Restaurant ɗin kawai, ba zan iya isa gida banci komai ba". sai a sannan Turaki ya buɗe baki yayi maganar da tasa Bello ya zabura, har yana ƙoƙarin miƙewa akan kujera.
da wani mugun shock Bello ke kallonsa yana ganin kamar ba Turakin da ya sani ba ne, wannan wani Turaki ne na daban da zai iya aikata abunda yake faɗa, amma nasa Turakin ko da ace giyar wake yasha ba zai iya aikata abinda wannan ya faɗa ba.
"what! kace mene?, na kasa fahimtar me kake son cewa". Bello ya tambaya har sannan idanuwansa a waje.
Turaki yace,"abunda kaji na faɗa". Bello Ƙaraye ya cire hular kansa yana goge wani uban gumi da ya fara keto masa, ya koma kamar wanda yaywa sarki ƙarya.
"wait Turaki! wait!, abar zancen wasa dan wannan maganan naka ba magana bane da za'a ɗauka matsayin wasa...".
bai ƙarasa abinda zai ce ba Turaki ya katse shi,"ni dama na taɓa faɗi maka abu a wasa ne? balle ka ɗau maganar nawa a shashance".
Bello yace,"to idan ba wasa kake ba Hauka ka yi?, dan maganar da kayi bata masu hankali bace kuma ba magana bace da hankalina zai ɗauka...kasan kuwa me ka faɗa?, Turaki are you in your sense? yaushe lissafinka ya fara kwancewa?".
danger ta tsayar da motarsu, fuskar Turaki a ɗaure ya juyo ya kalli Bello yace,"kaga Malam, ban faɗa maka personal issue na ba dan ka dinga min ihu aka ba, idan ka gane fine, idan ba gane ba just keep quite".
Bello yace,"ba zanyi shirun ba". yay ɗan jim yana maimaita furucin Turankin acikin kansa, anya kuwa bai sha wani abu ba kafin ya ɗauko sa?. ya ɗaga kai ya ƙara kallon Turakin da tsananin mamakin da yaƙi barinsa, da ƙyar ya iya buɗe baki yace masa,"da sanin wa kuma da izinin wa akai hakan Muhammad?".
Turaki yace,"da sanin kaina da izinin kaina ni ɗaya, sai kuma me?, sai akayi ya ya?".
da wani mugun jin haushinsa Bello yace,"sai ka yi ba dai-dai ba, kuma tun wuri kaje ka warware kwaɓar da ka aikata kai ɗaya, karma akai gaba naji kana ambatar sunana".
murya a sanyaye Turaki yace,"abinda nake ganin ya dace nayi shi nayi Bello, sakayyar da ya kamata nayi kenan Bello, kai kanka ka sani komai da lissafi nake yinsa, bana abunda bai dace ba ka sani. and na san babu wanda zaiyi suppprting nawa shi yasa nayi komai ni ɗaya, even if its you na tabbata hakan zaka aikata...ba zaka gane komai ba sai na maka cikakken bayani Bello, wannan hargagin naka duk ba shi bane, ka fara ɗaukar maganar da nai maka da mutunci sannan sai nai maka bayani dalla-dalla".
"bayanin banza Turaki, wane bayani zaka min dalla-dalla da zan fahimce ka?, wait! tunaninka ma kaina zai ɗauki maganar daka zo min da ita ne?, to ba ni kaɗai ba, babu me ɗaukar wannan zancen banzan naka, so tun wuri ma kwaɓar da kaje ka aikata kai ɗaya kaje ka warwareta kawai Malam".
a fusace yayi maganar, shima kuma Turaki cikin fusata yace,"Bello Tukur Ƙaraye karka ƙara min ihu acikin mota, karka ƙara ɗaga min murya".
shima Bello ya ƙara fusata yace,"Muhammad Turaki Habib ba zanyi ƙasa da muryata ba, kayi duk abinda kake ganin za kayi, ya za'ai ka aikata ba dai-dai ba kuma kace ba zanyi magana ba. tunda dama kasan ba zan goyi bayanka ba ai dole kaƙi yin shawara da ni kaje ka aikata abinda kake ganin ba zai zame maka matsala ba...ni har yanzu na kasa gane menene acikin kanka balle na fahimci kan zancen naka, anya baka sha wani abun ba?".
Turaki yay masa banza, Bello ya dinga kallonsa da bala'in mamaki, ko a mafarki bai taɓa zaton Turaki zai iya aikata abinda ya faɗa ba balle kuma a zahiri.
shi ya san waye Turaki, tun suna yara suke tare, ya san sarai abinda zai aikata da wanda ba zai aikata ba, and ya san ba zai taɓa aikata abu ba tare da ya nemi shawararsa ba ko kuma ya faɗa masa ba. Turaki baya gaban gansa sai da sanin mutum huɗu, dole Maama ce mutum ta farko da Turaki zai sanarwa abunda zai aikata, sannan shi ya biyo bayanta, sannan Baffa, sannan Zaytuna, dole mutum huɗun nan sai san abu kafin ya aiwatar da yinsa. amma this time around baya zaton cikin su huɗun akwai wanda yasan da wannan batun, sai a yanzu da shi ɗin ya sani, ya san abinda ba zai iya ƙaryatawa ba tunda yaga gaskiyar lamarin akan Fuskarsa da kuma furucinsa. wai har yana faɗa masa abunda ya dace shi nayi Bello?, tukunna ma!
Bello ya sauke numfashi yace,"Maama ta sani?, ni ne daka mayar da ni banza yanzu kaje kai gaban kanka baka faɗa min ba?".
har yanzu murayar Turaki da sanyi yace,"itama bata sani ba". Bello ya zaro ido,"what!". yace masa,"yes, bata san komai ba akai. kai ɗin ma na faɗa maka ne saboda na kasa riƙe abin ni kaɗai, ban san wane kalar asiri kayi min ba da bana iya riƙe sirrina sai na sanar maka". fuskarsa a tamke yayi maganar kamar yanda muryarsa ma take a tamke.
Bello yay ƴar dariya yace,"Allah ka hauka ce ko kuma ka fara shaye-shaye, faɗa min waye ya baka gurguwan shawarar nan na fara shaye-shaye?".
Turaki ya kallesa ta gefen ido yace,"Bello ni nake shaye-shaye?, ni kake cewa ina hauka? just saboda na fita hakkinka tunda na san bama ɓoyewa juna komai".
Be