NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 85 of 323

llo yace,"ai mahaukaci ma ba zai yi abinda kayi ba, sai me shaye-shayen dai, dan abinda ka aikata na ƴan ƙwaya ne, wanda yake cikin hankalinsa ba zai taɓa aikata haka ba wallahi...and imagine, ko kunya baka ji ba kake faɗa min wai Maama bata sani ba. so ko me zaka yi a haukace kake sai dai kaƙi yarda, kana buƙatar ganin likitan ƙwaƙwalwa dole". Turaki yay parking motarsa, without looking at Bello yace,"fitar min a mota". yace,"inje ina?". Turaki yace,"kaje inda masu hankali suke". Bello yay dariya sosai, dariyar dake ƙara ƙular da Turaki, ya dinƙa jin wani tuƙwiƙwi a zuciyarsa. Bello yace,"dan Allah dan Annabi ka juyo ka fuskance ni muyi maganar gaskiya, ka faɗa min cewa ƙarya kake yi, becouse the only Turaki i know ba zai yi wannan haukar ba". Turaki ya kallesa yana jin kamar ya bubbuge shi, wani takaicin Bello ya ƙara cunkushe masa a heart. yaja tsaki kawai ya fice daga motar, Bello na kallonsa ya tsayar da me napep ya hau suka bar wajen. ya tafi ya barsa da tunani kala-kala acikin ransa, abunda Turaki yayi sam ba na mutane ba ne. sai kuma yay shiru yana dogon nazari, to ma...sai kuma ya sauke numfashi, da ya sani ya basa damar yi masa bayani dalla-dalla, ƙila ya fahimce shi ɗin, amma duk da haka idan shi ya fahimta ta ya iyaye zasu fahimce shi?, da wanne idon ma zai jewa Hakimi?. fitowa yayi daga motar ya koma driver seat yaja motar, yana ta kiran wayar Turaki amma bai picking ba, kuma yasan yana sane, kuma ko da ace ya bisa gida yanzu ba zai taɓa sauraronsa ba, so gwara ma ya bari sai gobe sa haɗu, saboda haka kawai sai ya wuce gida da motar tasa. **** Fillo na zaune cikin inuwa a filin ƙofar ɗakinsu na ƴan aiki, littafi ne a gabanta da biro a hannunta. bitar karatunsu take yi dan gobe lesson teacher ɗin nasu zai yi musu exams. Ɗausiyya ta ƙaraso wajen itama, ta zauna akan tabarmar kusa da Fillo, ta leƙa abinda take karantawar sannan tace,"yauwa du Allah ki ƙara min bayanin wannan, ni ɗazu duk ban gane ba, ya saka turanci da yawa a maganar tasa". Fillo ta aje littafin, ta falli takarda ta shiga yiwa Ɗausiyya bayani turyan turyan kamar itace teacher ɗin. suna cikin yin karatun ne suka ji wayar ɗakinsu na ringing, Ɗausiyya ta miƙe tana ƙorafin ba za'a barsu su dinƙa hutawa ba, yanzu sai ace suzo suyi aiki yen yen yen. Fillo ta bita da kallo tana faɗin,"ke kuma da samun wuri, dama me kika zo yi idan ba aikin ba". Ɗausiyya ta ɗaga wayar, daga ɓangaren Zaytuna tace da ita,"ina Fillo?". tace,"tana waje tana karatu". tace mata,"kice tazo ta sameni". "tom Anty". ta faɗa tana ajiye wayar ta fito daga ɗakin. inda suke ta koma ta zauna ta ɗauki nata littafin tana sanarwa da Fillo saƙon. Fillo tace,"wacce Antyn?". tace mata,"Anty Zaytuna mana". Fillo ta miƙe tana faɗin,"au nai zaton Anty me dogon baki ce, wallah har gabana ya faɗi". Ɗausiyya tayi dariya tace,"idan itace ai ba zaki ga na dawo yanzu ba, da tuni tana nan tana surfa min zagi ni da iyayena kafin tace min kiranki take". Fillo ma tai dariya tace,"ba kya nan ai ɗazu aka ce mana shegu masu warin baki". Ɗausiyya tace,"sai kika mata shiru baki yi mata rashin kunya ba?". Fillo ta harareta tace,"ai tunda na faɗa miki sai kije ki mata tunda you are the boss". su kai dariya gaba ɗayansu Ɗausiyya na faɗin,"Anty Samha ta mu ta bala'i". kafin nan Fillo ta wuce kiran da ake mata. a ɗaki ta sami Zaytuna tana waya, ta tsaya daga bakin ƙofa tana jiran ta kammala, Zaytuna tayi mata alama da hannu cewar ta shigo ciki ta zauna. ta bar ƙofar a buɗe ta shigo daga ciki ta zauna akan carpet. Turaki yazo shiga ɗakin ganin Fillo sai ya fasa, ya tsaya yana kallon duk su biyun, babu wanda ya gansa kamar yanda basu ji alamar zuwansa wurin ba. yasa hannu ya janyo ƙofar a hankali yanda ba za tayi ƙara ba sannan ya wuce, duk dan kar suga giftawarsa. sanda Zaytuna ta kammala wayar ta dubi Fillo tace,"me kike yi yanzu?". Fillo tace,"babu komai, mun gama aiki, ina karatu ne dama kamin na tafi". Zaytuna tace,"to kinga dama kayan wadrobe ɗin nan zaki gyara min, Hammah na min yankan farce ya yanke ni, na kasa taɓa komai". Fillo tace,"sannu Addah". tace,"yauwa, na gode...idan kika gama ki ɗauki wancan ƙaraman trolly ɗin ki tafi da ita". Fillo ta kalli trolly ɗin da take nuna mata, small size ce kamar waccan da ta bata, tace,"tom Adda, na gode Allah ya saka da alkhairi, Allah ya ƙarawa Baffa da Maama lafiya". Zaytuna tace,"amin...na dai faɗa miki tun ranar nan, duk wasu tsaffin kaya da kika san kina da su ki bayar". Fillo tace,"na bayar Adda, wanda muke iri ɗaya da Maijidda kawai na bari". Zaytuna tai shiru for few seconds kamin tace,"tom shikenan, goben kuzo ke da Maijiddan, ina son ganinta". ta amsa,"insha'Allah Addah". Zaytuna ta shiga toilet, ita kuma Fillo ta fara gyaran da ta sakata. lokacin da Zaytuna ta kammala shiryawa zata fita wayarta tayi ringing, ganin sunan Happiness a jiki tayi saurin picking tana faɗin,"Hammah nah". daga inda yake ya amsa da,
🏠