NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 76 of 323

iye a kusa da ita bata sani ba muyi ficewarmu, Yami ba zata ce komai ba ƙarƙari tace da Kaka Ƙawata to ya za'ai babu komai ai, da saninki ai ba zaki fasa ba". ta faɗi maganar tana kwaikwayon muryar Yami. su duka sukai dariya, kuma cikin sa'a tana saka batirin ta kunna sai ga wayar ta kama. a tare suka sauke ajiyar zuciya. lokacin kira ya shigo da sabuwar lamba, ta miƙawa Maijidda tana miƙewa. ita kuma tace da ita,"ki ɗaga Dr Yusuf ne, tun safe yake kira wai na haɗaku, yama dai ce na masa kwatancen gidan nan nayi masa, ƙila ko zuwa zai yi". Fillo ta harareta tace,"yazo yayi me?". tace,"haka nace miki zai zo?, ce fa nayi ƙila zuwa zai yi, ki ɗaga kiji koma menene daga bakinsa". ta aje wayar a cinyar Maijidda ta tashi sai Kaka tace,"babu kyau dai wulaƙata mutum, musamman wanda ya taimaka maka a rayuwa, ba masu gidan nan ne kaɗai suka taimaka miki ba, harda shi likitan, dan shima ya bada jininsa an zuba miki". Fillo na ɓata fuska tace,"to Kaka yanzu sai kiji yace ai wani magani ko wata allura ya kawo". Kaka tace,"to ki ɗaga mana kiji dai me zai ce tunda ya neme ki, in allurar ce tunda ba shi ne zai yi miki ba ai sai kin so za'ai, abu da kece Halimanki, tun kan ki shigo nan zaki jefar da ita, sai kace kwanciyar asibiti tasa kin manta wacece ke". ba dai haka Fillo taso ba, sai dai bata son jayayya da Kaka, ta karɓi wayar ta ɗaga, tana yin sallama Yusuf ya ɗauki muryarta. daga cikin motar da yake ya kwantar da kansa jikin kujera sannan ya amsa sallamar. Fillo tace,"ina kwana, ya kake?". maimakon ya amsa mata sai taji yace,"ai na shanyu har na bushe, daka ni kawai ya rage ayi". taso yin dariya amma sai ta maze tace,"kaman ya?". yace,"kamar yanda Sister ɗinki bata faɗa miki ba, na kirata nace zanzo na duba jikinki before na bar gari tace min to, ta ban address kuma nazo inata kiranta taƙi ɗagawa, at the end ma sai ta kashe wayar, nayi zuciya zan tafi kuma sai na tuna da saƙonki nace to lallai ko zan kwana anan ba zan tafi ba". bakin Fillo a gaba tace,"saƙon me?, kuma ai ba daidai tayi maka kwatancen gidanmu ba". yay murmushi yace,"tambaya har guda biyu a jere, duk ranar da kika zama lauya ai sai ki ɗaure mutum. to da fari dai address daidai aka ban, domin kuwa gani a ƙofar gate ɗin gidan Alƙali Dikko, kuma gate na ɓangaren ma'aikatan gidan, gani ina kallon me gadi baƙi ɗan lukuti kamarki. saƙo kuma sai kin fito kya gani". da ƙosawa tace,"na san saƙon allura ne kuma bana so kuma ma bama gidan mun tafi ƙauyenmu, sai ka tafi". cikin kwaikwayon muryarta Yusuf yace,"kuma ma ba allura kaɗai bace harda magani, kuma ma da wuƙar farke ciki, kuma ma me gadi yace min kuna nan ba kwa fita, kuma ma ba zan tafi ba har sai kin fito". a wannan karon dai sai da sautin ƙaramar dariyar Fillo ya fito, Yusuf ya gyara zamansa yana sosa kansa wanda yasha sabon aski yace,"kinga Malama ki fito kawai nai miki tiyatar nan a wuce wurin, ni ban haƙura ba har yanzu nafi gane ai miki bakinki acikinki sai a ɗinke wannan bakin tsiwar da Maijidda tace yana isarsu". tasa hannu ta rufe fuskarta cike da kunya, sai kuma tace da shi,"to ka shigo kawai me gadin ba zai hanaka ba, sai kace masa wajen Kaka kazo". Yusuf ya kalli gate ɗin sai kuma yace,"a'a dai ki fito ɗin kawai, ba jimawa zanyi ba akan hanya nake". tace,"tom". ita da Maijidda suka fita, hannayensu saƙale dana juna, hijab ɗin jikinsu iri ɗaya komai da komai. yana cikin motarsa fara BMW, sai da suka isa wurin sannan ya fito. jikinsa shadda ce ƴar ubanta dark blue, ta amshi farar fatarsa, tunda ya fito yake ƙarewa girman gidan kallo tare da jinjina kai, yasan wannan gidan ko filoti goma sha albarka, har ƙasa suka tsuguna suka gaishe shi. hannayensa harɗe a ƙirjinsa yace,"Hassana da Hussaina". su kai murmushi kawai basu ce komai ba. Fillo ta lura yana da magana, hakan yasa tace,"Kaka tana gaisheka, kuma muna da aiki a cikin gida". yace,"ina amsawa, nima yanzu zan tafi ai ba sai kin kore ni ba, saboda nan da minti 20 jirginmu zai tashi. kawai ji nayi ina so nazo naga mara lafiya ne". Fillo tace,"ai naji sauƙi". yace,"ehh naga alama ai, Allah ya daɗa lafiya". ta amsa da amin, sai kuma duk suka yi shiru. Yusuf yace,"ranar da zaku bar asibiti baki bari na baki amsar tambayarki ba kika gudu". ta ɗago ta kalle shi tace,"amsar me? aini ban tambayeka komai ba". yace,"ehh bakinki bai faɗa ba amma ƙwayar idonki ta faɗa...kina jin kamar kin taɓa sanin me wannan fuskar ƴan gayun ko". ya faɗa dan raha yana shafa fuskar tasa. bata ce komai yace,"ko ba haka bane?". tace,"nayi mamaki daka fahimta". sai yay murmushi yace,"zaki iya tuna watarana?, lokacin baki kai haka girma ba, time ɗin gidaje uku ne kawai a estate ɗin nan, kin fito yawo kika ji ciwo kika zauna kan yashi kina kuka, wani bawan Allah me tausayi yazo ya sameki yasa ki kai shiru da ƙyar, yace ki nuna masa gidanku ya kai ki kika ƙi kika ce Kakar ki zata dukeki saboda bata san kin fito ba, yace to ki tsaya ya ɗauƙo first aid a mota ya wa
🏠