iru tana fashewa da kuka, har sannan bai ɗauke idonsa daga kanta ba, ganin kallon da yake mata yasa tace,_"na rantse da Allah babu wanda naje kashewa, nima gani na kawai nayi a wajen, ban san ya akayi naje ba, kuma ina ta neman hanyar gida na rasa"._
ya ƙara damƙe hannunta sannan yace,_"har lokacin da ya kaɗeki baki sani ba?"._ ba tare da ta kallesa ba tace,_"na sani, ina ta ɗaga masa hannu bai ganni ba kawai sai ya bige ni"._ numfashi ya sauke yace,_"to kin yafe masa ko kin barsa da Allah?"._ sai da ta ɗago ta ɗan kallesa tukunna tace,_"na yafe masa"._ ya ƙara sauke numfashi sannan yace,_"to aljanun naki da suka kai ki su nawa ne?, dama suna yawo dake ko ranar su ka fara?"_ a wannan lokacin kawai tsaida idonta tayi akan kafaɗunsa, ta girgiza masa kai tace,_"banda aljanu ai, ni banda aljanu, ko Malami za'a kira a tambaya"._ yace,_"wanne Malamin?"._ tace,_"Malamin Ruƙiyya"_.
yana kallon yanda take kallon ƙirjinsa kamar me karantar wani abu a wajen, sai da ya kalli wajen yaga babu komai kawai dai ba zata iya kallonsa ba shine take kallon wajen. sai da ya sauke ajiyar zuciya sannan ya saki hannayenta ya miƙe ya fita daga ɗakin ba tare da yayi musu sallama ba.
a yanzu da yake kallonta sai yake ganin kamar a wancan lokacin, har yanzu yana mamakin me ya kaita wajen, me taje yi?, abu ɗaya kawai zai yarda da shi tana da aljannu kuma su suka kaita, abunda kowa ya faɗa kenan. to ya yarda da wannan, amma wannan tsoron nata fa?, shi jininsa babu tsoro a cikinsa, saboda haka ya kamata wannan tsoron nata ya ragu tunda har jininsa na yawo a jikinta yanzu. ya rumtse ido yana tuna the first abunda likitoci suka faɗa sanda suka isa hospital, _"ta zubar da jini da yawa, jini take buƙata a halin yanzu, cikin gaggawa ba da ƙurewar lokaci ba"._
haka suka faɗa a sannan, kuma ba zai iya cewa ga wanda ya nuna masa hanyar laboratory ba, tsintar kansa kawai yayi a wurin, ba tare da kowa ya sa ni ba. abunda ya tsana a rayuwarsa shine ɓata lokaci da kuma dogon bayani, kuma abinda ya sani jininsa AB+ ne, to don me kuma sai an tsaya wani ɓata lokacin gwadawa?, dan haka dawowa kawai yayi ya kama hannun Zaytuna suka faɗa room ɗin da aka kwantar da Fillo.
_"ki saka mata jinina, ko leda nawa ake buƙata, ko da za'a kwashe shi duka"._ kayan aiki a ajiye suke to jiran me za tai?, dan haka kwanciya kawai yay akan gado tayi jone-jonen da zata yi, nan take jininsa ya fara shiga jikin Fillo. daga fara shigar jinin bai kuma sanin me ya faru ba, farkawa kawai yayi yaga wani yayi replacing nasa akan gadon, Dr Yusuf, likitan da shima yay kyautar nasa jinin wa yarinyar. sai daga baya Zaytuna ke masa bayanin ai ance shima yana buƙatar ya huta ne dalilin da yasa aka cire nasa kenan, dama leda 1 da rabi ake buƙata, Dr Yusuf ya bada rabin.
Turaki ya numfasa yay tattaki ya ƙarasa gaban Fillo dake tsaye har yanzu bata buɗe idonta ba, wataƙila tana jira ne taji ya fita daga kitchen ɗin sannan sai ta buɗe idon, ko kuma tana jira ne ya bata umarnin buɗewar, tunda ita bata da umarnin kanta sai na wani, ya lura da hakan tun farkon zuwanta.
sai dai yana zuwa dab da ita taji gabanta yay mugun faɗuwa, allon ƙirjinta ya girgiza, taji kamar ta arta a guje. so take tasa hannu ta toshe hancinta saboda ƙamshin turarensa da ke shiga hancinta, ba saboda rashin daɗinsa ba, idan tace ƙamshinsa babu daɗi tayi ƙarya, wannan ƙamshin yana ɗaya daga cikin ƙamshin da zata iya cewa da wuya a samu ƙamshi me daɗi irinsa. sai dai da ace tana da iko, da ace tana da iko da Turaki da ta haramta masa sanya wannan turaren, da tasa ya bar ƙasar nan yaje wata ƙasar sun wanke duk wani sauran ƙamshi na irin turaren nan dake jikinsa, ba ta son ƙamshin ta tsane shi, ba don komai ba sai don an haɗa asiri da shi, wannan asirin da yay sanadin zuwanta cikin dajin da ta kusa mutuwa.
ranar da Turaki ya tsareta da tambayar me ya kaita wancan wurin yana kama hannunta taji ƙamshin, ƙamshi ne da ba zata manta da shi ba, ta jima tana zuƙar ƙamshin a lokacin dan tabbatar daga inda yake fitowa, tunaninta ko asirinne ya kuma biyota, da ga baya ta ankara da cewa ba ƙamshin kowa ba ne sai nasa, that means ya tabbata kenan asirin nan nasan ne, kuma an haɗa asirin ne da turaren da yake sawa...saboda haka yanzu fatanta guda ɗaya ne, Allah ya bata wata dama da zata hana Turaki saka wannan turaren, ko kuma Allah ya ɓatar da turaren daga duniya gaba ɗaya.
jin takalmin Turaki gaba ɗaya akan kafaɗunta tai firgit ta buɗe ido ta sauke kallonta akan ƙafafunsa dake cikin takalmin shigowa kitchen. ta haɗiye wani busashshen yawu sannan ta iya buɗe baki tace,"kayi haƙuri ban san me kake cewa ba".
ya fito da hannayensa daga aljihu ya tamke fuska yace,"na miki kama da dodo?". da sauri ta girgiza kanta alamar a'a. yace,"to me yasa duk ranar da kika ganni kike rikicewa ki bi ki firgice, ko ina kama da aljaninki?". nanma ta girgiza kai cikin sauri tace,"a'a". yace,"to ina jinki tsoron na mene?".
a hankali tana shirin yin kuka tace,"ba