un kammala ba". "haka ne dama komai ai lokaci ne, yanzu ai ba tausa zaki ba Ilham jikina zaki taho".
Ilham ta bar matsa ƙafar da ta fara tayi jikinta suka rungume juna. duk su biyun suna masu jin daɗi. Ilham ƴar gidan Hashim ce mai martaba na yanzu ɗan Boɗejo, itace ƴarsa mace ta biyu wacce taci sunan Boɗejo Rumana, ta tafi america karatu inda ta karanci business administration, kuma tunda ta tafi bata dawo ba sai yanzu, shekara biyar cif.
ba don babu halin dawowar ba sai dan kawai mahaifinta yafi so ta nutsu tai karatunta, ya kanje ya dubata akai-akai shi da mahaifiyarta wacce itace mata ta biyu a wurinsa. Boɗejo ko da yaushe acikin mitar karatun Ilham ɗin takeyi duk sanda taje wajen me martaban, har ta kance ko dai dan yaga an saka mata sunanta ne shiyasa baya ƙaunarta, da ƙyar yake samu ya lallasheta, idan yace ta shirya akaita taje ta ganota sai tace ita ba zata je ƙasar arna ba, dama saudiya ne to anan tafi kauri amma ita kam ba dai ta hau jirgi taje ƙasar arna ta kwasowa kanta zunubi ba.
Aisha na gefe tana kallonsu da burgewa, ita bata taso ta sami kakanninta ko ɗaya ba duk sun mutu. shi yasa idan taga tsofaffi sai taji suna burgeta, dalilin da ya sa ta biyo Ilham kenan suka taho tare, amma yau tayi niyyar komawa kano saboda kar mahaifinta me martaba sarkin kano ya dawo bata nan, yana dira wanda zai so ya fara ganawa da shi itace, kasancewarta auta.
Hajiya Atika matar Hakimi ta shigo ɗakin, itama tai mamakin ganin Ihlam tace,"yaushe kika dawo?".
tace,"jiya da yamma, tun jiyan ma naso nazo naga Boɗejo Mami tace na bari dai zuwa yau".
Hajiya Atika na murmushi tace,"lallai ne to sannun da zuwa, fatan an kammala karatu lafiya?". tace,"lafiya lau Hajiya, ai banma taho ba sai dana jira result ya fita. jiya ina dawowa Me Martaba yay min kyautar wannan gidajen guda biyu na estate ɗinsa".
Hajiya Atika tace,"masha'Allahu, Allah yasa a amfana da karatun da akai, ita kuma ƙawar taki fa?".
Ilham ta kalli Aisha sannan tace,"ai ba tare mukai karatun ba, tazo min sannu da zuwa ne, itama ta kusa kammalawa tana karantar AEE ne a Germany".
Aisha ta gaida Hajiya da Boɗejo, suka amsa suna sanya musu albarka. Ilham tace,"Hajiya ita ɗin fa ƴar sarkin kano ce".
Boɗejo tace,"ni fa ince, shiyasa da ta shigo taƙi gaisheni ta hakimce mana akan kujera, ashe izzar masu sarautan ce, to ni nan da kike gani na haka kamar ba kowa ba to sarauniya ce ada, kuma ni na haifi Baban wannan yarinyar, kinga na zama matar sarki uwar sarki, nan gaba kaɗan ma zan zama Kakar Sarki, dan sai an sami wani jikan nawa ya hau kujerar sarautar nan, dan haka ki sadda kanki ƙasa ki min biyayya ki kwashi albarka, ko me gidan nan Hakimi da kike ganinsa ɗana ne shine na fari, kinga kuwa indai girman izzar sarauta ne aini ke da ita bake ba yarinya".
dukansu suka yi dariya. sai yanzu Hajiya Atika ta samu damar isar da saƙon Hakimi.
"dama Hakimi ne yace na faɗa miki ko kema zaki je wajen taron nan na buɗe company ɗin su Turaki".
Boɗejo tace,"shi Turakin ne zai buɗe kamfani ko kuma ɗana Dikko ya buɗe masa?".
Hajiya Atika tace,"ehhh Alƙalin ne ya gina ya kuma mallaka masa shi da Khalil, kamfanin haɗa lemuka ne".
Boɗejo tace,"ni dai ince, amma ina Turaki yaga kuɗin buɗe wani kamfani ai sai dai ɗan nawa. kuma tunda dai ya riga ya mallaka masa ba zani ba, babu wani taro da zanje ni kam, gwara naja mutuncina".
Aisha da Ilham na kallonta, Hajiya tace,"to akwai wata matsala ne Boɗejo?".
tace,"matsaltsalu ma kuwa, wa ya aikeni zuwa gurin da yake mallakin Turaki!, tun fa ranar da akai wannan zaman akan batun aurensa nace ko aikin asiri ke cinsa shikenan fa ya daina kulani, idan ya ganni ma ɗauke kai ya ke, jiya ma da suka zo gidan nan shi da ubansa kallon arziƙi bai min ba, yana ji Dikko na gaishe ni amma balagaggen yaron nan sai yasha mur ya kauda fuska gefe, to yanda ya ƙullace ni ɗin nan na sake naje kamfanin nasa ai sakawa zai yi a kore ni, kaɗan daga aikinsa, dama ya taɓa korata daga ɗakinsa daga zuwa in dubasa, kinga kuwa me zai kaini kamfani kuma, a'a ku ɗin dai kuje sai kun dawo, wannan ɗan ai halin wan Kakansa yayo, Sarki Adam ba, basu da kyau sam".
Hajiya tace,"to Allah ya kyauta, bari na sanar ma Hakimin".
Boɗejo tai shiru bata ce komai ba tana ta shafa kan Ilham, har Hajiya ta fita sai ta dawo tace,"Ilham ku ba zaku je ba?, su Hanifa tun ɗazu suka tafi. shi ma Me Martaban yanzu naji sunyi waya yana batun zasu tafi".
kafin Ilham tace komai Boɗejo tace,"kinga Atika du Allah tafiyarki, yaushe yarinyar ta dawo ko hutawa bata yi ba ace ta wani kama shiga cikin hayaniya, ƙila ma taje taron buɗewar kuma a fara haɗa lemon aƙi sammata, tunda me kamfanin ba mutumci garesa ba, gwara taja mutumcinta da ajinta".
Ilham tace,"Boɗejo ina son zuwa fa, dama haka nace ma Mami zan bi ku mu tafi, kuma fa idan banje ba Hammah Turaki ba zai ji daɗi ba tunda yasan na dawo, yaga duk ƴan'uwa sunje ni banje ba, sai yay zaton wani abu".
tana rufe baki Boɗejo tace,