NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 77 of 323

nke miki ciwon kamin ya dawo kika ɓuya a bayan bulo, kuma ya durƙusa yana haɗa hydrogen kika felle da siraran ƙafafunki kika bar wajen, kina gudu kina waige saboda kar ya kamoki". Maijidda ta ƙyalƙyale da dariya, Fillo kuma kunya ta kamata tasa hannu ta rufe fuska tana murmushi, Yusuf ma murmushin yake. tace,"kuma baka manta kamannina ba har wannan lokacin?". yace,"to yaushe akai abin?, shekara ɗaya da rabi ne fa kawai. kuma ai ba wani girma kika ƙara ba da za'a kasa ganeki, kin dai ɗan ƙara wayo ne kawai, sai abinda ba'a rasa ba, amma ai nasan ko yanzu kika ji ciwo zaki tirje a tsakiyar layin nan ki ta kuka abinki ke ɗaya har sai kinga me allura zaki gudu". murmushi bai bar fuskar Fillo ba har lokacin, taji hirar na tafiya da ɓacin ran da Amir ya haifar mata. Maijidda tace,"gaskiya baka da mantuwa". yace,"ai duk randa zan wuce ta wurin nan ai sai na tuna, kin ga fa haka ta riƙe ƙafa tana kallon ciwon tana ta tsala kuka kyace yanke ƙafar akai, kuma abin takaici ciwon fa ɗan ƙaɗanne ba me yawa ba". ya faɗa yana kwaikwayon yanda takeyi a lokacin. ya basu dariya sosai, yana da fara'a da barkwanci, Maijidda tace,"wallahi na tuna lokacin, ai in faɗa maka ciwon nan anfi wata guda ana jinyarsa, haka take ko ya taga jini a jikinta sai ta hargitse". yace,"kice da idonta biyu aka kaita asibiti ran na da mun shiga uku, ƙila duk patients namu sai sunce a sallamesu dan babu me iyawa da kukanta". Fillo ta harari Maijidda tace,"sharrin Hassana ne fa". Yusuf yace,"zan yarda ai, kece fa". ya kalli agogo yace,"kun ce zaku yi aiki nima kuma zan tafi, bara na ƙyaleku kar na cika ku da surutu, ina da yawan hira da ƙannena, ina son sisters mata musamman kamarku, amma ku ɗin sai naji kuna burgeni sosai". suka ce,"mun gode". yace,"nima na gode, amma ya kamata dai aje ayiwa Kakata godiya na dubiyar dana zo nayi". Maijidda tace,"tom shikenan kayi mana kwatance, sai mu zo wataran". yace,"yaushe kenan". tace,"ehh tou sai mun sami damar fita idan kamar Yami ta aikemu gidan sarki". yace,"to ai kuma ƙila lokacin bana nan". Fillo ta sami kanta da tambayarsa,"ina zaka je?". yace,"ai a kano nake da zama, nan nake zaune ni da matata, nan garin kuma gidanmu ne da Inna Wuro ta samu tayi bake-bake acikinsa ta hanamu sakat, ta mayar da gidan kamar nata...saboda haka idan zaku zo ku tabbatar kun fesa turare kamar zai yi magana, kun kuma kai mata ƙunshin leda ko da babu komai aciki in ba haka ba kun shigesu da sababi". Maijidda tace,"Kakarku ce Inna Wuron?". yace,"ita ta haifi Dad namu amma ta zamar mana ciwon kai, kowa ya gaji da ita...nima dan dai ita ta raine ni banda haka tuni na ɗinke bakin maganarta". sukai dariya su duka, Fillo ta katse hirar da cewa,"tom bari mu tafi, mun gode sosai Allah ya kai ka gida lafiya". suka faɗa a tare suna niyyar wucewa. sai ya tsayar da su. "tsaya ki karɓi alluranki Malama, ki kaiwa ɗaya Kakar taku da kuke cewa Yami wadda kike ɗan tsoro ta dinga tsira miki". Fillo ta ɓata fuska tana kama hannun Maijidda dan su tafi. sai gani sukai ya fito da fararen ledoji guda biyu manya, Fillo na ganinsu ta gane irin ledar kantin da Zaytuna ke yin siyayya ce. ya miƙawa Maijidda yace,"ga shi duka na na mara lafiya ne amma kema idan kina so ana iya tsira miki ko guda ɗaya ce, tunda naga da amana a tsakaninku". Maijidda ta karɓi ledojin tana masa godiya, shi kuma ya zagaya ɓangaren driver seat ya buɗe motar, idonsa na kan fuskar Fillo da ta cukule, sai haɗe gira takeyi kamar zata yi kuka, tana ta harar Maijidda. ya shiga motar yana ta smiling, ya zuge glass na ɗayan kujeran me zaman banza ya leƙa da salon tsokana yace,"Auta ya dai? a saki ran please kar Kaka tace na taɓa mata Hussaina, kuma dan Allah banda kukan allura kinji, kinga kin girma". Fillo da ta gama kumbura tai tafiyarta ta bar Maijidda a baya, yana kallon Fillo har ta shige cikin gida, haka kawai yake jin yarinyar ta tsaya masa a rai. ya kuma kasa gane dalilin hakan, tun randa suka bar asibitin yaji kamar zuciyarsa ta shaƙu da yarinyar, kamar yana ya dinga ganinta kullum, kamar dai yana so ya fahimci wani abun amma ya gagara. sai daya tabbatar da shigarsu gidan sannan ya bar layin yana ji a ransa yana so ya ƙara kasancewa da yarinyar. *Please Vote, Comment, and Share.* *LULLUƁIN BIRI* *©️Halima h.z* *21* Maijidda ce ta wuce da ledar kayan, Fillo na faɗa mata karta soma ta ambaci sunanta idan Kaka ta nemi ba'asin karɓan kayan Dr Yusuf. ai tasan an hanasu shine yana miƙowa ta amshe. Maijidda na ɗan jin tsoro tace,"to ni ai nai zaton da gaske alluran ne shiyasa na karɓa". Fillo na dariya tace,"kinga ke dai kije kisha faɗanki ke ɗaya, ni na tafi aiki. da nasha faɗan Kaka gwara na sha na Hajiya Madina". tana faɗa ta ƙara saurin tafiyarta tana taiwa Maijidda dariya, ita kuma nata jin shakkar shiga da kayan, ji take kamar ta koma taga idan Dr Yusuf bai tafi ba ta basa kayansa, to amma tasan zuwa yanzu ya tafi kam, dan ko ɓata lokacin da suka yi a wuri
🏠