NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 8 of 323

amma ga mamakinta sau ukun nan data buɗe bata taɓa cin karo da wani rubutun na daban ba bayan sunan Muhammad Turaki da yake jiki, sai ayanzu da take ganin wani rubutun sunan na daban da akayi shi aƙasan na turakin shi kuma da baƙar tawada amma ya fara disashewa hakan yasa ta kasa fahimtar kome aka rubuta. Kawai sai taji wani dunƙulallan yawu ya wuce ta maƙogwaronta, tun a ranar farko da layar nan taje hannunta wani ɓari na zuciyarta ke gaya mata Halimatu karki jawa kanki bala'i, irin wannan abun mutum idan ya gani kauda idonsa yake akansa, amma yau kece da ɗaukar takardar da babu makawa anyi ne dan asirin wani. Amma ayau sam zuciyarta bata yi mata wannan gargaɗin ba, illama ƙwarin gwiwar da take bata akan tayi iya duk ƙoƙarin da zata yi kan ganin ta karya wannan asirin, dan zata iya rantsewa wanda ake abun akansa ba shi da alhakin kowa, dan haka ta shirya yin jihadi akansa. Saboda haka kawai sai ta cure takardar wuri guda ta jefar, ta ɗauki baƙar ledar da ta bawa Maijidda ajiya gudun kar Kaka ta gani, itama ta jefar a wurin. Muryarta ta firo a fili tana faɗin,"har yanzu banda tabbacin asiri ne kuka yi ko ba shi, to koma dai menene sai dai yaci ku ku ɗaya, ga abinku nan ya koma kanku". Tana faɗar hakan ta ƙyasta ashana ta jefa, nan da nan ko wuta ta kama da wajen. Garin tayi baya ta bige ƙafarta ajikin kujerar wurin har taji ciwo a babban yatsan ƙafarta. Amma ko tsayawa tabi ta kan ciwon ba tai ba. Maijidda ko banda ambaton, "innalillahi wa'inna ilaihi raji'un". Babu abinda take. Har sanda Fillo ta risko wajenta ta kama hannunta dan su bar wajen. "ni kam na shiga uku dake Fillo, yanzu kin san iyakar inda wutar nan zata tsaya ne?, ba kya gudun abinda zai faru damu?". "idan an tambaya sai kice mune muka kunna kinji". Fillo ta faɗa tana ƙara jan hannunta dan su bar wajen. Duk rashin iya gudu na Maijidda sai gashi har tana kusan kerewa Fillo saboda ita numfashinta ya fara ƙoƙarin tsayawa. Kuma kan kace kobo hayaƙin wutar ya fallasu acikin gidan, saboda wuta ce ta tashi ba kaɗan ba sakamakon fulawoyin dake wajen, cikin mintunan daba zasu haura biyar ba sai ga fire service sunzo. Irin tashin hankalin da wutar ta haddasa a zuƙatan al'umma Allah ɗaya yasan yawansa, an kewaye wajen anata salati, saboda irin tashin ƙarni dake fita ta cikin wutar yana shiga cikin hanci ya haura saman ka, ya haddasa faɗuwar mutane da dama a wurin. Saboda wani irin wani ne da bashi da daɗi, dan asthmatic ma bai iya tsayawa a wurin. Haka ambulance tai ta shige da ficen ɗaukar mutane. A yayinda a wannan lokacin Fillo da Maijidda na can cikin uwar ɗakin Yami, hankalin Fillo kwance kamar ba ita tayi ba, Maijidda kuwa tai tsilli-tsilli da idanu kamar ta fashe da kuka. Tana ta yiwa Fillo maganar amma kamar da dutse ta ke. Dan ita a wannan lokacin ma tunaninta na kan wani lamari na daban da take haskowa wanda take tunanin yafi wannan hatsari. Ƙarshe dai da Maijidda ta isheta da maganar da ba zata iya zaman jinta ta miƙe ta bar mata ɗakin. Ta wuce ɗakinsu ta ɗauki littafinta ta hau assignment ɗin da Amir ya bata, wanda kusan kwana huɗu kenan da bata amma batayi ba saboda shiririta. Don Allah share to other groups🙏 Youtube Channel-Sahaz Multimedia *LULLUƁIN BIRI* *©️Halima h.z* *3* *Dare, 20:45pm.* Ƙafafun Hajiya Madina suka shigo cikin ƙaton parlon, wanda ƙamshinsa ya haɗe da sanyin acn dake hurawa ya haɗu ya bada wani sanyin ƙamshi me motsa zuciya. Jikinta sanye da ash abaya wadda taji adon stones ajiki, ƙyallin stones ɗin sai wurgawa suke ta cikin hasken fitilun parlon. Ganin Ƴaƴanta ya saka ta sakin murmushin da bata shirya masa ba, tana ƙaunar yaran fiye da yanda take son kanta, kowa yasan da hakan, abu ne ma da kamar tayi tambarinsa a goshinta. Tana tsaye daga bayansu tana ƙare musu kallo cike da so da ƙauna, su kuma hankalinsu ya tattara kan tab ɗin dake kan cinyar Sameer suna kallon pixx ɗin da sukai ɗazu na birthday ɗin Turaki. Gyaran muryar da tayi ne ya ankarar da su zuwanta, suka ɗago a tare suna kallonta fuskokinsu na washewa da murmushi. Ta zauna a kujerar dake fuskantarsu tana faɗin,"shine aka kasa jira nazo, wannan cin amanar har ina?". Tai maganar da sigar wasa kamar wadda ke tare da ƙawayenta. Samha ta ɗauko tab ɗin ta nufo wurinta tana faɗin,"Maama kinga wanda aka maku ke da Hammah duk yafi kyau wallahi". ta zauna kusa da ita tana nuna mata hoton da aka ɗauka a sanda Turaki ke saka mata cake a baki. Allah ɗaya yasan me taji cikin zuciyarta a wannan lokacin, dan shi kansa murmushin daya suɓuce a leɓenta bata san da zuwansa ba. Ta kai hannu ta shafa hoton, ƙwayar idanuwanta na haskawa da ƙyallin wata ƙauna dake tsakanin  Uwa da Ɗa wanda Ubangiji kaɗai yasan girmanta. "gaskiya munyi kyau, kamar ban haifi Hammah ba, kalle ni wata ƴar suwet a kusa da shi. Wannan idan sirikata ta gani ai sai tayi jealous idan bata san wacece ni ba". Ta faɗi hakan cike da raha, haƙoran makkan dake bakint
🏠