NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 86 of 323

"na'am Zaytun". sai kuma tai shiru tana jin cewarsa. ta waigo ta kalli inda Fillo take kafin ta amsa masa da cewa,"to Hammah". ta ƙara yin shiru na few seconds sannan ta ƙara cewa,"to Hammah, nima zan fita ne yanzu sai na dawo". da haka wayar tasu ta katse. tana sa wayar a jaka tace da Fillo,"idan kin gama kar ki tafi kinji, ki kunna system sai ki ƙarasa kallon da kike yi ran nan". wani daɗi ya mamaye Fillo, tana masifar son film ɗin, tun wancan ranar da ta kawowa Zaytuna assignmnt ta tarar bata nan sai Turaki ne a ɗakin, ta juya da sauri zata koma taji ya kirata yace ta dawo, ta shigo ɗakin ta zauna tayi tsilli-tsilli kamar ɓeran da aka girgiza acikin ruwan buta. tun zaman da tai a wurin gaba ɗaya sai ya manta da ita, kallonsa kawai yake acikin system. time to time sai yayi dariya ko kuma yay tsaki, Fillo dai na durƙushe a wurin kamar me neman gafara, kuma tun tana jin tsoro har tsoron ya barta, sai dai taita kallonsa ta wutsiyar ido, tana ƙara jin sabon haushinsa, idan taji yay dariya sai ta tambayi kanta dama yana dariya?. tafi ƙarfin minti goma sha biyar duƙe a wajen, tun tana a takure har ta saki jiki itama ta shiga kallon da yake yi a system ɗin, sai da aka kirasa a waya sannan ya tashi ya fita, ya fita ya barta da ci gaba da kallon, daɗin kallo ya mantar da ita yammar da tai, ta miƙe ƙafafu har sai da cajin laptop ɗin ya ƙare, lokacin ana sallar magriba. kuma sanda ta miƙe zata fita daga ɗakin sai ga shi ya dawo, ya kalleta ya kalla room ɗin, ta dabarbarce tana sarƙe yatsunta, ƙirjinta yana ta bugawa. daga sama taji muryarsa yana tambayarta,"ina Zaytun?". kanta a ƙasa tace,"bata dawo ba". sai yay mata kallon tsab yace,"ke kuma me kike yi anan?". ta ɗago kai tai masa duban mamaki tana saurin ɗauke ido daga cikin nasa da ya kafeta da su, bata bar jan yatsunta ba tace,"kaine ai ka tsayar da ni, kace nazo kuma aka kiraka ka tafi". yay shiru bai ce komai ba, ya juya zai tafi muryata na ɗan rawa cike da tsoro tace,"na tafi?". yace,"a'a kiyi ta zama". daga haka ya wuce ya barta a wurin. ta bar ɗakin da kewar film ɗin da bata ƙarasa gani ba, kuma da ta koma ranar raba dare suka yi tana bawa Maijidda labarin film ɗin, bata ma san ya akai Zaytuna tasan ta kalli film ɗin ba. kanta a ƙasa tana wasa da yatsunta tace da Zaytuna,"Adda ban iya kunna laptop ɗin ba". Zaytuna tace,"kina buɗewa zata kama, Turaki is the password". tace,"tom". sai ta ƙara ce mata,"zaki iya ɗin ko na kunna miki?". tace,"zan iya Adda, Adda Nihal ta taɓa gwada min". Zaytuna tayi murmushi tace,"ranar da kika sa ta dinƙa mana mitar ƙauyancin da kika mata?". kunya tasa Fillo rufe fuska. bayan fitar Zaytuna babu jimawa ta kammala gyaran wadrobe ɗin, ta ɗauki ƙaramar trolly ɗin ta buɗe taga sabbin kaya ne kamar wancan time ɗin da ta bata. abaya guda huɗu sai riga da skirt na material guda biyu da na atamfa guda ɗaya. duka kayan kamar sai da akayi measurement ɗinta, dan babu alamar ma kayan ragesu akayi. cike da farin ciki ta mayar ta zuge zip ɗin, wannan ma rabawa zasu yi ita da Maijidda kamar yanda suka raba wancan. maimakon taja trolly ɗin sai ta ɗauka ta ɗora akanta, ta fito ta rufe ɗakin farin ciki duk yaƙi barinta. zata sauka a stairs sai taji kamar mutum na sauke wahaltaccen numfashi a cikin ɗakin da yake gaba dana Zaytuna. sai taji ta kasa tafiya, ta tsinci kanta da komawa da baya har ta iso ƙofar ɗakin, ta tsaya tana ƙara tabbatar da abunda kunnuwanta ke jiyowa. bata manta da wani lokaci ba da suka zo gyara ita da Ɗausiyya, Nihal ta ke ce musu su gyara kowanne room dake upstairs banda wannan da yake da coffee door, shi ba'a buɗe shi totally. for sure daga room ɗin take jiyo sautin, to anya kuwa daidai ta ke ji acikin kunnuwanta?, ai ranar har suka gama zaryarsu anan basu ji wani abu makamancin haka ba, ta tsaya tana Contemplating ta buɗe ko ta tafi, abunda kunnenta ke jiyowa dai ba na wasa ba ne, ba irin abunda mutum zaiji bane ya ƙyale ya tafi. sai kawai zuciyarta ta tsaya akan ta buɗe ɗin, ta sauke trolly daga kanta. tasa hannu ta murɗa handle na ƙofar room ɗin, door ɗin ya buɗe yana bada wani sautin ƙara. tsabar mamaki da tsorata Fillo sai taji kamar ƙafafunta ba zasu ƙara ɗagawa ba, tabi wurin da Turaki yake a yashe a ƙasan tiles dafe da ƙirjinsa, numfashinsa na fita da ƙyar. ruwan hawaye na sauka ta gefen idonsa, kawai sai taji kanta yayi wani irin nauyi, hawayen nasa ya ɗimautata, kamar wannan ace yana hawaye?, me ke damunsa?. bata san lokacin da ƙafafunta suka kaita gabansa ba gwiwoyinta suka durƙushe a saitin da kansa yake, ta kallesa taga kamar ma a sume yake, gabanta ya faɗi saboda yacca idonsa ya tsaya a wuri ɗaya cak baya ko motsi. ta kai hannu ƙasan hancinsa taji yana numfashi, sannan ta sauke wata nauyyar ajiyar zuciya. tausayinsa yay bala'in kamata, taya zata iya barinsa taje ta sanar da halin da yake ciki?, idan ta tafi me zai iya faruwa before ta dawo?, me zata yi don taimaka masa a wannan l
🏠