosai babu abinda ya banbanta daga na Turaki dana Zaytuna. _but who is she?_, tambayar da taiwa kanta kenan, kuma kafin zuciyarta ta raya mata wata amsa sai ganin Turaki tai ya miƙe tsaye yana toshe duka kunnuwansa biyu yana doka goshinsa a jikin glass da ƙarfi. tayi azamar miƙewa tana ruƙo shi tana faɗin,"ka daina, zaka ji ma kanka ciwo". ta faɗa cikin tashin hankalin da ta rasa na menene, kuma rufe bakinta kenan jinin dake fita a goshinsa ya zuba akan ƙirjinta. ta kalla jinin dake ƙirjinta, ta kalla jinin dake fitowa a goshinsa, idonta a waje tace,"ka bari". ta faɗa da wani mugun ƙarfi tana sa hannu da iya ɗan ƙarfin da take da shi ta fizgo shi daga bakin glass ɗin da yake tsaye, sai gasa a gabanta, taja hannunsa ta zauna da shi a ƙasa tana kunce ɗankwalinta ta ɗaure masa goshin. "menene? ka daina kukan to dan Allah, ka faɗa min me kake so?, me zanyi maka?, ka jira anan karka ƙara tashi zanje na kira Maama". ta faɗa kukan dake bakinta na fitowa. kuma sanda ta yunƙura zata miƙe lokacin ya janyota jikinsa ya rungume tsam yana kama hannunta ya toshe kunnensa da su. muryarsa na fitowa cikin muryar namiji mai rauni da faɗin,"don Allahhhhh, ki taimaka min". _Ayi Haƙuri dan Allah, mun shiga rububin biki, from this week har next week, babu zama kullum tafe ake, idan an zauna kuma hayaniyar ƴan taro ta hanaka sakat balle ka sami natsuwar typing, kuma kun san jiki da jini, mutum naso ya huta idan yay struggling. dalilin da yasa kuka jini ɗiff kenan, kuci gaba da haƙuri tare da min uzuri._ *Comment naku shi ne ƙwarin gwiwata.* *LULLUƁIN BIRI* *©️Halima h.z* *22* After 4months, cikin ƙaton office ɗin da sanyin Ac ke ta busawa yana haɗewa da daddaɗan ƙamshin turaren dake jikinsa yana bada wani irin sanyayyan ƙamshi me motsa zuciya. Turaki ne zaune akan kujera dake ɗan juyawa da shi gefe zuwa gefe, one of his fingers on his lips, cikin yanayi na nazari akan wani lissafi nasa. numfashi ya sauke sannan ya shiga operating laptop ɗin dake kan table a gabansa, ya ɗau lokaci kafin ya ɗauƙi wayarsa a gefe yay calling numbern Khalil. in the next 3minutes sai ga Khalil ya shigo office ɗin, tun shigowansa Turaki ke kallonsa har sanda ya ƙaraso ya zauna kan kujera. "Director". Turaki ya faɗi sunan da yake kiran Khalil da shi a yanzu tun bayan mallakar wannan company ɗin da sukai. Khalil ɗin shima yana kallonsa ya amsa da nasa sunan da yake kiransa da shi na yanzu. "yes Manager". anan ne kuma Turaki ya ɓullo da wata magana wadda ta shafi aikin company ɗin nasu, sun ɗau tsawon lokaci suna tattaunawa akan issue ɗin, Khalil nata ƙara kawo dabaru da zasu daɗa ɗaga company ɗin nasu zuwa sama, dan sam basa saka kamfanin nasu a matsayin ƙarami saboda yana sabon buɗewa, so suke cikin ƙaramin lokaci ya kai wani babban mataki da ba kowanne company ke samu ba at once. a lokacin Turaki ya haɗa urgent meeting da staffs nasu, aka shiga aka ƙara tattaunawa kowa na bada POV nasa akan ganin kamfanin ya haɓɓaka. sai da suka ɗauki tsawon awa guda sannan suka gama. suna kammalawa kuma Turak
🏠