sukai sannan suka fito suka shiga kitchen, suna aikin Fillo na bitar karatunta, ɗan gutun turancin da brain ɗinta ta haddace sai maimaita shi take a zuciyarta, idan ta faɗesa a fili kuma sai taji maganarta wani banbarakwai sai tayi dariya, haka kawai Amir ya faɗo mata a lokacin, idan yay mata turanci sai yace ta faɗi abinda yace sai ta kasa, yace zata iya tace ita kunya take ji tasan ba zai yi daɗi a bakinta ba irin yanda yake daɗi a nasa bakin, sai kuma ta tuna abinda ya faru tsakaninsu a ɗazu, tai saurin watsi da tunaninsa tana jin zuciyarta na zafi.
Zaytuna ce ta taya su Fried rice ɗin da basu iya ba, sun maida hankali sosai wajen ganin yanda ake yi, duk abinda ta ɗauko na vegetable zata faɗa musu sunansa da amfaninsa da kuma yacca ake sawa, babu jimawa suka kammala Fried rice ɗin. suna aikin Ɗausiyya ke tambayarta,"Anty kuma sai ku iya cin abinda muka saka hannu?".
Zaytuna tai murmushi tace,"Hammah ne kawai baya cin abinda ƴan aiki suka dafa, amma mu kam muna cin duk abinda ƴar aiki ta dafa muddin ta kula da irin tsaftar da muke so, kema baki ga yau fes dake kika fito ba, kuma ina kallonki duk abinda kike yi cikin tsabta kike yinsa...yanzu ma kalle ki tsab, to tsabta ita ke sawa aci girkin mutum, duk daɗin girkin mutum idan baida tsabta sai dai yaci kayansa shi ɗaya".
Zaytuna da Ɗausiyya suka ɗauka tray suka fita da shi, suka bar Fillo da ƙarasa haɗa kunun shinkafar da Samha tace tana so tasha. ta fasa madarar gwangwani ta ruwa kenan sai taji kamar mutum a bayanta, ta waigo ta ga Turaki ne tsaye hannayensa a aljihu yana kallon abinda take preparing, da alama ma ba shigowarsa kenan ba.
sai ta nemi ta dirirce, ta durƙusa a gabansa da sauri tana gaishe shi, ita bata san me yasa ba amma duk sanda ta gansa sai ta tsorata. bai amsa mata ba ya wuce ya ɗauki cup ya dawo, tana nan durƙushen har lokacin, da wani irin voice tace da shi.
"kana buƙatar wani abu ne?". ya kalleta amma ba ita yake kallo ba hannayenta yake kallo, yace. "tashi". ta miƙe tana ɗan matsawa daga kusa da shi. fuskarsa a ɗaure yace,"what is this?". ta so fahimtar abinda yace, amma hakan bai samu ba, jin tai shiru ya waigo ya dubeta, tana tsaye kamar gunki duk ta cika da tsoronsa, hannun nan sai karkarwa yake, shi kuma abin na basa takaici.
yaja guntun tsaki ya ƙara cewa,"i am asking you, what is this that you are making?". yanda yay maganar murya a sama yasa ta fara ƙoƙarin hargitsewa, ta ƙanƙame hannayenta a jikinta tare da kulle idonta, shin har sai yaushe zai fara fahimtar wannan yaren ita kam bata jinsa, ita kuwa ko ba dan komai ba ai dole ta tsaya ta mayar da hankali akan wannan gatan da Hajiya Madina tai musu ta koyi turanci. ji take kamar tayi kuka, bata ko ƙaunar tana aiki a kitchen ya shigo, ko ba'a kitchen ba bata so tana aiki taga giftawarsa, ita haɗuwa ma da shi totally bata so.
Turaki ya tsaya yana kallon ikon Allah, shi kam ba dan ba dan ba, da sai yace yarinyar nan bata sahun mutane sai dai wata halittar. karkawarwa take kamar wadda ruwan sanyi yaywa mugun duka, ko kuma wacce iskar fanka ke kaɗawa. sai ya ajiye cup ɗin hannunsa kawai ya rungume hannunsa a ƙirji, ya jingina da jikin drower ɗin yana ta kallon sarautar Allah, ba zai ƙara magana ba balle motsi har sai ta gaji dan kanta ta dawo cikin hayyacinta, sannan zai buɗi baki ya faɗa mata karta ƙara ganinsa ta tsorata tunda shi ba dodo ba ne.
lokacin da ya tsareta da tambaya a asibiti ya haska acikin kansa da cikin idonsa, wannan lokacin da ya riƙe hannayenta dan hana su rawar da suke yi, amma still basu daina ba sai ma rawar hannun nata ya haɗe har da nasa, tambayarta yay kawai me ya kaita wannan wajen, amma yanda tabi ta ruɗe ta nemi ta firgice har sai da yasa ɗaya hannunsa ya riƙeta da kyau, dan kamar zata faɗo ne daga kan gadon.
_"me ya kai ki wannan wurin a wancan ranar?"_ tambayar da yay mata kenan amma kamar ya tuhumeta ne akan me yasa tai kisan kai. sai da ya matse hannunta da ƙarfi sannan ta buɗe ido ta kalle shi hawaye na sakko mata tace masa,_"ina?"_ harara kawai ya galla mata a lokacin, kafin yace,_"wurin da kika je za ki kashe kanki"._ sai kawai ta shiga girgiza masa kai, cikin rawar murya tace,_"Allah ba kashe kaina naje yi ba, ai babu kyau mutum ya kashe kansa"._ taji yay shiru bai yi magana ba, sai ta buɗe idonta dake rufe ta sauke a kansa, ƙwayar idonta ta shiga nasa, taji wani abu da bata taɓa jinsa ba, taga ya ɗaga mata gira duka biyun yana cewa,_"ummm ina jinki, to wa kika je kashewa?"._, saura kaɗan yay dariya saboda yacca ta ƙara ruɗewa da tambayar tasa, har tana ja da baya wanda inda ba'a kan gadon take ba tsab zata arta da gudu.
ƙoƙari take ta zare hannunta a cikin nasa tana girgiza kanta cikin tashin hankalin da ya rufeta farat ɗaya. hawaye ne sosai yake sakko mata a sanda take ce masa,_"Allah babu wanda naje kashewa, me yasa zan kashe wani, akan me?, ko cinnaka bana iya kashewa ka tambayi Kaka kaji, dan Allah kayi haƙuri kar ƴan sanda suji su kamani"._ tai sh